✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda ta’addanci da talauci suke dabaibayi ga mazauna iyakar Nijeriya da Nijar

In kana so ka karance bushasshiyar kasa, Nijar ce inda ya kamata mutum ya je.

A wata ziyarar da Aminiya ta kai a wasu kasuwanin kan iyakar kasashen Nijeriya da Nijar da garuruwan da suke kewaye da kasuwannin a jihohin Katsina da Jigawa da Sakkwato, ta iske wurare ne da suke cike da harkokin kasuwanci da harkokin da suke inganta tattalin arzikin kasa.

Wurare ne da suke da itatuwa da abubuwan tarihi, sannan mazauna wuraren suna samun ruwa a rijiyoyinsu wadanda suka yi bayani na kaiwa kimanin kilomita 5 daga inda ake gani.

A Illela da ke Jihar Sakkwato yanki ne da ake noman albasa wadanda rufe iyakokin kasar Nijar ya zame musu matsala saboda yadda harkoki suka tsaya cak a yankin.

Shugaban Kasuwar Maigatari Alasan Jobi, a zantawarsu da Aminiya, ya ce tattalin arzikin yankin ya samu tsaiko sakamakon rufe iyakokin kasashen biyu, wanda ya janyo tabarbarewar harkokin kasuwancin dawakai a yanzu, ba kamar yadda aka saba a baya ba.

Wanda a yau masu saye ba su wuce mutum 100, maimakon sama da mutum 300 da suke samu a kowane lokaci a baya.

Sun ce rufe iyakokin Nijeriya da Nijar da Kungiyar Raya Tattalin Arzikin Kasashen Afirka ta Yamma (ECOWAS) ta yi, ya gurgunta tattalin arziki da kara rura wutar talauci da sace-sace da yunwa, inda mutane da dama kan ci abinci sau daya kawai a rana.

Sai dai duk da rufe iyakokin, wasu suna satar hanya wajen daukar kaya da sace-sace.

Wannan ne abin da ke faruwa a Illela a Jihar Sakkwato.

A Kongolam a Jihar Katsina yara maza ’yan shekara goma sha ne suke amfani da motor kaya zuwa Damagaram kusa da Maimujiya a kasar Nijar.

Yaran sun ce suna amfani da baro su tura kaya ta barauniyar hanya zuwa Maimujiya a cikin minti 15 a kan Naira 2,500 sannan su dawo zuwa Kongolam su jira wata motar kayan.

Sani Daura direban tasi ne ya ce, akwai barauniyar hanya sama da 20 da shingen bincike daga Kongolam Maimujiya a kasar Nijar wanda masu tsaron hanyar ake ba wa dama su wuce a kasar wanda ba a san ko nawa ake ba su ba.

Masu sayar da burodi a kauyukan Daura wadanda suke dauka zuwa kasar Nijar sun ce komai ya tsaya cak, sakamakon hauhawar farashin man fetur da tsadar fulawa. Sannan rufe iyakokin Nijar sun hadu sun lalata musu harkokinsu na samu.

Rufe iyakokin Nijeriyya ya zama matsala musamman ga ’yan tasi na Kongolam da Damagaram wadanda kaso 70 matasa ne.

Muhammad Abdullahi, Sakataren Kasuwar Maigatari, ya ce, “Kafin rufe iyakokin kasashen biyu ina harkokin kudi sama da milliyan goma.

“Amma yanzu ba na iya na milliyan biyu a ranar kasuwa. Maigatari garin kasuwanci ne ba mu da komai sai lokacin noma.

“Mu ’yan uwa ne da ’yan Nijar wanda tunda aka rufe iyakokinsu aka sa su a keji.”

Ahamed Diddiri Ahamed Sarikin a ’yankin Mai’aduwa ya yi bayani game da yadda ake fataucin katako daga Nijeriya zuwa Agadez ta kasar Nijar.

Idan suka sayar da katako su ma su sayo gishiri ko wasu kayayyakin su cika mota da kaya su kawo gida su sayar.

Amma yanzu wannan kasuwanci ya tsaya wasu ma ba su yin kasuwancin baki daya. Ahmed Galadiman Daura ya ce kaso daya cikin hudu na masu zuwa kasuwar Mai’aduwa ’yan Nijar ne.

“Tunda aka rufe iyakokin kasar muka daina sayar da kaya su ma suka daina saye. Mu a wurinmu talauci shi ne babban damuwarmu.

“Kuma rufe iyakokin ya jefa da yawan mutane cikin talauci kamar masu aiki da masu fatauci da sauransu.

“Babu wanda zai iya iyakance talaucin da muke ciki a nan a yanzu saboda wannan matsala,” in ji shi.

Sani Kalmo shi ne Shugaban Kasuwar Illela ya ce kasuwar takan samar da tirela 150 wanda kowace na dauke da buhu dubu, amma yanzu ba sa wuce tirela biyar saboda ’yan Nijar ba sa zuwa.

Bello Isa Ambarura dan Majalisar Tarayya mai wakilatar Illela da Gwadabawa, ya ce mafiya yawan mutane da suke da karamin kasuwaci sun talauce.

“Mutanen da suke iya sayen buhun waken suya su sayar a kasar Nijar da yawansu ba sa iya haura kan iyaka,” in ji shi.

Ya ce shi ma kasuwancin da ake yi a cikin gida ya samu tangarda.

Ya ce, “A Illela mutane na iya sayen buhunan hatsi su lai Konni su kuma sayar da su.

“Mata da ke sayar da atamfofi su ma suna daukowa daga Sakkwato su kai Konni su sayar.

“Mutane da yawa a Karamar Hukumar Illela suna wannan kasuwanci, amma yanzu an samu tsaiko, harkoki sun tsaya.”

Yusha’u Mai’aduwa shi ne Shugaban ’Yan Kasuwar Mai’aduwa reshen masu sayar da dabbobi, ya bayyana halin da kasuwar take ciki game da fataucin rakuma daga nisan wuri kamar Legas sakamakon canjin rayuwa da hauhawar farashi rakuma.

Ya ce idan ka sayi rakumi kamar a Naira dubu 100, yanzu za ka iyar sayar da shi 250,000 sakamakon canjin kudin kasar Nijar. Shugaban ’Yan Kasuwar ’Yan Doki a Garki, ya ce “Doki yana da matukar tsada sosai, don haka ba kowa yake saya ba.

“Kafin kulle iyakar muna sayar da babban doki kimanin Naira dubu 70 zuwa dubu 500.

“Ko a makonnin da suka gabata wani ya sa kudin wani karamin doki a kan Naira dubu 700 amma masu saye ba su yarda ba.”

Mata biyu da yara 11

“Ba na zuwa Nijar ’yan kwanakin nan saboda rashin kudi. Ban je Nijar ba kusan wata goma ke nan yanzu.

“Babu abin da nake yi in ba zaman fada ba a matsayina na dagaci.

“Ba zan iya dogara kadai da abin da nake samu ba a nan.  Ina da ’ya’ya 11 da mata biyu. Rayuwar ta yi wahala.”

Mutane da yawa sun fada talauci, daya daga cikinsu ya ce, “Akwai yawan jama’a a yanzu fiye da a da.

“Akwai mutane da yawa a wannan yanki nawa da ba sa iya zuwa Nijar. Ba su da natsuwa. Yanzu Naira 2,500 ne ake canza CFA daya.

“Idan kana son zuwa Damagram daga nan za ka biya CFA shida ne. Kusan Naira 12,000 ke nan daga nan zuwa Damagaram.

“A da idan ka biya 1,000 zuwa 2,000 zai ishe ka daga Daura zuwa Damagaram, amma a yanzu Naira 12,000 ne zai kai ka daga Daura zuwa Damagaram. Babu kudi a yanzu saboda babu kasuwanci sosai,” in ji shi.

Mu ’yan uwa ne

 “Lokacin da Turawa suka zo ne suka raba mu, amma dukkanmu daya ne. Akwai auratayya a tsakaninmu ’yan uwan juna ne mu.

“Lokacin da Turawa suka zo sai suka kafa Daular Faransa da ta Birtaniya.

“Duk muna a karkashin masarauta iri daya ne. Mutanen Nijar na sa Sarkinsu mu ma muna da namu Sarkin. Muna kuma auratayya a tsakaninmu.

“Harshenmu daya kuma addininmu daya,” in ji Abubakar Magaji masanin tarihi a Masarautar Daura.

Motocin da aka kwace

Galadiman Daura ya ce jami’an hana fasa-kwauri sun kwace manyan motoci a kan hanyarsu ta zuwa Mai’aduwa.

“Saboda rufe iyaka da aka yi wanda ya janyo karancin abinci, duk wata mota da ke kan hanyarta ta zuwa Mai’aduwa sai a kama ta.

“A lokacin ziyarar Shugaban Hukumar Kwastam yankin, mun fada masa hakan, yanzu an yarda cewa wadannan kayayyakin hatsi da aka kama za a sake su ga masu su da yarjejeniyar cewa a Nijeriya za su sayar da kayan ba a kasar Nijar ba.

“Abin da ake bukata a tsakaninmu da karamar hukumar shi ne tireloli 19 na masara a duk mako.

“Duk tirela da ta ta zo wucewa sai ka ji suna cewa Nijar za ta je. Abin da ke faruwa ke nan.

“Ya yi karin bayani a kan matsalar, a lokacin da Shugaban Kwastam ya zo sulhu a kan cewa tireloli ba za su je Mai’aduwa ba a lokacin.

“Sai dai su tsaya a Daura, wanda yake kilomita 25 daga nan sai a yi amfani da kananan motoci don kwaso kayan.

“Hakan ya sa kudin da muke kashewa ya karu. Yanzu idan kana da tirela ta tsaya a Daura sai an sauke kayan an samu karamar mota sai kuma a sake sawa ta kai ta dawo.

“Yanzu idan ka kawo tirela 100 na masara a Mai’aduwa za ka sauke su sai a sa su a kananan motoci don su shiga da su.

“Mece ce hikimar da ke tattare da wannan abin?”

“Yana na sa mu kashe ninkin abin da muke kashewa a baya. Bayan haka hanyar Daura zuwa Mai’aduwa na da tsawo. Akwai wuraren jami’an tsaro masu yawa.

“Nisan kusan kilomita 20 ne kawai amma shingayen jami’an tsaro daban-daban har guda 20,” in ji shi.

‘Muna kai masara kasuwanni daban-daban’

Ya yi bayani dangatanka ta musamman tsakanin kasuwannin da ke hade da sauran kasuwannin.

A cewarsa, “Kasuwanci ne ke sa ci gaban wasu kasuwanci, misali duk masarar da za ta shigo nan, ban da wadda za mu yi amfani da ita, akwai kasuwa daya da muke kaiwa, ita ce, Kasuwar Maigatari a Jihar Jigawa. Akwai kasuwa a Babura.

“Akwai kasuwa a Garki a Jihar Katsina; har da Kasuwar Zango. Duk muna kai masara. Ninki biyu A da kafin mulkin Turawa Nijeriya da Nijar kasa daya ce.

“Idan aka hada masu jin Hausa ’yan Nijar da Nijeriya, Nijeriya za ta kara girma har ma ta kai iyakar Benin da Burkina Faso.

“Wannan na nufin Nijeriya za ta ninka girmanta sau biyu.

“Kasar Nijar tana da girma da fadin kasa. Idan aka raba Nijar zuwa kashi biyu a ba Nijeriya kashi daya, za ka samu kusan daidai girman Nijeriya,” in ji Farfesa Attahiru Sifawa, Malamin Tarihi a Jami’ar Sakkwato.

Dangote

Mairago Bashir Mashi wanda aka fi sani da Dangote Mairago yana kasuwanci raguna da awaki a Kasuwar Mai’aduwa.

Ya ce: “Ragon da ake sayar da shi a kan Naira 70,000 a baya, yanzu yana kai Naira 120,000.

Jar akuya kuwa ana sayarwa a kan Naira 20,000, awakin yankin sahara da suke daga Nijar, ya danganta da lafiyarsu idan har kuma suna da kiba sosai kudinsu yana farawa ne daga Naira 25,000 ko Naira 30,000.’’

Ta yaya za a rayu?

“Mutane suna mutuwa, wasu kuma na fama da yunwa. Idan lebura ya yi aiki na rana daya ya samu Naira 1,500, mudun masara na kai Naira 1,600 yanzu, muna biyansa Naira 1,500, to, ta yaya zai rayu?

Wasu mutane suna cin abinci sau daya a rana. Wasu ma ba sa cin komai. Ko’ina ka je za ka rika ganin maroka. Babu matsuguni kuma babu inda za su je,’’ in ji Habu Daura da yake bayyana irin tabarbarewar tattallin arzikin yankin.

Daga Damagaram zuwa Garki

Ado Magariya, ya ce, “Shekara 40 ke nan ina sayar da rakuma. Ina kawo rakuma daga Magariya da ke Damagaram.

“Na fito ne daga Magariya daga Magariya ina kai rakuma zuwa Dingass, Damagaram da wasu wuraren. Ina kawo rakuma daga dukkan wuraren nan zuwa Garki.

“Akwai rakuma da yawa a nan amma dalilin rufe iyaka ne ya sa yanzu babu su.”

Kaso 60 na burodi Salisu Daura, Shugaban Matasan Masarautar Daura ya yi bayanin gidajen burodi a Daura da Nijar: “Kusan kaso 60 na burodin da ake yi a Daura, Mashi da Dutsi ana kai shi Nijar ne.

“Kuma muna kai kayan abinci zuwa Nijar kuma mu ma muna sayo wasu kayan abincin daga can. Wasu suna daukar masara, gero, shinkafar gida da kwakumba,” in ji shi.

Ya ce duk da haka kasuwancin burodi da Nijar ya ja baya. Naira miliyan 2 ake sayen doki Yanzu doki ana sayar da shi Naira miliyan 2 a Daura: “Muna zuwa Nijar ne don mu sayo shanu, tumaki da dawakai.

“A da doki daya ana sayar da shi a kan Naira 300,000, amma yanzu zai yi wahala ka samu matashin doki a kan Naira 800,000.

“Za ka iya samun dokin Naira 500,000 amma wanda ya haura shekara 10. Mu kuma ba ma son tsohon doki saboda mu ’yan kasuwa ne.

“Yanzu za ka samu dokin da ya kai kusan Naira miliyan 2. Saboda yanayin tattalin arzakin Nijeriya.’’

Matasa 8,000 marasa aikin yi

Ana maganar rashin aikin yi a Daura sosai: “Muna da kusan matasa 10,000 a kananan hukumomi 5 wadanda suke kasuwanci a tsakanin Nijeriya da Nijar.

“Kusan kaso 70 na matasan ba za su iya ci gaba da yin kasuwancin ba. Amma yanzu mutum 2,000 ne kawai suke iya yin kasuwanci a Nijar.’’

Ribar Naira 20,000 kawai

Bashir Galadima ya fito ne daga Nijar kuma ya ce ribar ba ya fita: “Ina sayar da dawakai kuma ina kawo su daga Nijar zuwa Nijeriya. Ina kawo dawakai 10 zuwa 15 daga Nijar, amma yanzu ina iya kawo guda biyar ne kacal.

“Ba na samun kudi sosai a kasuwanci. Ribana tana kaiwa Naira 100,000 a da, amma yanzu ba ta wuce Naira 20,000. Ina kawo dawakai daga Damagaram. ina tafiyar kusan kilomita 300 wato tafiyar kwana hudu ne’.’

Shanu 1,000

Lokacin da aka rufe iyakar Nijeriya da Nijar, mutane da yawa daga Nijar sun daina zuwa kasuwa.

Kafin a kulle iyakar shanu 3,000 ake kawowa daga Nijar zuwa Illela duk ranar kasuwa.

Da aka kulle iyakar shanu 1,000 ake kawowa Illela, ga rashin kudi a hannun mutane.

Rashin tsaro

Lawan Ibrahim, Sarkin Zangon Illela, ya yi korafi a kan rashin tsaro, duk da iyakar a bude take.

“Wata sabuwar matsalar kuma ita ce rashin tsaro, saboda duk inda ’yan ta’adda suka ga rakuma sai su kai hari.

“’Yan ta’adda sun kwace rakuman wasu daga cikin mutanena, kusan rakuma 100. Wannan abin ya faru ne mako biyu da suka wuce kusa da Gaba.

“Wannan ne karo na 3 a wannan shekarar. Idan aka hada jimilla, kusan rakuma 460 aka sace wa mutanena a kan hanyarsu daga Nijar zuwa Illela.

Sace-sacen rakuma daga ’yan bindiga

Muhammad Hassan dan Ruwawuri ne a Karamar Hukumar Tangaza a Jihar Sakkwato. A wurare hudu aka gano rakumansa.

Ya ce, “Harin farko da aka kawo a kan hanyar Gada ne. Sun kwace rakuma 19 a lokacin da muke tahowa daga Illela.

“Kusan wata shida ke nan a lokacin iyaka a kulle take. Na biyun kuma a nan hanyar Gada ce a lokacin ma iyakar na kulle.

“Kuma suka sace mana rakuma 17. Farmaki na uku kuma na dawo daga Dogon Dutsi a Nijar, kusa da Ruwawuri suka sace min rakuma 8.

“Farmaki na hudu ya faru ne bayan na sayar da rakumana suka farmake ni suka amshe kudin.

Farmakin masu kasuwanci kayan hatsi

Kalmalo ya ce ana kai farmaki ga masu kasuwanci kayan hatsi a duk lokacin da suka debo kayan hatsi zuwa Nijar.

Ya ce: “Kawai suna kashe mutane ne ba sa daukar wani kayan hatsi.

’Yan kasuwa 8 aka kashe a shekara uku da suka wuce.’

Farin cikin ’yan kasuwa Danladi, Sarkin Shanun Illela ya ba da shawara a kan a bude iyakar da aka yi: “Mutanen Illela da wadanda suke kasuwar suna murnar bude iyakar kasa da aka yi. Mutane suna kawo shanu yanzu.

A lokacin da iyakokin kasashen ke kulle, mutane da yawa daga Nijar ba sa iya zuwa.’’

Nijar kamar gidana ne

Farfesa Yusuf Adam ya yi magana a kan illar kulle iyakar kasa da yadda ya shafi ba da tallafin karatu a Jami’ar Bayero da ke Kano (BUK).

Ya ce dalibai suna ziyartar Nijar duk shekara don karo ilimi.

A cewarsa: “In kana so ka karance bushasshiyar kasa, Nijar ce inda ya kamata mutum ya je.

“Dalibai suna daukar rahoto a kan yanayin zaizaiyar wannan kasa da kuma yanayin garin ga ’yan Adam da yanayin kasuwancinsu.

“Da muna cikin wani yanayi amma yanzu da aka janye takunkumin muna fata a wannan shekara mu sake komawa Nijar.”