Ana zargin masu garkuwa da mutane sun kai farmaki har gida inda suka sace wani lakcara na jami’ar Abubakar Tafawa Balewa, Farfesa Aliyu Muhammad tare da harbin ’ya’yansa biyu a garin Zariya.
Lamarin ya auku ne a ranar Lahadi da daddare inda maharan suka bude wuta kan mai uwa da wabi a kofar gidan Farfesan da ke Unguwar Wusasa.
- ‘Babu bukatar shaidar gwajin COVID-19 daga wurin dalibai yayin komawa makaranta’
- Mutum miliyan 15 na ta’ammali da kwaya a Najeriya — Buba Marwa
Maharan sun kashe Abdul’aziz Aliyu dan Farfesa Aliyu wanda shi ne shugaban sashin koyar da aikin gona na Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa da ke Bauchi.
Sun kuma harbi wani dan kaninsa mai suna Abubakar Kabir inda a halin yanzu yake jinya a gadon Asibiti kamar yadda Aminiya ta tabbatar.
Wani dan Farfesan na fari mai suna Dokta Khalifa Usman Aliyu, ya yi wa Aminiya bayanin yadda lamarin ya faru y ace, “A ranar Lahadi da misalin karfe goma da rabi na dare mahaifin na ya dawo gida nima na dawo sai na tarar da shi ya fito rufe gilashin motarsa domin yana shirin komawa bakin aiki a Bauchi gobe Litinin.”
“Bayan shiga ta gida kenan sai karar harbe-harbe ta ko ina a cikin gidanmu wanda hakan ya sanya na haura ta baya na tsallaka na kutsa wani wuri na buya, sai na fara kiran makwabta ta waya don su kawo mana dauki domin maharan sun kwashe kusan awa daya suna cin karensu babu babbaka.”
“Bayan lafawar harbin sai na kira kaninsa wanda ake kira Bona domin inji inda yake da kuma halin da ake ciki sai ya ce ai sun kashe kanimu kuma sun tafi da Baba.”
Dokta Khalifa ya kara tabbatar wa da Aminiya cewa “tsawon wannan lokacin da aka kwashe, babu wani jami’in tsaro ya zo kawo dauki har zuwa lokacin da maharan suka gama abinda suke yi suka tafi.”
Wani kanin Farfesan mai suna Kabir Aliyu wanda ya ke zaune a babban gidan su ya yi wa Aminiya karin bayani cewa, “Ni kaninsa ne, ni ne nake binsa domin mahaifammu daya da shi, mun gama tattaunawar yadda zai koma wurin aikinsa washe gari domin ni direba ne.”
“Ya ce zan kwasar masa kaya shi kuma da mai dakinsa za su tafi a motarsa tare don haka na wuce yara a kofar gida suna hira bayan minti kadan sai yaran suka shigo gida a guje sai karar harbi ta ko ina kamar ana yaki domin harsashi duk ya huda mana ginin kofar gida.”
“Bayan mun ji harbin ya lafa sai muka fito muka tarar sun harbe mana yara biyu daya wanda aka kashe Abdul’aziz dan yayan nawa ne shi kuma wanda bai mutu ba Abubakar ni ne na haifeshi, kuma sun tafi da shi yayan nawa Farfesa Aliyu.”
Wani jami’in kungiyar ’yan Bijilanti wanda mazaunin unguwar ne ya ce maharan sun kwashe tsawon awa daya suna harbe-harbe a unguwar kafin su kama gabansu.
Ya ce, “irin makaman da suke dauke da shi ba kowa zai iya tunkarar su ba, kuma wannan shi ne karo na uku da suke kawo wa unguwar hari suna sace mutane, kuma idan ma sun sato ta nan suke wucewa domin nan ya zame musu hanya.”
Ya ce, “ko malamin makarantar kimiya da fasaha da aka sace kwanakin baya ta nan suka wuce da shi sannan kuma suka sace matar wani kabilar Ibo da kuma wata mata da kauwarta duk a nan yankin namu, domin muna makwabtaka da unguwar madaci kuma nan da Dala kuma kan hanyar su ne.”
Mai Unguwar Kuregu da ke Wusasa, Alhaji Ahmadu Amfani ya ce shi Farfesa dan majalisan masarautar Wusasa ne domin shi ne wazirin masarautan Wusasa don haka a lokacin da lamarin ke faruwa sun yi kokarin sanar da jami’an tsaro domin kawo dauki.
Ya yi kira da al’ummar da ake tare da su su rika kokarin sa ido a kan abin da ke kaiwa da komowa, da kuma abokan mu’amalarsu gami da kokarin sanar bayanai a kan abin da basu yarda da shi ba.
Yayin da Aminiya ta nemi jin ta bakin mai magana da yawun rundunar ’yan sandan Jihar Kaduna, ASP Aliyu Mohammed Jalige, ya yi alkwarin waiwayar wakilinmu a yayin da a lokacin tattara wannan rahoto yana kan hanyarsa ta dawowa garin Kaduna.