Hukumar Kashe Gobara ta jihar Kano ta ceto rayukan mutum 132 da dukiyoyin da darajar miliyan 16.5 a lokuta daban-daban da hadarin gobara ta ritsa da su a watan Oktoban 2020.
Wannan yana dauke ne cikin wani jawabi da kakakin hukumar, Saidu Muhammad ya sanyawa hannu a ranar Laraba.
- Gobara ta cinye dakunan kwanan dalibai 16 a Kano
- Gobara ta kone wani sashen gidan wuta na Dan-Agundi dake Kano
- Gobara ta tashi sau 15 cikin kwana 4 a Kano
- Gobara ta cinye daki da shaguna 7 a Kano
Sai dai yace mutane takwas sun rasa rayukansu tare da asarar dukiya ta kimanin miliyan N8.6 a Jihar.
Ya kara da cewa hukumar ta kai dauki a wurare 86 da suka samu rahoto.
A cewarsa bincike ya nuna cewa ana samun yawaitar gobarar ne sakamakon rashin iya amfanin da tukunyar gas, da kuma kayan wutar lantarki.
Muhammad ya ja hankalin mutane dasu ke kokarin kiran hukumar tasu akan lokaci a duk lokacin da aka samu gobara a wani yanki na jihar.