✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sojoji sun kashe kwamandojin ISWAP 10

Sojoji sun kashe mayaka akalla 100, sun lalata masana'antar makamai, sun kwashe kifi buhu 457 na ISWAP

Sojoji sun lalata masana’antar makaman kungiyar ISWAP tare da kashe mayakanta akalla 100, ciki har manyan kwamandojinta a tsakiyar watan Ramadan din da muke ciki.

Manyan kwamandojojin kungiyar 10 tare da sauran mayakan sun sheka lahira ne bayan dakarun Rundunar Hadin Gwiwar Kasashen Tafkin Chadi (MNJTF) sun yi musu dirar mikiya sun yi raga-raga da masana’antar makaman da ke Arina Woje, a yankin Tafkin Chadi.

Kakakin rundunar MNJTF, Kanar Muhammad Dole ya bayyana cewa, “Kwamandojin kungiyar da sojoji suka kashe sun hada da Abubakar Dan Buduma, Abubakar Shuwa, Abu Ali da Abu Jubrilla da sauransu.

“An kwace muggan makamai, har da makaman atilare, kayan hada abubuwan fashewa, kwalekwale da sauran ababen hawa da sauransu a hannunsu.”

Sanarwar da ya fitar a ranar Lahadi ta ce sojojin sun yi wa mafakar mayakan na ISWAP da ke Zanari da Fedondiya da sauran wurare raga-raga ne ta hanyar amfani da jiragen yaki da kuma dakarun sojin kasa.

“An yi nasara kubutar da mutane da dama daga hannunsu, ciki har da mata da kananan yara da suka yi garkuwa da su.

“Sauran abubuwan da aka kwace sun hada buhunan hatsi masu tarin yawa, man fetur, miyagun kwayoyi, kakin soji da sauran abubuwa, kuma an lalata su,” inji Kanar Dole.

Ya ce a samamen da sojojin suka kai kan mafakar mayakan na ISWAP a cikin watan Ramadan, a yankin Kimeguna, ta bangaren Jamhuriyar Nijyar, sun kama wasu masu yi wa kungiyar safarar kifi dauke da buhuna 457 na kifi kuma ana bincikar su.

Ya kara da cewa sun kama buhunan masara da na wake da injinuna nika da kuma babura da lalatattun motocin sojoji da kungiyar take basaja da su a maboyarta da ke Fedondiya.

Ya bayyana cewa dakaraun Najeriya, Jamhuriyar Nijar da Chaci, da kuma ’yan sa-kai na Civilian JTF sun shafe tsawon mako guda a cikin watan azumin Ramadan suna luguden wuta a maboyar mayakan kungiyar ta’addancin da ke yankin.

A cewarsa, sun gano yadda kungiyar ta ISWAP ta koma amfani da motoci makare da abubuwan fashe ko dasa su, wadanda a baya-bayan nan suka yi sanadiyyar raunata sojoji 18, baya ga wasu soja uku da dan Civilian JTF daya suka rasa ransu.