✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Yadda ’yan kato-da-gora suka fatattaki ’yan bindiga a kauye

Ya ce daya daga cikin ’yan kato-da-gorar yankin ne ya fita da niyyar yin fitsari sai ya hangi hasken fitilar ’yan bindigar

Yunkurin wasu ’yan bindiga na yin garkuwa da wasu mutane a gundumar Kekeshi dake Karamar Hukumar Abaji a Babban Birnin Tarayya Abuja ya gamu da tarnaki daga ’yan kato-da-gorar yankin.

A makon da ya gabata ne dai aka sace mutum hudu a yankin, ciki har da wani yaro mai kimanin shekaru 13, kuma har yanzu suna hannun maharan wadanda ke neman Naira miliyan 10 a matsayin kudin fansarsu.

Wani mazaunin yankin da bai amince a ambaci sunansa ba ya ce lamarin ya faru ne ranar Juma’a da misalin karfe 9:22 na dare.

Ya ce daya daga cikin ’yan kato-da-gorar yankin ne ya fita da niyyar yin fitsari sai ya hangi hasken fitilar ’yan bindigar a kusa da wasu gidaje dake gefen garin.

“Ganinsa da suka yi ne ya sa suka haske shi da cocilar daga nesa,” inji majiyar.

Ya ce daga nan ne kuma daya daga cikin maharan ya yi harbi a iska ganin yadda yake ta hango hasken cocilolin ’yan kato-da-gorar da ma na sauran mazauna yankunan ba kakkautawa.

Majiyar ta kuma ce karar harbe-harben bindigogin ’yan kato-da-gorar ne ya tsorata maharan har suka cika wandonsu da iska.

“Daga nan ma sai da suka ci gaba harbinsu, har sai da suka tabbatar sun fita daga yankin sannan sun gudu,” inji majiyar.

Sai dai Kakakin Rundunar ’Yan Sandan shiyyar Abuja, ASP Maryam Yusuf ba ta amsa rubutaccen sakon da wakilinmu ya aike mata domin tabbatar da harin bay a zuwa lokacin hada wannan rahoton.