Sarkin Musulmi, Alhaji Abubakar Muhammad Sa’ad, ya bayyana cewa gobe Talata, 30 ga watan Afrilun 2025, ita ce za ta kasance 1 ga watan Zhul Qi’ida na shekarar 1446 ta Hijiriyya.
Wata sanarwa da shugaban kwamatin ganin wata na fadar, Farfesa Sambo Wali ya fitar ta ce an ɗauki matakin ne saboda ba a ga jinjirin watan ba a ranar Lahadi.
- Yadda matar gwamna ta sa mata gasar haihuwar ’yan uku
- Rasha ta ayyana tsagaita wuta ita kaɗai a yakinta da Ukraine
Hakan na nufin yau Litinin, 28 ga watan Afrilu ne 30 ga watan Ƙaramar Sallah na Shawwal.
A ƙa’idar kalandar Musulunci, kowane wata yana yin kwana 29 ne, amma idan ba a ga jaririn watan ba sai a cika shi zuwa kwana 30.
Aminiya ta ruwaito cewa tun a ranar Asabar da ta gabata ce Fadar Sarkin Musulmin ta ba da umarnin duban watan na Zhul Qi’ida.