✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Yadda rikicin ’yan kungiyar asiri ke lakume rayuka a Osogbo

Mutane sun koka kan yadda fadan ke jawo salwantar rayuka a jihar.

A ranar Asabar wani mutum ya rasa ransa, yayin wani rikici da ya barke tsakanin ’yan kungiyar asiri a Osogbo, babban birnin Jihar Osun.

Rikicin da ya barke tsakanin ’yan kungiyar asiri ta Aiye da Eiye, ya haifar da zaman dar-dar a Osogbo.

Mutane da dama sun tsere daga yankin da fada ya faru domin tseratar da rayuwarsu.

Wani wanda ya gane wa idonsa abin da ya faru ya shaida wa Aminiya cewar an kashe mutumin ne a makarantar Firamare ta Laro, da ke yankin Isale a Osogbo.

An dauke gawar mutumin zuwa dakin ajiye gawarwaki na asibitin kwararru na Asubiaro.

Sai dai wakilinmu ya kasa samun wayar kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar, Yemisi Opalola, don samun karin bayani game da lamarin.

Mutane da dama a jihar sun bayyana damuwarsu, a kan yadda rikicin ’yan kungiyar asiri ke salwantar da rayuka a jihar.

A satin da ya gabata ma, fadan ’yan kungiyar asirin ya jawo salwantar rayuka biyu a yankin Sabo, a Osogbo.