Shugabannin wasu kasashen duniya tuni sun aike da sakon taya murna ga zababben Shugaban Amurka, Joe Biden, biyo bayan nasarar da da ya samu a zaben da aka gudanar a ranar 2 ga watan Nuwamba.
A watan Janairun 2021 ne za a rantsar Joseph Robinette Biden Jr. a matsayin Shugaban Amurka na 46 bayan ya kayar da Shugaba Donald Trump mai rike da mulkin kasar.
Biden ya lashe zaben shugaban Amurka
An cafke jagoran ‘yan adawar Ivory Coast
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya taya zababben Shugaban murna lashe zaben tare da neman ya kara inganta dangartakar Amura da sauran kasashen nahiyyar Afrika.
Firaiministan Ireland Michael Martin, bayan taya murna da fatan yin aiki tare da zababben shugaban, ya kuma nuna akwai dadaddiyar abota a tsakaninsu.
Justin Trudeau wanda shi ne Firaiministan Canada, ya taya zababben shugaban murna da mataimakiyarsa , Sanata Kamal Harris, inda shi ma ya yi fatan yin alaka tare da gwamnatinsu wajen shawo kalubalen da suka addabi duniya baki daya.
Ita kuwa gwamnatin Jamus ta cewa ta yi nasarar Joe Biden za ta kafa tubalin dangartaka mai karfi tsakanin Amurka da kasashen da ke tsallaken Kogin Atlantic.
Firaiministan Scotland Nicola Sturgeon, ita ma ta shiga sahun shugabannin duniya da suka aike da sakon taya murna ga zababben shugaban na Amurka da kuma mataimakiyarsa Kamala Harris.
Keir Starmer, shugaban Jam’iyyar Labour a Birtaniya, ya ce nasarar Joe Biden za ta tabbatar da cikar muradinsu na samuwar hadin kai a maimakon rashin gaskiya da rarrabuwar kawuna.
Kazalika, Firaiministan Birtaniya Mista Borris Johnson wanda ya kasance aminin Donald Trump, ya aike wa da Joe Biden sakon taya murna, haka kuma shi ma Shugaban Faransa, Emmanuel Macron ya bi sahu.