Wani matashi dan shekarar 20 ya fada hannun hukuma kan zargin kashe mahaifinsa da adda a Jihar Jigawa.
Rundunar ’yan sandan Jihar Jigawa ta kama wanda ake zargin kashe mahaifinsa mai shekara 57, da adda.
Wanda aka kashe ya samu raunuka a kafadarsa da wuya da kirjinsa, kuma an kai shi Babban Asibitin Tarayya (FMC) da ke Birnin Kudu, inda aka tabbatar da mutuwarsa.
Rahotanni sun ce lamarin ya faru ne a ranar Litinin 5 ga Mayu, 2025, da misalin ƙarfe 10:00 na safe a unguwar Bakin Kasuwa, da ke Karamar hukumar Gwaram.
- Wata mata ta auri maza biyu a lokaci guda a Kano
- ’Yan PDP 6 a Majalisar Tarayya sun koma APC
- Daukar nauyin dalibai: Rikici ya barke a Hukumar Raya Arewa Maso Yamma
Kwamishinan ’yan sandan Jihar Jigawa, AT Abdullahi, ya ba da umarnin cewa Sashen Binciken Manyan Laifuka na Jihar (SCID) da ke Dutse su karɓi ke cin domin don gudanar da bincike mai zurfi, wanda bayan nan za a gurfanar da wanda ake zargin a gaban kotu domin ya girbi abin da ya shuga.
Kakakin rundunar, SP Lawan Shiisu Adam, ya tabbatar da kama wanda ake zargin tare da ba da tabbacin cewa za a yi adalci kuma za a bayar da ƙarin bayani a nan gaba.