Wani sojan Najeriya ya bude wa abokan aikinsa wuta, ya kashe soja daya da wani ma’aikacin jinkai a wani sansanin sojoji da ke yankin Damboa, Jihar Borno.
Sojan ya kuma harbi wani matukin jirgin agaji na Majalisar Dinkin Duniya, lamarin da ya sa ta bukaci a gudanar da cikakken bincike a kan abin da ya faru.
- NAJERIYA A YAU: Yadda Dan Chana Ya ce Ya Kashewa Ummita Miliyan N120
- Sojoji sun kashe jagororin IPOB 13
Mataimakin Daraktan Yada Labarai na Rundunar sojin Kasa ta Najeriya, Manjo Samson Zakhom, ya ce, “Sojoji ba su ba ta lokaci ba wajen bindige sojan da ya bude wuta, domin su takaita yawan asar rayuka da zai iya jawowa.
“Amma matukin jirgin ya farfado, yana samu sauki, gawarwakin kuma an kai su Asibitin Sojoji na Runduna ta 7.
“An far gudanar da bincike kan lamarin sannan an dauki matakan dakile faruwar irin haka a nan gaba,” in ji jami’in.
MDD ta yi tir da harin Borno
Babban Jami’in Jinkai na Majalisar Dinkin Duniya a Najeriya, ya yi Allah wadai da abin da sojan ya aikata.
Jami’in ya yi ta’aziyya ga iyalan wadanda suka rasu a harin na Borno, yana mai jaddada bukatar bayar da goyon baya ga ma’aikatan agaji.
Ya kuna yaba wa hukumomin sojin Najeriya bisa matakan gaggawa da suka dauka kan lamarin gami da na binciken da suka fara domin hana maimatuwar hakan a nan gaba.
Wannan na zuwa ne washegarin da wani soja da ya yi tatul da giya ya kade wani mai mukamin Birgediya-Janar da mota ya kashe shi a cikin bariki.
Tuni dai aka tsare Kofur din sojan da ya yi ajalin Janar din domin ya fuskanci shari’a.