✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda Aka Kashe Mayakan ISWAP 11 A Dajin Sambisa

Dakarun sojin Najeriya da ke sintiri na musamman a Dajin Sambisa a Jihar Borno sun yi nasarar kashe ’yan ta'addar kungiyar ISWAP  11.

Dakarun sojin Najeriya da ke sintiri na musamman a Dajin Sambisa a Jihar Borno sun yi nasarar kashe ’yan ta’addar kungiyar ISWAP  11.

A cikin wata sanarwa da rundunar sojin ta fitar ta ce an gudanar da wani samame ne da wata runduna ta hadin gwiwa tare da kai hari kan ’yan ta’addan a kauyen Jongo.

Rahoton na nuna cewar, sojojin sun yi artabu da ’yan ta’addan, inda suka yi raga-raga da mayakan ISWAP 11, yayin da sauran suka ranta a na kare tare da munanan raunuka.

Bayan arangamar sojojin sun gudanar da bincike a yankin, inda suka kwato makamai masu yawan gaske.

Sanarwar na cewar, cikin makaman da aka kwato sun hada da harsashi 99 da  alburusai nau’in 7.62 x 54mm,  39mm, da sundukan harsasan bindigar AK-47 guda uku, gurneti biyu, da kuma bindigogin gida guda biyu.

Cigaba da Kakkabe ‘yan ta’addar ISWAP tare da kwace makamansu na taimakawa  matuka wajen inganta tsaro da zaman lafiya a yankin na Arewa maso Gabas.