✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Yadda direba ya kashe jami’in KAROTA a Kano

Direban hankado jami'in KAROTA daga saman mota ya fado nan take ya mutu.

Wani direba ya banke jami’in Hukumar Kula da Zirga-zirgar Ababen Hawa ta Jihar Kano (KAROTA) da mota wanda hakan ya yi sanadin mutuwar jami’in.

Lamarin ya faru ne a kan Titin BUK, tsakanin Kofar Gadon Kaya da Kofar Famfo a garin Kano, bayan jami’in na KAROTA ya bi wata tanka a safiyar ranar Talata.

Wani ganau ya ce jami’in na KAROTA ya bi tankar ne a guje ya dafe a kofarta bayan sun tsayar da motar amma direban ya ki tsayawa.

Ya ce bayan jami’in ya dafe a kofar motar, sai direbanta ya hankado shi, nan take kansa ya fashe, kwanyarsa ta zube a kan titi.

An bi direban motar amma ya ki tsayawa, kawo yanzu dai babu labarin ko an kama shi bayan ranta a na kare.

Kakakin hukumar KAROTA, Nabilusi Abubakar ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce an ajiye gawar jami’in a Asibitin Kwararru na Murtala Mohammed da ke Kano.

Abubakar, ya ce KAROTA ba ta da cikakken bayani, saboda tana jiran rahoton likitoci, kafin ta fitar da sanarwa ta musamman tare da ba wa manema labarai cikakken bayanin binciken da suka gudanar.

Tuni dai hukumar, karkashin jagorancin shugabanta, Baffa Babba DanAgundi, ta ba da umarnin baza koma don cafke direban da ya kashe mata jami’in.