Daya daga cikin jagororin ’yan bindigar da suka addabi Jihar Katsina, mai suna Ado Sarki, ya bayyana tubansa tare da mika wa gwamnati makamansa.
Ado da yaransa na daga cikin masu addabar Kananan Hukumomin Safana da Batsari, yankunan da hare-haren ’yan bindiga suka yi wa mummunar illa a Jihar.
- A fara duba watan Ramadan daga ranar Litinin – Sarkin Musulmi
- Gwamnatin Tarayya za ta fara aikin jirgin kasa daga Ibadan zuwa Kano
Ado wanda ya jagoranci wadansu daga cikin yaransa wurin mika makaman, ya yi alkawarin cewa sun yi hannun riga da ayyukan ta’addanci, ko da a bakin ransu ne.
Ga dai abin da Adon ya ce a lokacin mika makaman ga Kwamishinan ’Yan Sanda na Jihar, CP Sanusi Buba.