✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda ’yan fashin banki suka kashe mutum 4 a Kogi

Sun tarwata ofishin ’yan sanda biyu a aika-aikan da suka yi a Jihar Kogi.

An kashe mutum hudu wasu da dama kuma sun jikkata bayan ’yan fashi sun kai hare-hare a wasu bankunan kasuwanci uku a Jihar Kogi.

’Yan fashin sun kai hare-haren ne da rana tsaka a yayin da mutane ke cikin gudanar da harkokinsu, washegarin da ’yan bindiga suka yi garkuwa da mahaifiyar Shugaban Ma’aikatan Gidan Gwamnatin Jihar.

Dandazon ’yan fashin da suka kai harin a kan babura da motoci sun kuma lalata ofisoshin ’yan sanda tare da fatattakar ma’aikatan da ke ofisoshin.

’Yan fashin bankin sun kai hare-haren ne a unguwannin, Egbe  da Odo Ere da ke Karamar Hukumar Yagba ta Yamma da misalin karfe uku na rana, suna barin wuta, wanda hakan ya sa mutane suka yi ta ranta a na kare.

Rahotanni sun ce sai dai ’yan fashin bankin suka fara zuwa ofishin ’yan sanda da ke Egbe suna harbi babu kakkauta sannan suka tayar da ofishin ta hanyar amfani da abin fashewa, ’yan sandan da ke wurin kuma suka arce domin kubuta da rayukansu.

Shaidu sun ce an tsinci gawar mutum biyu a kan titi a garin Egbe da aka kai hari a harabar reshen bankin First Bank da ya daina aiki.

Wata majiya ta ambato shugabannin wani bankin zamani a garin suna cewa an kashe mutum daya, wasu da dama da suka ji rauni kuma ana jinyar su a Asibitin Cocin ECWA da ke garin.

Bayan harin ne Egbe ne ’yan fashin suka wuce zuwa garin Odo Ere, hedikwatar Karamar Hukumar Yagba ta Yamma, inda suka ci karensu babu babbaka a reshen bankin UBA da ke garin bayan a nan ma sun lalata wani ofishin na ’yan sanda.

An tabbatar da tsintar gawar mutum biyu a Odo Ere  a yayin da jama’a ke kokarin tserewa bayan maharan sun bude wuta.

Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Kogi, Idris Dauda Babban, ya tabbatar da aukuwar lamarin, wanda ya ce rundunar tana tattara kan bayanai a kai.