✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnan Kano ya kama hadiminsa da satar abincin tallafi

Babban hadimin gwamnan Kano ya shiga hannu kan karkatar da abincin tallafin da gwamnatin jihar ta bayar a raba wa talakawa

An cafke wasu mutum biyu kan zargin karkatar da kayan abincin tallafin da Gwamnatin Jihar Kano ta bayar.

’Yan sanda sun cafke wani hadin gwamnan jihar mai suna Tasiu Al’amin-Roba tare a wani mutum suna sauya wa masara da shinkafar tallafin da nufin sayarwa.

Dubun waɗanda ake zargin ta cika ne bayan Gwamna Abba Kabir Yusuf ya kai ziyarar ba-zata ga wani suton da suka ɓoye kayan abincin abincin tallafin a unguwar Sharada.

Gwamnan ya gane wa kansa yadda waɗanda aka zargin suke juye shinkafa da masarar tallafin daga kananan buhunamasu cin kilo 10 da tambari da gwamnatin jihar, suna mayarwa cikin manyan bahuna.

An kuma samu waɗanda ake zargin, da emtin manyan buhuna 200 da ake zargin za su mayar da abincin tallafin ciki domin su sayar wa ’yan kasuwa.

Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Kano, Ussaini Muhammad Gumel ya ce rundunar ta fara bincike domin gano yawan buhuna da waɗanda ake zargin suka riga suka sayar.

Ya kara da cewa za a gurfanar da su a gaban ƙuliya da zarar rundunarsa ta kammala bincike.