Hukumar Sibil Difens (NSCDC) ta kama mutane 42 kan zargi da sata, sojan gona da mallakar haramtattun makamai da sauran laifuka a Jihar Borno.
Kwamandan NSCDS a jihar, Musa Faruk ya ce jami’an hukumar sun kama mutane 11 kan yin fasa-kwaurin karafa da wasu biyar kan yin sojan gona a matsayin sojoji, ’yan sanda da jami’an hukumar inda aka kwato katunan shaida aikin hukumomin tsaron na bogi daga hannunsu.
An kuma kama wasu bakwai bisa zargin yin jabun katin tallafin gwamnatin JIhar Borno a kananan hukumomin Dikwa da Mafa.
- An kama hadimin Gwamnan Kano kan satar abincin tallafi
- Muguwar kaddara ta sa na shiga Kannywood —Hafsat
- TRUST TV ya zama Gwarzon Kafofin Yada Labarai na 2023
“A kwanakin baya ne Gwamnan jihar ta Borno ya bada kayayyakin tallafin abinci wanda sai an nuna katunan ne mutum zai iya amfana.
“Hakan ne ya sa wadannan bata-gari suka buga irin wadannan katuna na jabu da aka kama su da katinan guda 50 da suke sayar da kowanne a kan Naira 11,000,” in ji shi.
Faruk ya ce binciken farko ya nuna ’yan damfara suna gudanar da munanan ayyukansu ne da hadin bakwai wasu bata-garin ’yan sanda da bayan dubunsu ta cika an yanke musu hukunci.
Ya ce rundunar ta kama wasu mutane 16 kan mallakar muggan makamai ba bisa ka’idar ba tare da kafa wata fitacciyar ’yan daba mai sun a “Marlians”.
“An kama su ne kan zargin tada kayar baya da haifar da fitina a cikin dare suke kuma hana zaman lafiya a cikin birnin Maiduguri,” in ji shi