’Ya ta’addan kungiyoyin Boko Haram da ISWAP da na Ansaru na rige-rige da juna wajen dibar sabbin mambobi daga ’yan bindigar da ke addabar Jihohin Arewa maso Yamma da Arewa ta Tsakiya, kamar yadda binciken Aminiya ya gano.
Mazauna yankunan da jami’an tsaro da ma masana da suka tattauna da wakilinmu sun ce tuni yunkurin ya fara samun nasara inda shahararrun ’yan bindigar suka fara mubayi’a ga kungiyoyin ta’addancin.
Hakan dai na nufin za su ci gaba da aiki tare ta bangaren musayar bayanai da makamai da kuma taimakon juna.
Jihohin da lamarin ya fi kamari dai sun hada da Neja da Kaduna da Zamfara da Katsina da Sakkwato da kuma Kebbi.
Wadannan Jihohin dai na da dazuzzuka masu zurfi sosai da ’yan ta’addan kan shiga cikin sauki ba tare da samun tarnaki ko tirjiya daga jami’an tsaro ba.
Binciken Aminiya ya gano cewa akwai akalla kungiyoyin ta’addanci uku da ke gudanar da harkokinsu a Jihohin da ayyukan ’yan bindigar ya fi shafa inda suka kara neman gindin zama.
Wani masani kuma mai bincike kan ayyukan ta’addanci a Cibiyar Bincike ta Tony Blair da ke Landan, Audu Bulama Bukarti ya shaida wa Aminiya a karshen mako cewa ayyukan kungiyar Boko Haram a yankin Arewa maso Yamma ba karamar barazana ba ce ta kowacce fuska.
Sai dai Hukumar Tsaron Farin Kaya ta DSS taki cewa uffan a kan bukatar wakilinmu ta neman tsokacinta kan wannan batun.
Hanyoyin da suke bi wajen dibar sabbin mambobi
Majiyoyi masu tushe wadanda suka yi magana da wannan jaridar bisa sharadin ba za a bayyana sunansu ba sun ce tuni kungiyoyin Boko Haram da ISWAP suka jima suna kokarin kafa sansanoni a Jihohin Arewa maso Yamma da kuma Neja, a kokarin da suke yi na kara raba hankalin jami’an tsaro.
Kungiyar Ansaru dai wacce kafin wannan lokacin take da babban sansaninta a Okene a Jihar Kogi an ce ita ce ta zama kanwa uwar gami wajen hada kan wadannan ’yan bindigar da ke karkashin jagorancin Dogo Gide a dajin Kuyanbana a Jihar Kaduna.
“Kungiyar Ansaru ta jima a Arewa maso Yamma tun 2012, amm a ’yan shekarun nan suna kokarin dawo wa da karfinsu. Daga cikin irin shirin da suke yi akwai dibar ’yan bindiga daga yankin. Wannan ne dalilin da yasa suka fara yin wa’azi da Fillanci suna kuma ba manoma rance,” inji Bulama Bukarti.
A wani sakon murya da aka fitar a kwanan nan na tattaunawa tsakanin Dogo Gide da wani wanda ya kira waya game da batun sace daliban Birnin Yawuri, an jiwo mutumin na bayyana kansa da Abu Abdallah, irin sunayen da ’yan Boko Haram suka fi amfani da shi.
Ko da yake Aminiya ba ta kai ga tantance sahihancin sakon ba, amma wata majiya wacce ta yi mu’amala da Dogo Gide a baya ta tabbatar da cewa muryar tasa ce.
Wani jami’in tsaro a Jihar Zamfara ya ce ko a kwanan nan sai da wasu ’yan ta’adda da ake kyautata zaton ’yan Boko Haram ne suka sauka a dajin Dumburum da ke Karamar Hukumar Zurmi ta Jihar, kuma jagoran ’yan bindigar yankin da aka fi sani da Alhaji Shingi ne ya sauke su inda suka kafa sansani a dajin.
Wuraren da suka kafa sansanoni
Aminiya ta gano cewa ’yan kungiyar ta Boko Haram sun kafa sansanoni a dajin Wawa da ke Jihar Neja, inda suka mayar da ’yan bindiga da dama daga dazukan Zamfara karkashinsu.
Wani mazaunin yankin wanda ke da ’yan uwa a can ya ce yanzu haka ’yan ta’addan sun fara kafa wa mazauna garin dokoki.
’Yan bindigar da ke dajin na Wawa dai na karkashin shugabancin Dogo Gide, wanda ke kula da dajin Dangulbi a Jihar Zamfara, da ma wasu sassa na yankin Zuru a Jihar Kebbi.
Dogo Gide dai na daya daga cikin wadanda suka jagoranci tattaunawa domin sako daliban makarantar sakandiren Kankara a Jihar Katsina.