Rundunar tsaro ta NSCDC ta kori jami’in ta da ta kama da hannu dumu-dumu wajen satar kayan tallafin annobar COVID-19.
Rundunar ta dauki matakin korar jami’in nata mai suna Iliya Ibrahim bayan da faifan bidiyonsa ya karade kafafan sada zumunta, inda aka nuno sa sanye da kayan sarki cikin masu satar kayan abincin yana rike da nasa kayan da ya dauko a wani runbun adana kayan abinci da ke yankin Gwagwalada a Babban Birnin Tarayya Abuja.
Sanarwar korar na kunshe ne a wata takardar da mai taimakawa Babban Kwamandan Rundunar ta fuskar Watsa Labarai, Ekunola Gbenga ya fitar a ranar Talata a Abuja.
Sanarwar tace babban kwamandan rundunar Abdullahi Gana Muhammadu ya amince da bukatar da kwamitin ladabtarwa na kananan ma’aikata ya nema na a kori Iliya Ibrahim da ke aiki da ofishin hukumar na Gwagwalada bisa samun sa da aka yi da hannu a satar.
An nemi korarsa ne bayan an tuhume shi da saba dokar aiki laifin da ake samun kaso mai yawa na ma’aikata da shi, inda aka yanke hukuncin korarsa daga aiki bayan da kwamitin ladabtarwar ya zurfafa bincike.
Babban kwamandan rundunar ya yaba wa manbobin kwamitin ladabtarwar da ma daukacin mutanen da suka taimaka wajen samar da bayanan da suka taimaka wajen gano jami’in.
Ya kuma ce akwai bukatar jama’a su cigaba da bada bayanai domin fitar da baragurbi daga cikin jami’an rundunar.