Zaben Shugaban kasa da Majalisar Dokoki ta kasa da aka gudanar a ranar Asabar da ta gabata kuma aka karasa a wasu jihohi a ranar Lahadi ya gudana cikin kwanciyar hankali da lumana, tare da kawo sauyin da iskarsa ta fara kadawa lokacin da wasu jam’iyyun adawa suka hade suka kafa babbar jam’iyyar adawa ta APC a bara.
Zaben wanda aka rika takaddama kansa bayan dage shi da mako shida, ya kawo karshen mulkin Jam’iyyar PDP na shekara 16, bayan da dan takarar Shugaban kasa na Jam’iyyar APC Janar Muhammadu Buhari ya kada Shugaban kasa mai ci Dokta Goodluck Jonathan a zaben da kuri’a miliyan 15 da dubu 405 da 928 inda Jonathan ya samu kuri’a miliyan 12 da dubu 663 da 950.
Daga Jihar Bauchi wakilinmu Hamza Aliyu ya ce Jam’iyyar APC ta lashe zaben Shugaban kasa da gagarumin rinjaye, yayin da ta lashe kujerun sanatoci uku da na majalisar wakilai 12. dan takarar Sanata a karkashin Jam’iyyar APC a mazabar Bauchi ta Kudu Malam Ali Wakili ya doke Gwamnan Jihar Malam Isa Yuguda na Jam’iyyar PDP, yayin da Aliyu Hamma Misau na APC ya doke mataimakin shugaban masu rinjaye a Majalisar Dattawa Abdul Ahmed Ningi daga mazabar Bauchi ta Tsakiya, sai Sanata Nazifi Gamawa na Jam’iyyar APC ya doke dan takarar PDP Farouk Mustapha daga mazabar Bauchi ta Arewa.
Daga Kano wakilinmu Jabiru A. Hassan, ya ruwaito cewa Jam’iyyar APC ce ta lashe zaben Shugaban kasa da sanatoci da ’yan majalisar wakilai 24 da ke jihar.
Ya ce baturen zaben jihar Farfesa Muhammad Harisu yake bayyana cewa sakamakon zaben ya ce Jam’iyyar APC ta samu kuri’a miliyan daya da dubu 909 da 999, PDP kuma ta samu kuri’a dubu 219 da 779 a zaben Shugaban kasa. Sannan APC ta lashe kujerun Majalisar Dattawa uku da daukacin ’yan majalisar wakilai 24 daga jihar.
Sanatocin da suka samu nasara sun hada da Gwamnan Jihar Dokta Rabi’u Musa Kwankwaso da Sanata Kabiru Ibrahim Gaya da ke wakiltar Kano ta Kudu, wanda wannan ne karo na uku da yake lashe zabe a mazabar, sai Alhaji Barau Jibrin, wanda ya taba zama dan majalisar wakilai a 1999.
Daga Jihar Kaduna wakilinmu Mohammad Yaba, ya ce tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Ahmed Makarfi da tsohon Sanata Ahmad Aruwa sun fadi a zaben majalisar dattawa da aka gudanar a jihar.
Alhaji Suleiman Hunkuyi na Jam’iyyar APC kuma tsohon Kwamishina a zamanin Gwamna Makarfi ne ya doke Sanata Makarfi a Arewacin Kaduna da kuri’a dubu 447 da 917 shi kuma Makarfi ya samu kuri’a dubu 136 da197.
Wani dan rajin kare hakkin dan Adam Kwamrade Shehu Sani na Jam’iyyar APC kumaa ya doke Sanata Ahmed Mohammed Mukhtar Aruwa na PDP a mazabar sanatan Kaduna ta Tsakiya da kuri’a dubu 468 da 964, yayi Aruwa na PDP ya samu kuri’a dubu 168 da 241.
Ya’u danjuma Laah na Jam’iyyar PDP ya doke Dokta Ishaku Shekarau na Jam’iyyar APC a mazabar sanatan Kudancin Kaduna da kuri’a dubu 259 da 239 yayin da Shekarau ya samu kuri’a dubu 119 da 22.
Daga Jihar Zamfara wakilinmu Shu’aibu Ibrahim ya ce Jam’iyyar APC ta lashe zaben Shugaban kasa a jihar da kuri’a dubu 612 da 202, yayin da PDP ta samu kuri’adubu 144 da 833, kamar yadda babban jami’in tattara sakamakon zaben Farfesa Abdullahi Abdu Zuru ya fadi a Gusau.
Sai dai jam’iyyar PDP ba ta ji dadin karon ba, inda Sanata Sahabi Ya’u kaura da ’yan majalisar wakilai biyu masu ci Bilyaminu Shinkafi da Sani Umar suka rasa kujerunsu ga Jam’iyyar APC, inda har wa yau APC ta lashe sauran kujerun sanatocin da na majalisar wakilan.
Daga Jigawa wakilinmu Umar Akilu Majeri ya ce Jam’iyyar APC ce ta lashe kujeru uku na majalisar dattawa da kujerun majalisar wakilai a zaben da aka gudanar.
Alhaji Sabo Muhammed Nakudu na Jam’iyyar APC ya lashe kujerar sanata da kuri’a dubu 237 da 947 yayin da abokin karawarsa na Jam’iyyar PDP Abdulmumini Hassan Zareku ya samu kuri’a dubu 93 da 420. A shiyyar Hadeja mazabar da shugaban majalisar jihar Adamu Ahmed Sarawa ya shekara 16 na wakiltarsu, kuma ya tsaya takarar sanata, tsohon Mataimakin Gwamnan Jihar Alhaji Ubali Shitu Hadeja na Jam’iyyar APC ya kada shi da kuri’a dubu 193 da 950 yayin da Sarawa na PDP ya samu kuri’a dubu 97 da 196. Sai Sanata danladi Sankara na PDP da ya sha kasa da kuri’a dubu 136 da 574, yayin da dan takarar Jam’iyyar APC Malam Abdullahi Abubakar ya samu kuri’a dubu 270 da 239, kamar yadda babban jami’in tattara sakamakon zaben Farfesa James Ayatse ya sanar.
Daga Nasarawa wakilinmu John D. Wada, ya ruwaito cewa Jam’iyyar PDP ce ta lashe zaben Shugaban kasa da kuri’a dubu 273 da 460, yayin da Jam’iyyar APC ta samu kuri’a dubu 236 da 838, kamar yadda baturen zaben jihar Farfesa Hassan Rafindadi ya bayyana.
A zaben sanatan Nasarawa ta Yamma Dokta Abdullahi Adamu ya sake komawa kan kuejararsa da kuri’a dubu 98 da 321, yayin da a abokin takararsa Aliyu Wadada na PDP ya samu kuri’ dubu 79 da 834. A mazabar Nasarawa ta Kudu kuwa, Akitet Salihu Huseini Igyebola na Jam’iyyar APC ya doke Sanata Suleiman Asonye Adokwai na Jam’iyyar PDP da kuri’a dubu 95 da 760 shi kuma Sanata Adokwai ya samu kuri’a dubu 91 da 981. A mazabar Nasarawa ta Arewa Philips Aruwa Gyunka na Jam’iyyar PDP ne ya lashe zaben sanata da kuri’a dubu 32 da 761 inda abokin takararsa na Jam’iyyar APC Alhaji Hamza Idris ya samu kuri’u dubu 21 da 321
Daga Jihar Gombe wakilinmu Rabilu Abubakar ya ruwaito cewa Jam’iyyar APC ta lashe kujerun sanata biyu da ’yan majalisar wakilai hudu a zaben na ranar Asabar, yayin da Jam’iyyar PDP ta samu sanata daya da ’yan majalisar wakilai biyu.
Ya ce zaben ya gudana ne cikin fargaba bayan samun labarin ’yan Boko Haram sun kai hari kauyen Shole a karamar Hukumar Funakaye inda suka kashe farar hula biyu da dan sanda daya kafin su wuce Dukku su kashe dan majalisar jihar daga Dukku ta Kudu Alhaji Umar Aminu da ake kira Mai Masallaci.
Tsohon Gwamnan Jihar kuma dan takarar Jam’iyyar APC, Sanata danjuma Goje daga Gombe ta Tsakiya ya kayar da Usman Bello Kumo na PDP, yayin da tsohon Mataimakin Shugaban Majalisar Wakilai Alhaji Usman Bayero Nafada ya lashe kujerar Gombe ta Arewa a karkashin Jam’iyyar APC, Mista Joshu’a Lidani na PDP daga Gombe ta Kudu ya cinye zaben mazabarsa.
’Yar majalisar wakilai ta PDP daga Kaltungo da Shongom, Hajiya Fatima Binta Bello, ta ci zabe a karo na biyu sai Ali Isa JC daga billiri da Balanga wanda ya kayar da Yusuf Manu Swa. Ustaz Yunusa Abubakar na APC ya kayar da dan majalisa mai ci a PDP Shu’aibu Umar Galadima a Gombe ta Tsakiya, sai mazabar Gombe da Kwami da Funakaye inda Yaya Bauchi Tongo na APC ya kada Ya’u Hassan Marafa na PDP, sai tsohuwar Ministar Ilimi A’ishatu Jibrin Dukku, ta APC ta kada abokin karawarta Talban Dukku a mazabar Dukku da Nafada.
Daga Jihar Adamawa wakiliyarmu Amina Abdullahi ta ruwaito cewa dan tubabben Gwamnan Jihar Admiral Murtala Nyako ya ci zaben sanata na Arewa maso Yammacin Jihar.
Alhaji Abdul’azeez Nyako ya yi nasara da kuri’a dubu 126 da 406, yayin yayin da mai bi masa Hajiya A’isha dahiru ta Jam’iyyar PDM ta samu kuri’a dubu 91 da 578, sai Dokta Idi Hong na PDP y azo na uku da kuri’a dubu 48 da 506.
Daga Taraba wakilinmu Magaji Isa ya ce, kwamishinan zabe a jihar Malam Ahmed Makama ya ce Jam’iyyar PDP ta samu galaba a zaben Shugaban kasa da kuri’u dubu 310, sai APC ta samu kuri’a dubu 261 da 326. Kuma ya ce mukadashin Gwamnan Jihar Alhaji Sani Abubakar danladi na PDP ne ya lashe zaben sanatan Arewacin jihar da kuri’a dubu106 da 163 dan takarar APC Alhaji Ali Sani Kona ya samu kuri’a dubu 99 da 440.
Sai Alhaji Bashir Marafa na Jam’iyyar PDP ya zama sanatan Taraba ta Tsakiya da kuri’a dubu 48 da 582, dan takarar APC Yusuf Alhaji Yusuf ya samu kuri’a dubu 38 da 620. A Taraba ta Kudu Sanata Emmanuel Bwacha na PDP shi ya lashe kujerar sanatan da kuri’a dubu 114 da 249 Janar Ishaya Bauka na Jam’iyyar SDP ya samu kuri’a dubu 42 da 846.
Sai dai Jamiyyar APC a jihar ta ki amincewa da sakamakon zaben na ranar Asabar, inda shugabanta Alhaji Hassan Hardo ya yi zargin cewa an yi amfani da sojoji da jami’an tsaro da ma’aikatan hukumar zabe da ’yan Jam’iyyar PDP wajen tafka magudi a zaben.
Ya ce an tafka magudi a mazabu da dama a kananan hukumomin Karim-Lamido da Sardauna da Bali da Takum da Wukari, inda aka mured nasarar ’yan takararsu aka ba na PDP.
Ya ce jam’iyya zata bi hanyoyin da dokar kasa ta tanada don karbo kujerun da ’yan takararta ta ci.
Daga Yobe wakilinmu Sani Gazas Chinade, ya ce Janar Muhammadu Buhari na Jam’iyyar APC ne ya lashe zaben Shugaban kasa da kuri’a dubu 446 da 265 yayin da dan takarar Jam’iyyar PDP Goodlukc Jonathan ya samu kuri’a dubu 25 da 526.
Kwamishinan ya kara da cewar, a Jam’iyyar APC ta lashe kujerar sanatoci biyu, inda Sanata Bukar Abba Ibrahim ya lashe kujerar Yobe ta Gabas, ya kada abokin karawarsa Abba Gana Tata na PDP, sai Sanata Ahmed Lawan na APC ya lashe ta Yobe ta Arewa, inda ya doke tsohon Minista Yerima Lawan Ngama na PDP.
A Kudancin Yobe, Muhammad N. Hassan na PDP ne ya kada Sanata mai ci Alkali Abdulkadir Jajere na APC. Jam’iyyar APC ta kuma lashe kujera biyar daga cikin shida na Majalisar Wakilai, inda ta bar PDP da daya.
Daga Jihar Kebbi wakilinmu Bashir Lawal Zakka ya ce Jam’iyyar PDP mai mulkin jihar ta sha mugun kaye a hannun Jam’iyyar APC inda ta cinye kujerun majalisar dattawa uku na jihar da kuma kujerun majalisar wakilai takwas, inda PDP ta tashi a tutar babu.
Gwamnan Jihar Alhaji Sa’idu dakingari ya sha kasa a takarar sanatan Kebbi ta Arewa a hannun tsohon babban sakatare a ma’aikatar Neja-Delta Dokta Yahaya Abdullahi.