Wasu ’yan bindiga sun hallaka hakimin Bajida da ke Karamar Hukumar Fakai ta Jihar Kebbi ta hanyar saran sa da adduna a kan hanyarsa ta komawa gida.
Rundunar ‘yan sanda ta jihar Kebbi ta tabbatar da kisan Alhaji Musa Muhammad Bahago, ta kuma ce tana iya bakin kokarinta domin ganowa da kuma gurfanar da masu laifin don su girbi abun da suka shuka.
Kakakin rundunar Nafi’u Abubakar ya ce, “Ko da yake ba mu riga mun kama kowa daga cikinsu ba, amma tuni jami’anmu suka dukufa wajen ganin mun kamo su”.
Wata majiya mai kusanci da iyalan marigayi Alhaji Musa Muhammad Bahago ta ce kwanaki kadan kafin kisan wasu matasa kusan 20 dauke da miyagun makamai sun yi wa fadarsa kawanya.
Majiyar ta ce maharan a kan babura sun je fadar basaraken kowannensu fuskarsa a lullube, kafin daga suka tafi da suka fahimci wanda suke fakon ba ya cikin gidan.
Da ya fahimci ana farautar rayuwarsa ne ya kai rahoto ga na gaba da shi a sarauta inda su kuma suka shawarce shi da ya takaita tafiye-tafiyen sai idan ya zama dole.
A ranar da iftila’in zai faru, hakimin ya tafi Zuru domin kai rahoton barazanar ga ‘yan sanda ne ‘yan bindigar da ke fakon sa suka far masa da sara da adduna har suka kashe shi.