’Yan bindiga sun kashe mafarauta 17 tae da garkuwa da wasu 25 a Dajin Tsayau da ke Karamar Hukumar Jibia a Jihar Katsina.
Wasu shugabannin maharba a Jibia da suka bukaci kar a bayyana sunansu sun ce abin ya faru ne a kusa da garin Tsayau ne a ranar Laraba.
- Daliban firamaren Kaduna sun tsere daga hannun ’yan bindiga
- ’Yan bindiga sun sace limami da mutum 10 a Suleja
- Matar aure ta kashe danta, ta kona mijinta
- Yadda kananan yara suka rasu yayin wasa a cikin fada
“An tabbatar mata cewa an kashe 17, mutanen da suka je neman ’yan uwansu sun tabbatar cewa sun ga gawarwaki 17,” inji su.
Aminiya ta gano cewa maharban sun shiga maboyar ’yan bindigar ne a yayin da suke farauta, su kuma ’yan bindigar suka bi su a kan babura suka kashe 17, suka kame 25.
Majiyarmu ta ce ’yan bindigar sun bukaci a biya su Naira miliyan 50 kudin fansar mafarautan, amma da dangin maharban suka ce ba su da su sai suka ce musu su je gwamnati ta ba su.
Majiyar ta ce tun da farko wadanda suka san yankin sun shawarci mafarautan kar su shiga wurin amma suka ki, zuwansu kuma ya firgita iyalai da dabbobon ’yan bindigar, shi ya sa suka mayar da martani.
Ta ce an binne daya daga cikin gawarwakin 17 saboda ta riga ta fara rubewa.
“Mun kira gwamnati ta taimaka a ceto mafarautna. Ranar Lahadi sun kira mu cewa idan ba ma son su za su kashe su,” inji majiyar.
Wakilinmu ya gano cewa mafarautan sun fito ne daga yankuna daban-daban irinsu Katsina, Tsagero, Abukur, Kanyar Uban Daba, Mashi, Fadi Gurje, Ku Tare Dandagoro, Muduru da kauyukan Jibia.
Kakakin ’Yan Sandan Jihar Katsina, SP Gambo Isah, ya ce rahotannin da suka samu game da lamarin masu karo da juna ne, amma suna kara bincike don tabbatar da abin da ya faru kafin su fitar da bayani