✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda shigar Osinbajo masallaci ta haifar da takaddama a Kano

Babu laifin da Osinbajo ya aikata don ya shiga masallaci ba tare da ya kwabe takalmansa ba.

Mabiya a zaurukan sada zumunta da sauran al’ummomi na ci gaba da bayyana ra’ayoyi mabanbanta kan yadda Mataimakin Shugaban Kasa, Farfesa Yemi Osinbajo ya shiga masallaci da takalmi a Jihar Kano.

Aminiya ta ruwaito cewa, a ranar Talata ce mataimakin shugaban kasar ya ziyarci Jihar Kano domin halartar taron tunawa da Sardaunan Sokoto, marigayi Sa Ahmadu Bello sannan kuma da ta’aziyyar wadanda manyan mutane da rasuwar ta girgiza jihar da ma Najeriya baki daya.

A wani hoto da tuni ya karade dandalan sada zumunta, ya nuna mataimakin shugaban a masallacin Darul Hadith da ke Unguwar Tudun Yola sanye da takalminsa a kan kujera, a lokacin da ya ke ta’aziyyar marigayi Dokta Ahmad Ibrahim BUK da ya rasu makonni biyu da suka gabata.

Wannan hoto dai ya fusata wadansu bisa la’akari da mizani na mahangar da suka dora lamarin a kai, a yayin da wasu ke yin tofin Allah-tsine a kan mataimakin shugaban kasar, wasunsu kuma na kare shi suke yi da cewar hakan bai ci karo da addini ba gami da wadansu dalilai da suka rika wassafawa.

Wasu masu yin tofin Allah-tsinen sun rataya laifin ne a kan gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje da Ministan Sadarwa, Sheikh Isa Ali Pantami, wanda a cewarsu sun gaza ankarar da mataimakin shugaban kasar kan shiga masallaci da takalmi kuskure ne.

Cikin wani sako da wani mabiyin shafin Facebook mai Yasir Ramadan Gwale ya wallafa, “Obama ma da zai shiga Masallaci sai da ya cire takalmi, watakila saboda ya girmama Musulmin da suke Sallah a ciki saboda ya san suna cirewa in za su shiga.

“Amma shi Osinbajo ba wanda ya iya ce masa ya tube takalmi, Musulmi basa Sallah da takalmi akan dadduma.

“Gaskiya cin fuska ne ana kallonsa da takalmi amma ba wanda ya nuna masa ya cire alhali duk ’yan tawagar kowa ya cire nasa da zai shiga.

“Ya kamata a ce Mataimakin Shugaban kasa ya zama very diplomatic (jakada na kwarai) a lokacin da yake neman Musulmi su yarda da shi saboda yana da bukata a 2023” a cewar Yasir Ramadan Gwale.

Shi kuwa Bashir Muhammad cewa ya yi shiga Masallaci da takalmi mai tsafta ba laifi bane.

“Hakika hotunan da ake ta yadawa, ba ‘wai’ tayar da hankali suke yi na sosai ba – saboda ba a kan Osinbajo aka fara ganin haka ba.

“To amma, hakan ba ya nufin cewa duk lokacin da wani ya aikata haka, ba za a kalle shi a matsayin wanda bai aikata wani na ba-wai ba.

“Ko da shiga cikin Masallaci da takalmi (idan musamman ana da yakinin cewa yana da tsarki) ba laifi ko matsala ba ne.

“Yana da kyau a ce su Ganduje da Pantami, sun fada masa cewa “ranka ya dade, ana dan cire takalmi idan za a shiga.”

“Wannan kuwa, saboda martaba Masallatan da muke dasu; da kuma kyakkyawar tarbiyyar da muke ita, ta tsaftace wuraren bautar mu” a cewar Muhammad Bashir.

Shi ma wani mabiyin shafin Facebook mai suna Ibrahim El-Caleel ya bayyana ra’ayinsa, inda ya bai wa mataimakin shugaban kasar uzurin cewa na kusa da shi ne ba su fada masa abin da ya dace ba.

“Wannan kuma ra’ayi na ne. Tabbas zan mishi uzuri, kuma ina da dalilai na!

“Musulmai sukan yi nauyin baki wajen fadawa wadanda ba musulmai ba cewa abu kaza ba daidai bane. Da an ce da Osinbajo ya cire takalmin shi, zai cire dole. Tun da shine yake son yin ta’aziyya.”

“Idan ma yace ya fasa zai juya, to ai babu wani abu da aka rasa. Yo dama ya taba zuwa masallacin ne jin wa’’azin Malamin don ya amfana? Ai wannan shi ne yafi amfani fiye da ta’aziyyar ma.

“Amma a nan ni ban ga laifin Osibanjo ba. Don kuwa ba dole bane ya hararo cewa abin da ya yi bai kyauta ba. A matsayin shi na dan siyasan dimokuradiyya, ba na tunanin da gangan zai yi wannan aikin da ya yi don cin fuska.

“Shi abinda ya kai shi wajen nan ba wai don ya samu lada bane a wajen Allah, ladan ta’aziyya. A’a. Ladan siyasa ne yaje nema. Kuma duk wanda zai je neman ladan siyasa, babu yadda za’a yi da gangan ya yi cin fuska ga mutanen da yaje neman ‘attention’ goyon bayansu.

“Abin da ya fi shi ne nan gaba a daure a gaya mishi ya cire takalmi kawai. Duk wannan “condemnation” (tir da Allah-wadai) ba shine abin yi ba.

“Musulmai kawai su dage ne wajen gaya wa kowa limits iyakarsa na addininsu. A daina wani jin nauyi ko kunya. Idan suka yi nauyin baki suna tunanin wai wanda ba musulmi bai san “ya kamata” to idan fa yazo ya yi rashin kirki, laifin ba nashi ba ne.

“Nima yanzu idan na je shiga coci (Allah Ya tsare ni) da kaftan dina da hula bangwal tangaran, ba dole ba ne in tuna cewa wai ana cire hula. Dole sai in sun tuna mini, sannan sai in cire. Tunda ni wajen ibada na da hula nake shiga.

“Shi iya abin da ya sani shi ne, ya zo yayi ta’aziyya. Maganar takalmi ba lallai ba ne ma ya ji. Don ba dole ba ne ma wani ya fada masa ko daga baya. Allah Ya sa mu dace,” a cewar El-Caleel

Haka kuma wani fitacce da ya saba yin sharhi kan abubuwan da suka shafi al’amura na yau da kullum a kan shafinsa na Twitter mai suna Gimba Kakanda, cewa ya yi “babu laifin da Osinbajo ya aikata don ya shiga masallaci ba tare da ya kwabe takalmansa ba.

“Ana iya shiga masallaci da takalmi matukar an tabbatar da tsaftarsa da tsarkinsa, saboda haka duk wannan tayar da jijiyar wuya da ake yi ba shi da manufa.

“Sai dai a mahanga ta siyasa, cire takalmansa ya kamata ya yi a shawarce, wanda hakan zai nuna yana la’akari da alada kuma zai nuna cewa shi mutum ne mai tawali’u,” a cewar Gimba.