Aminiya ta tattauna da Sarkin Kugen Sarkin Zazzau Malam Suleiman Abubakar domin jin yadda buga Kuge ya samo asali da inda sarautarsa ta samo asali a kasar Hausa da amfani da kuma gudunmawar da Kuge ke bayarwa a masarautu.
Sunana Suleiman Abubakar Sarkin Kugen Sarkin Zazzau kuma na gaji kakana ne, kuma duk da ina da ’yan uwa da yayyi amma sai ni jikan gidan Allah Ya ba ni wannan sarauta. Na taso na ga kakana ne Sarkin Kugen Sarkin Zazzau, to sai na ga sunan gidanmu ke nan domin duk wanda ya zo Kofar Kona za a ce ga gidan Sarkin Kugen Sarkin Zazzau, to amma sai na ga sunan da sarautar suna neman fita gidanmu don haka sai na ce, bari ni in dauka in kara farfado da ita. To kuma cikin ikon Allah da na fara sai ina bin duk inda ya bi har Allah Ya sa yau na gaje shi a sarautar buga Kugen Sarkin Zazzau.
Ina makaranta sai aka kawo mun takarda cewa Mai martaba Sarkin Zazzau ya nada ni sarautar gidanmu ta Sarkin Kugen Sarkin Zazzau, kuma a ranar Juma’a 23 ga Afrilun 1997 ne na gaji kakana. Sarkin Zazzau ya nada ni na zama Sarkin Kugen Sarki, kamar yadda aka sanar da ni shi ne da ma asalinmu daga gidan Sarautar Kano muka fito domin a can ne asalinmu yake. To sai shi kakan namu ya nemi izinin Sarkin Kano Alhaji Ado Bayaro cewa, shi yana so ya koma garin Zariya da zaman Sarkin sai ya yi masa izini ya yarda ya koma, don haka sai ya dawo garin Zariya a zamanin marigayi Sarkin Zazzau Aminu to tun daga wancan lokaci ne gidanmu yake rike da wannan sarauta domin dama buga Kugen ba wai ana yin sa don dadi ne ba a’a shi Kuge ana buga shi ne domin shelantar da wani abu da yake faruwa ga al’umma ko kuma idan Sarki zai kai rangadi wanda a da can ake yi.
Shi dai Kuge kamar yadda sauran sarautu ke da nasu irin nau’o’in mu namu wanda muke bugawa ba wai karfe ba ne a’a wanda na gada a gidanmu tsantsan azurfa ne wanda muke bugawa kuma kamar yadda ka sani ko kake ji, shi kuge idan ana buga shi kuma iska na tashi to za ka iya jin sa a nisan kilomita kamar biyar daga inda kake saboda kararsa domin yana da amo sosai.
Kuge ya samo asali ne tun zamanin ana yaki kuma dama don yaki ake amfani da shi idan Sarki ya yi dammara za a je yaki to sai a buga kuge, to, duk wanda ya ji ana buga kuge to akwai wani babban al’amari da yake faruwa. Sai dai yanzu da ba yaki kuma duk wata hanyar da za ka sanar da jama’ar duniya tana da yawa don haka aka daina amfani da shi sai wajen al’adun gargajiya. Amma duk daren Alhamis in dai Mai martaba Sarki yana gari, to sai na je gidan na buga kuge har na tsawon wani lokaci kafin in yi sallama in dawo gida, kuma ina gamawa za ka ga Mai martaba Sarki ya aiko min da sako, kuma sako babba domin yin hidimar iyali.
Kuge da kake gani ba a buga shi a ko’ina sai dai gidan Sarki domin ba don dadi ake buga kuge ba, kamar yadda na shaida maka a baya an fi amfani da shi wajan shela mara dadi a da can lokacin ana yaki.
Kuma ni Suleiman ina jin dadi kwarai da alfahari da wannan sarauta tawa domin yadda ake jingina ni da Mai martaba Sarkin Zazzau, a ce wai kamana yau ga shi ana alakanta ni da wani bawan Allah mai tausayi mai kula da al’umma mai kokarin taimaka wa masu rauni don haka ina jin dadin danganta ni da shi, domin ina cikin tafiya za ka ji an ce ga Sarkin Kugen Sarkin Zazzau nan ka ga ai abin jin dadi ne a dubi kamata ana danganta ni da shi.
Magaji fa? To wannan na Allah ne amma dai yanzu haka ina da mata biyu da ’ya’ya goma kuma namijin da nake da shi yaro ne karami don haka na bar wa Allah komai wajen wanda zai gaje ni domin ni ma ai kakana na gada.
A karshe Sarkin Kugen ya ce, yana yi wa Allah godiya da Ya daga darajasa ta sarautar da ya gada a gidansu “Sannan ina kira ga matasa su daina zama haka kawai su yi kokarin neman ilimi na addini da na zamani da kuma yin sana’a,” inji shi.