Dakarun sojin Najeriya da ke sintiri na musamman a Dajin Sambisa a Jihar Borno sun yi nasarar kashe ’yan ta’addar kungiyar ISWAP 11.
A cikin wata sanarwa da rundunar sojin ta fitar ta ce an gudanar da wani samame ne da wata runduna ta hadin gwiwa tare da kai hari kan ’yan ta’addan a kauyen Jongo.
Rahoton na nuna cewar, sojojin sun yi artabu da ’yan ta’addan, inda suka yi raga-raga da mayakan ISWAP 11, yayin da sauran suka ranta a na kare tare da munanan raunuka.
Bayan arangamar sojojin sun gudanar da bincike a yankin, inda suka kwato makamai masu yawan gaske.
Sanarwar na cewar, cikin makaman da aka kwato sun hada da harsashi 99 da alburusai nau’in 7.62 x 54mm, 39mm, da sundukan harsasan bindigar AK-47 guda uku, gurneti biyu, da kuma bindigogin gida guda biyu.
Cigaba da Kakkabe ‘yan ta’addar ISWAP tare da kwace makamansu na taimakawa matuka wajen inganta tsaro da zaman lafiya a yankin na Arewa maso Gabas.