Mama yaushe za a koma makaranta? Wannan ce irin tambayar da yara suke damun iyayensu da ita tun daga lokacin da aka rufe makarantu sakamaakon yaduwar annonbar cutar coronavirus a fadin Najeriya.
Ahmad Ibrahim dan shekar takwas na daga cikin yaran da ke damun mahaifiyarsa Hajiya Maryam Baba wadda ta shaida wa Aminiya cewa tana kokarin neman amsar da za ta ba shi a duk lokacin da ya tambaye ta.
“Nakan amsa masa da cewa ban sani ba, har ta kai yana jin haushi.
“Hakan ya sa na fara kauce wa tambayoyinsa ko kuma na amsa masa da cewa sai lokacin da aka gama ‘corrona’.
“Kai ta kai wani lokacin idan na ga zai dame ni sai na kira malamar ajinsu don ta yi masa bayanin halin da ake ciki”, inji ta.
Hajiya Maryam ta kara da cewa ba ta san ‘ya’yanta sun damu matuka su koma makaranta ba sai lokaccin da aka rika yada jita-jitar cewa za a koma makaranta a watan da ya gabata inda suka yi ta murna.
“Tun da suka ji wanann labari suka yi ta murna, domin akwai wanda sai da ya dauki kayan makarantarshi ya kai su wanki, amam abin bakin ciki sai ga shi labarin ya zama na kanzon kurege”.
Kimanin watanni hudu ke nan yanzu da gwamnati ta rufe makarantu don dakile bazuwar annobar coronavirus a tskaanin jama’a, matakin da ya tilasta dalibai zama a gida tare da iyayensu.
Duk da cewa a ranar 29 ga watan Mayu gwamnati ta bayar da sanarwar shirin sake bude makarantu ga daliban ajujuwan karshe na firamare da karamar sakandire da babba, amma ta ce sauran daliban wadanda su ne suka fi ywa za su ci gaba da zama a gida.
Lamarin da ke kara sanya damuwa a zukatan iyayen yaran, ko da yake daga baya an jingine batun bude makarantun ma kacokan.
Yayin da take yi wa Aminiya bayanin halin da take ciki, wata mahaifiya mai suna Dakta Rukayya Yusuf ta ce tana mamakin yadda ‘ya’yanta suke kaunar komawa makaranta.
“A kowane lokaci ‘ya’yana suna yin maganar komawa makaranta. Haka za ki ji sun zauna suna maganar malamnsu da kawayensu da irin karatu da wasannin da suke yi. Kai duk wani abun da ya shafi makaranta.
“Sun gaji da zaman gida, kai hattaa kayan wasansu sun gaji da yin wasa da su, su dai kawai a koma makaranta shi ne fatansu”, ta ce.
A cewarta, tambayar da babban danta mai shekara tara yake yi mata ita ce yaushe wanann annobar za ta kare.
“Kai hatta karamin dana Faruk wanda a koyaushe idan za a tafi makaranta sai ya nemi uzuri don kada ya je makarantar a yanzu haka kullum sai ya tambayi lokacin da za a koma makaranta.
“A yanzu haka dai babu abin da yara ke yi sai dai su zauna a gida suna wakokin makaranta da kwaikwayon yadda malamansu ke koyarwa a aji”, inji ta.
Ita kuwa wata mahaifiya Malama Umma Garba ta bayyana wa Aminiya cewa hutun dolen ya sa ‘ya’yanta sun tsani zaman gida gaba daya.
“Zan iya tunawa lokacin da aka fara rufe makarantu da farko ‘ya’yanta sun yi murna.
“Kin san wasu lokuta yara ba su son zuwa makaranta sukan nemi uzuri da zai hana su zuwa makaranata.
“To bayan an gama azumi, aka gama bikin sallah sai suka fara damuwa da zaman gidan”.
Kabiru Usaini ya shaida wa Aminiya cewa ‘ya’yansa sun tilasta masa ya kai su gidajen yan ajinsu domin su ga juna su kuma yi wasa tare.
“Yaran suna kewar junasu hakan ya sa sun matsa min sai na rika kai su gidajen ‘yan ajinsu suna wasa tare da juna.
“A wasu lokutan su ma kawayen nasu suna zuwa gidanmu don ganin ‘ya’yana . Hakan ya sa sukan sami annashuwa”.
Ita kuwa Fatima Muhamamd cewa ta yi zaman yaran a gida ya sa ko yaushe idan za ta fita sai ta fita tare da su.
“Yayin da ake karatu nakan yi amfani da wannan lokaci na je ziyarce-ziyarcen da nake son yi, amma yanzu dole sai dai na tafi tare da su, saboda sun gaji matuka da zaman gidan.
Shirin koyarwa ta rediyo da talbijin
Gwamnatin Jihar Kano ta bullo da shrin koyarwa ta gidajen rediyo da talbijin don kawo dauki ga asarar karatu da dalibai ke yi sakamakon zaman gida da cutar coronavirus ta tilasta.
An bullo da shirin ne don ilimintar da dalibai da kuma karfafa musu gwiwa don su sami ilimi duk da cewa suna zaune a gida tsawon lokaci.
Yayin bude shirin, Kwamishinan Ilimi na jihar Muhamamd Sanusi Sa’idu ya ce shirin zai ilmintar da daliban tare da taimaka musu wajen yin damarar tunkarar jarabawar da ke gabansu.
“A maimakon su zauna ba tare da karatu ba muka yanke cewa mu fara yin wanan shirin a matsayin bitar darussansu”.
Sai dai binciken da Aminiya ta gudanar ya nuna cewa ba lallai ne shirin koyarwar ya kai bantensa ba saboda wasu dalilai.
Muajheed Hafeez dan aji daya na babbar sakandare ya ce bai san ana gabatar da shirin koyarwa a kafafen watsa labarai ba.
“Gaskiya a gidanmu ba mu fiye sauraran rediyo ba. Ni yanzu ma nake jin batun ana koyarwa a rediyo”.
Ita kuwa Sadiya Aminu yar firamare cewa ta yi, “shirin rediyon ba ya ba ni sha’awa, saboda yawanci da turanci ake yi. Gaskiya ba na fahimta sosai”.
Wata mahaifiya Firdausi Abdulkadir ta ce duk da cewa tana sane da shirin, amma daga baya ta yanke kauna daga gare shi.
“Da aka fara shirin a rediyo ina ta murna akalla yara sun samu abin yi. Ban da ma haka shirin zai ba wa yara damar koyan karatu a gida.
“Sai dai lokacin da aka fara shirin a rediyo sai na lura darussan ba su tafiya daidai da manhajar karatunsu na makaranta”, inji ta.
Sai dai ba haka abin yake ga Amina Aminu ba, ‘yar aji biyun babbar sakandare wadda ta ce, “Tun daga lokacin da ka fara watsa wannan shiri a gidajen rediyo ban taba yarda ya wuce ni ba.
“Ina bibiyar lokutan da ake gabatar da shirin a kusan dukkanin kafafen watsa labarai da ke jihar nan.
“Kuma gaskiya na koyi abubuwa da yawa”, inji ta.
Binciken Aminiya ya gano cewa iyaye da ‘ya’ya dukkaninsu sun kagara su ga lokacin da za a kara bude makarantu.
“Tsoron da muke yi shi ne idan har aka ci gaba da garkame makarantu har zuwa wani lokaci ‘ya’yanmu za su yi asarar gaba dayan shekarar ke nan.
“Muna fatar mu ga nan ba da dadewa an koma makaranta ko yaranmu za su samu su shiga aji na gaba”, inji wani daga cikin iyayen yaran.
Sai dai zuwa yanzu gwamnati ta dakatar da shirin bude makarantu ga dalibai masu jararbawar kammala firamare da sakandare.
Ministan ilimi Adamu Adamu ya ce ba za a za a bude makarantun gwamnatin Tarayya ba har an samu tabbacin dalibai ba za su kamu da cutar coronavirus ba.
Hakan ta sa daliban Najeriya ba za samu rubuta jarabawar sakandare ta WAEC ba, wanda ake sa ran farawa daga ranar 5 ga watan Agusta.