Kotu ta yanke wa wani matashi hukuncin ɗaurin shekara biyu a gidan yari kan laifin yunƙurin soka wa mahaifinsa makami a unguwar Fagge da ke Jihar Kano.
Kotun da ke zamanta a yankin Mai Alluna ta yanke wa matashin hukuncin ne bayan bayan alƙali ya kama shi da laifin yunƙurin soka wa mahaifinsa almakashi saboda ya hana shi kuɗin kashewa.
’Yan sanda sun gurfanar da matashin ne a kan laifin ɗura ashariya da barazanar kisa da kuma ɗaukar makami ba bisa ka’ida ba.
Bayan karanta masa takardar tuhumar, matashin ya amsa laifin, inda Alƙali Nasir Ahmad ya yanke masa hukuncin ɗaurin shekara biyu da tarar Naira dubu 20, da kuma karin ɗaurin wata shida tare da bulala 40.