Fadar shugaban kasa a jiya da dare ta fitar da wata sanarwa da ta kira rahoton gaskiya wanda ya bayyana yadda ake zargin daraktoci bakwai da ta dakatar na hukumar bayar da agajin gaggawa ta NEMA da sace fiye da Naira biliyan daya.
Sanarwar da fadar shugaban kasar ta fitar ya ce rahoton ya nuna yadda tsohon daraktan hukumar Mohammed Sani Sidi ya rika yin amfani da asusun ajiya 20 a bankuna daban-daban na kasar duk da matsayin da yake rikewa na ma’aikacin gwamnati.
Wani jami’i a fadar shugaban kasar sun yi zargin cewa daraktan da ta dakatar ya yi gaggawar kai lamarin gaban majalisar tarayya don ya kawo cikas ga binciken da Hukumar Yaki da Ta’annutin Kudi ta EFCC kan lamarin.
Ya ce rahoto na musamman da hukumar da ke binciken lamarin ta aikewa fadar shugaban kasar ya nuna cewa tsohon daraktan wanda aka dakatar ya ci amanar ofishinsa da karfar cin hanci da kuma saba doka.