✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotu ta tsare ’yan TikTok 2 a Kano

Ana tuhumar ababen zargin da wallafa bidiyon da suka saɓa wa tarbiyya da addini.

Wata Kotun Majistire mai lamba 7 a Kano, ta bayar da umarnin tsare wasu ’yan TikTok biyu kan zargin wallafa wasu bidiyon batsa a shafukansu na dandalin sada zumunta.

Hukumar Tace Fina-Finai ta Kano ce ta gurfanar da ababen zargin biyu — Isa Kabir Brigade da Fatima Adam Kurna — kan wallafa bidiyon da suka saɓa wa tarbiyya da addini.

Sai dai bayan lauyan da ke ɓangaren masu shigar da ƙara, Garzali Maigari Bichi ya karanta musu ƙunshin tuhume-tuhumen, sun musanta wasu daga ciki.

Dangane da hakan ne Alƙalin Kotun, Halima Wali ta bayar da umarnin tsare ababen zargin tare da ɗage zaman kotun zuwa ranar 24 ga watan Afrilu.

Ana iya tuna cewa dai Hukumar Tace Fina-Finai ta Kano ta ɗaura ɗamarar tsaftace dandalan sada zumunta ta hanyar kame da ladabtar da masu wallafe-wallafen duk wani abu da ya ci karo da tarbiyya da addini.

Ko a bayan nan sai da hukumar ta gurfanar da wasu mutum biyu — waɗanda aka yankewa hukuncin ɗauri na shekara guda ko zaɓin biyan tara ta Naira dubu 100 — kan wallafa bidiyon batsa a shafukansu na TikTok.