Magoya bayan sojojin da suka yi juyin mulki a kasar Burkina Faso sun gudanar da gangamin nuna goyon baya kan hambarar da gwamnatin kasar.
Al’ummar kasar na murnar juyin mulkin ne a daidai lokacin da Kungiyar Bunkasa Tattalin Arzikin Kasashen Yammacin Afirka (ECOWAS) da Majalisar Dinkin Duniya suke la’antar juyin mulkin.
- Iyayen mutumin da ake tuhuma da kashe Hanifa sun tsere
- NAJERIYA A YAU: Zaben 2023: Wa zai kai Najeriya tudun mun-tsira
Dubban magoya bayan sojojin ne suka fito kan titunan Ouagadougou, fadar gwamnatin kasar, dauke da tutar kasar suna bushe-bushen sarewa a yayin gangamin nasu na nuna goyon baya ga sojojin da suka kifar da gwamantin Shugaba Roch Christian Marc Kabore.
Daya daga cikin masu shirya gangamin, Lassane Ouedrago, ya ce sun dade suna kira ga Shugaba Kabore da ya sauka daga kujerarsa saboda gazawarsa wajen magance kashe-kashen da ake yi a cikin kasar amma ya yi kunnen uwar shegu.
A ranar Litinin ne, dakarun sojin Burkina Faso suka kame Shugaba Christian Kabore, wanda jama’ar kasar suka sha yi wa zanga-zanga a kan gazawarsa wajen dakile hare-haren ’yan ta’adda a kasar.
A halin yanzu dai kasar na hannun Laftanar-Kanar Paul-Henri Sandaogo Damiba wanda shi ne ya jagorancin hambarar da Gwamnatin Kabore, sannan ya sa aka tsare shi.