Al’ummar Matane, kauyen su Sakataren Gwamnatin Jihar Neja, Ahmed Ibrahim Matane, sun arce bayan ’yan bindiga sun far wa garin suna kone-kone.
Hantar mutanen Matane ta kada ne bayan ’yan bindigar sun shiga garin da safiyar ranar Talata suna banka wa gidaje da kantuna da sauran kadarori wuta. Daga nan suka shiga wasu kauyuka suka ci gaba da aika-aikar.
Kwamishinan Kananan Hukumomi da Tsaron Cikin Gida na Jihar Neja, Emmanuel Umar, ya ce maharan sun kona gidaje da dama da kuma kantuna da sauran abubuwa a harin na Matane.
Kwamishinan, ya kara da cewa maharan sun rika bi kauye-kauye suna cin karensu babu babbaka, amma ya ce ba shi da tabbacin yawan mutanen da harin ya ritsa da su.
Ya ce maharan sun kuma kai hari a unguwar Bamba-Lamba da ke Gabashin Kontagora da kuma wasu kauyuka.
Wani mazaunin Bamba-Lamba mai suna Hashimu Ahmed ya shaida wa wakilimu cewa ’yan bindiga sun kai wa garin nasu hari ne da misalin karfe 5 na yamma, suka kone shi kurmus bayan sun yi masa kawanya.
’Yan bindigar, “Sun zagaye kauyenmu, amma na samu na tsere tare da iyalaina zuwa garin Kontagora. Sun kona gidajenmu, yanzu a fili muke kwana a Kontagora. Muna bukatar taimako.”
Kwamishinan Kananan Hukumomi da Tsaron Cikin Gida na Jihar Neja, Emmanual Umar, ya bayyana cewa tun ranar Litinin jami’an tsaro ke bin sawun maharan bayan da suka tare hanyar da ta taso daga Minna zuwa Suleja.
Ya ce ’yan bindigar suna cikin takura saboda jami’an tsaro sun tare hanyar da ita kadai suke iya bi su tsere daga Jihar Zamfara su shigo Jihar Neja.
Ya kara da cewa a halin yanzu ’yan bindiga suna kwasar kashinsu a hannun jami’an tsaro bayan da aka datse iyakokin kananan hukumomin Rafi da Mariga, a yayin da jami’an tsaron suke ci gaba da karkashe bata-garin.