More Podcasts
Akwai cututtuka da dama da ke yaɗuwa, kuma mafi yawan mutane da ke ɗauke da su, ba su san suna da su ba.
Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce zaman lafiya, samun abinci da wadata, da rashin damuwa a ƙwaƙwalwa na daga cikin abubuwan da ke tabbatar da lafiyar mutum.
- NAJERIYA A YAU: Hanyoyin Komawa Cin Abinci Yadda Ya Kamata Bayan Watan Ramadana
- NAJERIYA A YAU: Dalilan Da Ke Hana Wasu Teloli Cika Alƙawari
Ɗaya daga cikin manyan cututtukan da ke damun mutane da yawa, ita ce cutar hawan jini. Wannan cuta na kashe aƙalla mutane miliyan biyu a duk shekara a Najeriya.
Shirin Najeriya A Yau na wannan rana zai yi bayani ne kan cutar hawan jini da kuma hanyoyin da za a bi don magance ta.
Domin sauke shirin, latsa: nanhttps://www.buzzsprout.com/1822045/episodes/16913858-dalilan-kamuwa-da-cutar-hawan-jini-da-hanyoyin-magance-ta.mp3?download=true