Tun hambarar da gwamnatin dimokuradiyya a Jamhuriyya ta Farko ta zamanin su Sa Abubakar Tafawa Balewa, mulkin kasar ya rika kwan-gaba-kwan-baya a tsakanin sojoji da fararen hula.
Kuma duk da dawowar mulkin farar hula a 1999, wadansu suna ganin, tsofaffin janar-janar ne suke juya akalar siyasa da mulkin kasar nan.
- Manyan ’yan siyasar da suka karya alkawarin sauya sheka
- Najeriya A Yau: Taskun da ’yan gudun hijira ke ciki a Najeriya
Masu wannan ra’ayi suna zargin cewa tsofaffin janar-janar din ne suke ‘zabar’ wanda zai zama Shugaban Kasa da sauran manyan mukamai.
Suna kafa hujja da haka kan yadda a 1999 suka hana duk wani dan Arewa tsayawa takarar Shugaban Kasa.
Aminiya ta zanta da masana siyasa da ’yan siyasar kan yadda ake tafiyar da siyasar kasar nan.
Sojoji ne ke gudanar da siyasar kasar nan —Alhaji A.K. Daiyabu
Tsohon Shugaban Jam’iyyar AD ta Kasa, kuma Shugaban Rundunar Adalci ta Najeriya, Alhaji Abdulkarim Daiyabu, yana cikin masu ra’ayin cewa sojoji ne suke juya akalar siyasar kasar nan, inda ya yi zargin cewa su da yaransu ne kadai suke juyi a kan kujerun shugabancin kasar nan.
Alhaji Abdulkarim Daiyabu ya ce tun daga lokacin da sojoji suka yi wa ’yan siyasa masu imani da mutunci da tsoron Allah da tausayin bayin Allah juyin mulki to tun daga nan kasar ta shiga wani hali.
Ya ce bayan da sojojin suka mulki kasar nan na wasu shekaru, wannan ba ta ishe su ba, sai da suka yi kutukutun suka yi juyin siyasa daga ’yan siyasa farar hula zalla, masu imani da mutunci zuwa sojoji uku.
“Sojoji ne biyu suka fito da na ukunsu Olusegun Obasanjo daga kurkuku wanda aka daure shi rai-da-rai suka kakaba mana shi ya zama Shugaban Kasa na farar hula a 1999.
“Ba na mantawa a wancan lokacin sai da dan takararmu Olu Falae ya shaida wa kotu cewa kada su rantsar da Obasanjo domin dan kungiyar asiri ne, amma saboda son zuciya aka rantsar da shi haka.
“Har ta kai cewa hatta dan uwansu soja wanda ake ganin ya bambanta da su, Muhammadu Buhari ba ya goyon bayan abin da suke yi,” inji shi.
Ya ce, “Haka aka yi ta tafiya, sai baya kasar take yi har aka zo kan mulkin Shugaba Buhari wanda talakawa suka zabe shi domin su samu canji.
“Lura da sanin cewa Buhari ba zai ba su hadin kai ba, don haka ana zabarsa a 2015, aka yi masa abin da aka yi masa ya kamu da rashin lafiya kamar zai mutu.
“Iyakar abin da aka sanar da al’umma shi ne wai guba aka sanya masa a na’urar sanyaya daki, amma har yanzu ba a sanar da mu su wane ne suka yi laifin ba balle irin hukuncin da aka yi musu. Saboda lalacewar hukumar shari’a da mulki irin na sojoji.
“Iyakar tozarta mulki da al’ummar da ake yi wa mulkin ba ta wuce wannan ba.
“Matukar za a nemi ran Shugaban Kasa haka ba a kama kowa ba, ba a hukunta kowa ba, wane ne zai tsira? Wacce irin gwamnati ce haka? Idan kowa bai damu ba, wadanne irin mutane ne mu?”
Alhaji A. K. Dayyabu ya ce ’yan siyasar baya ba za su taba yarda sojoji su shiga siyasa ba.
“Na tabbata idan da ’yan siyasa farar hula masu imani da mutunci irin su Malam Aminu Kano da Sa Ahmadu Bello Sardauna Sakkwato da Sa Abubakar Tafawa Balewa da Cif Obafemi Awolowo suna da rai babu wani soja da ya isa ya zama Shugaban Kasa na farar hula bayan ya yi mulkin soja,” a cewarsa.
Ya ce, “Mafita daya ce ta rage wa dukkan wadanda aka zalunta na kowane bangare, su hadu su yi duk mai yiwuwa su ga an rusa duk jam’iyyun da aka yi mulki da sunansu.
“Wadanda suka janyo muka shiga dimuwa irin wacce muke ciki a yanzu.
“Duk wanda ya taba rike kowane irin mukami na amanar jama’a a titsiye shi ya dawo da duk dukiyar da ya mallaka tsakanin kudi da kadara ba bisa ka’ida ba.
“Sannan a hukunta masu kowane irin laifi. A harbe na harbewa, a rataye na ratayewa a bainar jama’a.”
Ya ce, “Alhamdulillah Allah Ya fara fahimtar da bayinSa na kwarai, matasa suna kusantarmu da neman makomar farar hula zalla masu tsoron Allah da tausayin bayin Allah a siyasace, musamman wadanda aka zalunta?
Ba tsofaffin janar-janar ke juya siyasar Najeriya ta bayan fage ba —Dasuki Nakande
Wani jigo a Jam’iyyar APC kuma tsohon Ministan Watsa Labarai da Sadarwa, Alhaji Ibrahim Dasuki Salihu Nakande, ya ce ba gaskiya ba ce, zargin da ake yi cewa har yanzu wadansu tsofaffin janar-janar ne suke juya siyasar Najeriya, ta bayan fage.
Alhaji Dasuki Nakande, ya bayyana haka ne a zantawarsa da Aminiya, inda ya ce gaskiyar magana, yanzu dimokuradiya ta zauna a Najeriya.
Domin an kafa jam’iyyu kuma kowace jam’iyya tana cin gashin kanta, bisa ga dokoki da ka’idojin da aka tsara, na yin zabubbukan fid da gwani, kamar yadda ta gada.
“Don haka, gaskiya wannan zargi ba haka yake ba,” inji shi.
Alhaji Dasuki Nakande, ya ce ziyarar da ’yan siyasa suke kai wa tsofaffin sojoji suna zuwa ne domin neman albarka.
Ya ce “Ai kowace jam’iyya tana son ta tafi da masu fada-a-ji, don haka za ka ga ’yan siyasa suna ziyartar malamai da sarakuna.
“Domin akwai shugabanci a ko’ina, kuma shugabannin nan suna da mutane da suke fada masu su ji.
“Don haka ’yan siyasa, suke zuwa wajen shugabanni da suke cikin al’umma, domin neman su samu amincewarsu da yardarsu, don a samu albarkar shiga takara.
“Haka abin yake ga ziyarar da ’yan siyasa, suke kai wa tsofaffin janar-janar.”
Alhaji Dasuki, ya ce ya kamata a fahimci cewa tsofaffin janar-janar din wadansu sun yi shugabancin kasar nan.
“Misali Janar Ibrahim Babangida ya yi shugabancin kasar nan na tsawon shekara takwas.
“Haka Janar AbdulSalami Abubakar ya yi shugabancin kasar nan, shi ya mika mulkin dimokuradiyar da muke ciki a kasar nan.
“Kuma har yanzu, yana shugabancin wani kwamitin tabbatar da zaman lafiya a duk zabubbukan da za a yi a kasar nan.
“Saboda haka, wadannan tsofaffin janar-janar ba za su rasa wasu shawarwari masu kyau da za su bai wa ’yan siyasa ba,” inji shi.
Tsoma bakinsu na da amfani —Sanata Shehu Sani
A zantawar Sanata Shehu Sani da Aminiya ya ce tsoma bakin tsofaffin sojoji a siyasar kasar nan na da amfani domin suna da tarihin Najeriya fiye da kowa.
“Ya danganta wace irin rawa suke takawa kuma a wace jam’iyyar siyasar?
“Siyasa ta PDP ko APC ko ta kasa gaba daya? Sannan wane ne daga cikin manyan sojojin?
“Na farko shi ne ’yan siyasa suna da matsala wurin hadin kansu saboda buri na mukaman da suke nema.
“Saboda haka a lokaci da yawa sai ka ga tsofaffin sojoji musamman wadanda suka yi mulki sukan shiga cikin irin wannan magana don kawo sulhu a tsakaninsu da kawo karshen husumar da kan faru.
“To, a hakan wadansu shigarsu kan yi masu dadi, wadansu kuma ba ta yi musu dadi — wannan ke nan.
“Akwai kuma irin su Janar AbdulSalami Abubakar za ka ga suna shiga ciki amma ba maganar siyasa ta jam’iyya ba, sukan shiga siyasa ta kasa da al’umuran zamantakewa.
“Shi yake shugabantar kwamitin zaman lafiya da sulhu na kasa, wadannan za ka samu hannunsu a ciki.
“Amma kan akwai tabbacin cewa suna da karfi suna kuma sa baki a cikin siyasa daga bayan fage kuma hakan ya yiwu ne saboda ’yan siyasa suna da wahalar hada kansu shi ya kawo shigar irin wadannan mutane domin samar da sulhu da sauransu. Don haka wannan ba karya ba ce.”
Sanata Shehu Sani ya kara da cewa, “Ya danganta ne da irin rawar da suke takawa ne idan na neman a samu sulhu ne a tsakanin ’yan siyasa babu laifi su tsoma baki a matsayinsu na tsoffafin sojoji za a iya sa su a matsayin dattawa saboda haka babu laifi a irin rawar da suke takawa da kuma kokarin da suke yi.
“Don saboda yanzu lokaci ya wuce da za a rika tunanin cewa za su kifar da gwamnati ko tilasta wa gwamnati yin abin da ba ta so kuma yana da kyau su yi amfani da basirarsu wurin shiga tsakani don samun sulhu a tsakanin jama’a.”
Game da batun hadin kan ’yan siyasa, Shehu Sani ya ce, “Su kansu tsoffafin shugabanni sojojin masu ba da shawara ba wai za su kasance da mu ba ne har abada domin da yawansu sun riga sun girma, wato akwai lokacin da za a kai babu su.
“Amma amfanin sa bakinsu shi ne sun san tarihin Najeriya sun kuma shiga cikin rikicin Najeriya sun san jiya, sun san yau, amfani da basirarsu na da fa’ida.
“Su kuma ’yan siyasa ai son mulki da son zuciya da yunwar mulki ke janyo matsalar, amma shigar wadannan sojoji da tsoma bakinsu wajen kawo mana sulhu na da amfani,” inji shi.
Daga: Lubabatu I. Garba, Kano da Hussaini Isah, Jos da Mohammed I. Yaba, Kaduna.