✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

‘Yadda ’yan bindiga suke karbar haraji daga gare mu’

"Ana tilasta wa mutane ko su biya haraji ko su yi aikatau a gonakin barayin."

Matsalar tsaro da ta ta’azzara a Arewa maso Yamma, inda ’yan bindiga suke kisa da sace mutane da dabbobinsu mutane da dama suke tserewa daga karkara, hakan ya sanya wadansu ke ganin tamkar barayin suna tafiyar da kwarya-kwaryar gwamnati ce a wadannan yankuna.

Wani bincike da Aminiya ta yi a Kananan Hukumomin Danmusa da Batsari da Dandume da Dutsinma a Jihar Katsina ya gano kauyuka da dama inda mutane suka saura a yankunan da suke makwabtaka da dazuka ko dai ana tilasta musu ba da haraji ga barayin kafin su yi noma ko kuma suna aikatau a gonakin barayin.

A tattaunawa da Aminiya, Sarkin Ruma, Hakimin Batsari, Alhaji Tukur Mu’azu, ya ce dagatan gundumomi takwas na Batsari sun tsere zuwa cikin garin Katsina domin samun mafaka.

Hakimin ya ce, “Babu wanda yake zaune a kauyukan da suke kusa da dazukan nan in ba wanda ba ya da komai ba, ko sun san ba abin da za su samu daga gare shi, ko wadanda suke hada kai da su. Sun hana manoma shuka gonakinsu sannan babu shanun da suka rage. Yanzu haka garin Batsari ya yi cikar kwari da ’yan gudun hijira,’’ inji Sarkin Ruma.

Ya tabbatar wa Aminiya cewa shekara uku ke nan shi kansa ya hakura da noma gonarsa mai kimanin kadada biyu inda barayin suke amfani da gonar.

Muhammed Auwal mai shekara 55, manomi a kauyen Nahuta a Batsari ya ce tun bara barayin suke tilasta wa manoman kauyen biyan haraji domin noma gonakinsu.

“Bana sun bukaci kauyen da yake kusa da mu na Kasai, da mutanen kauyen su hada musu kudin taki kuma dole sai da suka hada.

“Bara kowane magidanci a Nahuta sai da ya biya Naira dubu, inda muka hada fiye da Naira miliyan biyu ga barayin sannan muka kai musu kudin kafin su kyale mu yi noma. Amma a bana, mun yi sa’a ba su nemi haraji daga wajenmu ba, sai dai har yanzu kauyukan da suke kewayenmu na fama da haka,” inji shi.

Wani dattijo mai suna Malam Tasi’u Liman mai shekara 70 a kauyen Batsarin-Alhaji, ya ce shi ya biya harajin da kuma saya wa barayin taki.

Ya ce, “Bara kowanenmu ya biya akalla Naira 2000 kuma a watan Yuli mun tara kudin saya musu taki. Kowane mai garman shanu sai da ya ba da Naira 2000 wanda ba ya da garma kuma Naira 500.

“Kudin taki kuma kowane baligi sai ya ba da Naira 200 zuwa 500. Mun kai musu kudin cikin daji, amma duk da haka sukan zo su kwace maka waya ko kudi ko duk wani abu mai muhimmanci. Yanzu wajen mako uku ke nan ba na iya zuwa gona.”

Dahiru Isma’il, a garin Batsari karamin manomi ne da bai ambaci sunan kauyensa ba, saboda tsaro, ya ce tilas ya bar gonarsa mai kadada uku. Ya ce, “Za a tilasta maka yin aiki a gonakinsu kafin ka je gonarka. Na san mutane da dama wadanda aka tursasa wa yin noma da sauran ayyukan a gonakin barayin. A kauyenmu ba sa tambayar haraji sai dai mu je mu yi musu aiki.”

Sani Muslim Batsari, Shugaban Kungiyar Ci gaban Batsari (BALDA), ya ce. “Ina noma kusan buhu 300 a baya; amma yanzu bai fi buhu 50 nake nomawa a gonata da ke kusa da gari ba.

“Barayin nan sun mamaye dazukan sun share suke nome su.

Wadansu daga cikinsu sukan noma buhu 3,000. Wadansu kauyawa sun shaida mana cewa barayin sun kwace musu gonaki ba tare da biyan ko sisi ba. Ayyukansu suna matukar shafar zamantakewarmu; sun haddasa tsada da karancin amfanin gona sannan ga rashin ayyuka ga matasanmu saboda manyan manoman da suke samar musu da ayyuka duk sun guje wa gonakinsu,” inji shi.

Da Aminiya ta ziyarci kauyen Gurzar Kuka a Karamar Hukumar Danmusa, Audu Sada, manomi ya bayyana yadda dan uwansa ya cika Naira 20,000 a kan Naira 200,000 da barayin suka nema a matsayin haraji kafin su kyale mutanen kauyen su noma gonakinsu.

Ya ce, “Kwanaki, sun shigo nan da rana rike da bindigogi kirar AK-47, suka bukaci mu hada musu Naira 200,000 kafin su bari mu yi noma. Sun yi mana alkawarin ba za su sace kowa ba idan muka biya kudin; yayana ne ya ba da cikon Naira 20,000.”

Alhaji Mato (ba sunansa na ainihi ba) manomi ne a kauyen Kwanar Kura a Karamar Hukumar Dandume ya bayyana yadda a farkon damina ya ba da kudi ga barayin kafin suka bar shi ya shuka gonarsa, sannan sun sake bukatar karin kudin lokaci da aka fara noma.

“A farkon damina, sai da na biya su Naira 50,000 kafin su bari in shuka dawa a gonata. Sannan kwanan nan suka kora masu noman da na tura su yi mini noma inda suka yi musu barazana. Sun ce kudin da na bayar sun gama aiki, don haka sai na sake ba da Naira 50,000 kafin su bar ma’aikatan da na tura su ci gaba da aiki; babu abin da na iya illa in biya saboda babu wanda ya isa ya nuna musu yatsa,’’ inji shi.

Aminiya ta gano cewa kwanakin baya wadansu manoma biyu sun gamu da fushin barayin inda suka harbe su a kauyen Kurechi a Karamar Hukumar Dutsinma sakamakon kin biyan wani jagoran barayin mai suna Habibu harajin noma gonakinsu.

Daya daga cikinsu ya rasu sakamakon harbin, dayan kuma har yanzu yana jinya a asibiti. Sannan manoma da dama a yankin sun gudu daga gonakinsu, kamar yadda Aminiya ta gano.

Har wa yau, manoma da dama sun shaida wa Aminiya cewa Habibu yana tilasta musu biyan haraji daga Naira 50,000 zuwa 100,000 kafin su yi noma ko a sace su.

Wata majiya a kauyen Kurechi da ba ta so a ambaci sunanta ta shaida wa Aminiya cewa jagoran barayin sananne ne a wajensu inda a farko ya yi alwashin ba zai bari kowa ya yi noma ba har karshen daminar bana idan ba a biya shi haraji ba a kauyukan Kurechi da Sana’wa da Jan-Ruwa da kauyukan makwabta.

Dokta Yakubu Abba Abdullahi, shi ne Babban Mai bai wa Gwamnan Jihar Katsina Shawara kan Harkokin Noma, ya tabbatar wa Aminiya cewa ayyukan ’yan bindigar sun yi matukar illa ga harkokin noma a jihar.

A cewarsa, “Mun kiyasta gonaki 5,884 masu girman kadada dubu 58 da 330 aka yi watsi da su sakamakon rashin tsaro. Sannan an kai hare-hare har sau 590, yayin da aka sace shanu dubu 159 da 613, kuma mutum dubu 156, suka tsere daga muhallansu, galibi a yankunan karkara. Sannan lamarin ya shafi manoma dubu 226 da 650 da suka noma kadada 6, 800 a bara; tabbas hakan ya shafi amfanin gonar da ake samu a jihar da kashi 30 a barar.

“A bana kuma daga Janairu zuwa Yuni, lamarin ya sanya an yi watsi da kadada dubu 23 da 333 na gonaki 2, 924. Sannan an kai harehare da sace mutane sau 651; inda aka sace shanu dubu 17 da 733 – ana tsammanin hakan zai shafi kashi 17 na ayyukan gona a bana a jihar.

Ya ce, “Ko da yake, yanzu za a iya cewa lamarin ya dan inganta saboda rahotannin da muke samu suna nuna cewa gonakin da a da ba a iya zuwa yanzu ana zuwa sakamakon hare-hare ta sama da sojin Najeriya ke kaddamarwa a yankunan.”

Ya tabbatar da cewa kananan hukumomin jihar 12 ne ayyukan ’yan bindigar ya fi shafa, wato Batagarawa da Batsari da Danmusa da Faskari da Dutsenma da Jibiya da Kankara da Kurfi da Sabuwa da kuma Safana; yana mai cewa wadannan kananan hukumomin su ne kashin bayan harkokin noma a jihar.

Ya tabbatar wa manoma cewa gwamnatocin jiha da na tarayya suna kokarin magance lamarin yana mai nanata cewa yanzu manoma sun koma gonakinsu a Kankara da Sabuwa wadanda a da ba a iya noma a yankunan.

Kungiyar Manoma ta AFAN Alhaji Kabiru Ibrahim, Shugaban Manoma ta Najeriya (AFAN), ya tabbatar wa Aminiya cewa kungiyar tana sane da batun karbar harajin da ’yan bindigar suke yi daga manoman yankunan karkara a Jihar Katsina, inda ya yi gargadin cewa hakan babbar barazana ce ga wadatar abinci a kasar nan.

Ya ce, “Tabbas mun samu korafe-korafe daga manoma cewa a wasu lokutan sukan biya haraji ga barayin dajin kafin a kyale su su yi noma. Hakika hakan babbar barazana ce ga wadatar abinci; kuma a sani cewa akwai babbar alaka a tsakanin wadatar abinci da rashin tsaro, sannan da zarar akwai matsalar tsaro, to babu yadda za a iya samun wadatar abinci.”

“A lokuta da dama mun ji cewa manoman ba sa iya zuwa gonakinsu har sai sun cim ma yarjejeniya da barayin dajin. Sai dai ba mu san ko nawa suke bayarwa ba; amma tabbas sukan cim ma yarjejeniya da barayin a farkon damina.

“Muna karfafa gwiwar mambobinmu cewa su zage damtse wajen noma domin ciyar da mutum miliyan 200 da ke kasar nan. Lokacin da aka gabatar da wadannan korafe-korafe mun je muka bukaci gwamnati ta tabbatar da samar da tsaro ga manoman,” inji shi.

Ya kara da cewa gwamnati tana yin bakin kokarinta amma akwai bukatar ta kara kaimi.

Ra’ayin masani

Dokta Sani Yakubu Gombe, kwararre ne a harkar noma, ya ce, “Idan manoma suna bayar da haraji bisa ka’ida ko ta haramtacciyar hanya hakan zai shafi kudi da aikatau na noman wanda kuma zai haifar da hauhawar farashin amfanin gona, kuma hakan zai rage ribar da manoman za su samu a karshen kaka.

“Ta fuskar zamantakewa kuwa, fargaba da tsoro na rashin kwarin gwiwar iya zuwa gonarka zai haifar da damuwa a ruhi da dimauta saboda babu kwarin gwiwa a tare da manomin don haka zai rasa karsashin yin noma,’ inji shi..

Ya ce, “A mahangar cim-ma muradun dorewa (SDGs) da Najeriya ke hankoron cim-mawa zuwa shekarar 2030; biyun farko kai-tsaye sun shafi kawar da yunwa da rage kaifin talauci; to, idan wadannan manoman ba su yin noma, samar da abinci zai yi wahala.

“Kamar gwamnati ba ta daukar matakan dakile matsalar daga tushe. Wadannan mazauna karkara da ba a samar musu da muhimman kayan bukatun rayuwa domin manoman su ci gaba da zama a inda suke da karfafa gwiwar matasa marasa ayyuka a karkara su zauna domin samun abin yi na ciyar da iyalansu sannan su yi tunani mai kyau; alal hakika za mu ci gaba da ganin bayyanar miyagun abubuwa irin su ’yan bindigar nan da masu sace mutane da sauran matsalolin tsaro.”

Martanin ’yan sanda

Duk da tabbacin da mazauna yankunan karkara a wadannan kananan hukumomin suka bayar cewa sukan biya haraji ga ’yan bindiga, Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Katsina, SP Gambo Isah, ya musanta korafin nasu. Ya ce, “Ba mu samu korafin da ke nuna ’yan bindiga suna karbar haraji daga manoma ba. A ina hakan ya faru; kuma wadanne mutane aka bukaci su biya harajin?”

Wannan labarin Gidauniyar Daily Trust da MacArthur Foundation suka dauki nauyinsa.