Ta dai faru ta kare yayin da Kungiyar Kwallon Kafa ta Real Madrid ta Spain ta lashe kofin Zakarun Turai (UCL) a karo 14 bayan doke Liverpool ta Ingila a wasan karshe da ci daya mai ban haushi a ranar Asabar ta makon jiya.
Wasan wanda ya gudana a filin wasa na Stade de France da ke birnin Paris na Faransa, an samu tsaikon fara taka ledar da minti 36 sakamakon wata hananiya da ta tashi a wajen filin saboda kutsen da wadansu magoya baya suka yi inda suka nemi shiga filin wasan da tikitin bogi.
- Yadda shaye-shaye da kwallon kafa ke hada kan Musulmi da Kirista
- Hajj 2022: Maniyyata 1,105 za su sauke farali daga Gombe
Bayanai sun ce lamarin ya fi shafar magoya bayan kulob din Liverpool.
Dan wasan gaban Real Madrid dan kasar Brazil – Vinicius Junior ne ya jefa kwallon a minti na 59; a wasan da magoya baya da ma kocin kungiyar, Carlos Ancelotti suka ce bai zo musu da babban kalubale ba idan aka kwatanta da sauran zafafan wasannin da kungiyar ta yi gabanin wasan karshen.
Yadda Madrid ta tsallake rijiya da baya a wasannin kifa daya-kwale uku
Gabanin kaiwa wasan karshe, Real Madrid ta doke manyan kungiyoyin Turai da suka hada da Paris Saint Germain (PSG) ta mai rike da kofin gasar Faransa da Chelsea mai rike da kofin UCL da kuma Manchester City mai rike da kofin Firimiya ta Ingila.
A wasannin zagaye na biyu, a wasan farko a gidan PSG, Real Madrid ta sha kashi da ci daya mai ban haushi. Sannan a filin wasa na Bernabeu, sai da PSG ta fara jika wa Madrid aiki da karin kwallo guda a raga.
Amma Karim Benzema ya farke kwallayen biyu da karin ta uku duk a cikin minti 17; lamarin da ya bai wa Real damar zuwa zagayen Kwata Fainal.
Benzema ya ci gaba da jan zarensa a zagayen Kwata-Fainal, inda Real ta doke Chelsea a wasan Kwata-Fainal na farko da suka buga a Stamford Bridge – gidan Chelsea – da ci 3 – 1.
Duka kwallayen uku, Karim ne ya zura su a cikin mintuna 25. Ke nan sau biyu yana cin kwallaye uku rigis a jere.
Real ta sake shammatar masu nazarin kwallo a duniya, a wasan zagaye na biyu da ta kara da Chelsea a Spain.
Da farko, Chelsea ta farke kwallayen da Real ke bin ta da rarar guda; amma cikin minti na 80 matashin dan wasan gaban kulob Madrid – Rodrygo ya farke kwallon sannan Benzema ya zura karin guda a ragar Chelsea a minti shida na karin lokaci.
Da haka ne Real ta sallami Chelsea tare da samar wa kanta gurbi a zagayen kusa-da-karshe.
A filin wasa na Etihad, Real ta sha kashi da ci 4 – 3 a hannun Manchester City a wasan farko na zagayen kusa-da-karshe; inda Benzema ya zura kwallo biyu a ragar City yayin da vinicius Junior ya ci guda.
Sai dai lissafi ya sake dagule wa Real a filin wasa na Bernebau bayan da City ta zura kwallo guda a ragarta a minti 73 da fara wasan zagaye na biyu.
Amma kamar a almara, shigar dan wasan gaban kungiyar, Rodrygo ke da wuya sai ya jefa kwallo biyu cikin kasa da minti daya da rabi a ragar City – na farko ana saura dakika 39 minti 90 na wasan ya cika; sannan ya jefa ta biyu ana dakika 50 a karin lokaci.
Cikin minti biyar da karin minti 30 a wasan, Benzema ya zura kwallo da fenareti da ta yi sanadin sallamar City daga gasar yayin da ita kuma Real ta samu nasarar zuwa wasan karshe a karo na 17 a gasar UCL.
Karo na uku a jere ke nan Real na shammatar duniyar kwallon kafa da irin yadda take tsallake rijiya da baya kuma ta yi nasara.
Tun a wasannin rukuni, Real ta doke Inter Milan wacce take rike da kofin Italiya na Serie A, a lokacin gida da waje.
Ke nan za a iya cewa Real ta buge dukkan Zakarun Kasashen Turai kafin ta lashe Kofin UCL.
Shekarun da Madrid ta lashe kofin UCL
A kakar farko ta wasan kofin Zakarun Turai da aka fara a 1955/1956, Real ce ta fara cin kofin inda ta doke Kungiyar Stade de Reims ta Faransa.
Real ta ci gaba da cin karenta babu babbaka tana cin kofin har zuwa 1959/1960. Sai da ta ci kofin karo biyar a jere ba tare da wata kungiya a Turai ta ce mata kanzil ba.
Sai a 1965/1966 kofin ya fada a hannun wata kungiyar, sannan ta sake shiga kamfar kofin har zuwa 1997/1998. Ta kuma ci kofin a karo na 8 da 9 a 1999/2000 da kuma 2001/2002.
A shekarar 2014, ta sake cin kofin karo na 10 a wasan hamayya da Athletico Madrid. Real ta kuma jan zarenta inda ta lashe kofin sau uku a jere 2015/2016, 2016/2017 da 2017/2018 – karo na 11, 12 da 13; yayin da a kakar bana ta lashe kofin a karo na 14.
’Yan wasan Real tara da Ronaldo ne kadai ’yan wasan da suka taba cin kofin UCL sau biyar a tarihi, wadanda suka hada da Gareth Bale da Karim Benzema da Casemiro da Nacho da Dani Carvajal da Isco da Toni Kroos da Marcelo da kuma Luka Modric.
A tarihin gasar, kungiya daya ce kawai ta lashe kofin rabin kofunan da Madrid ta lashe a Gasar UCL wato AC Milan wacce ta ci kofin sau bakwai; sai Liverpool mai shida.
Sannan kungiyoyi biyu ne kadai in ban da Real din suka taba lashe gasar har sau uku a jere su ne Ajax da ke Netherlands da kuma Bayern Munich ta Jamus. A nan ma, Real ta zama gagara-badau.
Real Madrid ta yi amanna da wasu camfe-camfe lura da yadda ta yi nasara a dukkan wasannin karshe guda bakwai da ta buga a Gasar UCL, musamman guda biyar na baya-bayan nan, ya nuna cewa akwai wasu dabi’u ko camfe-camfen da suke samun gindin zama a kungiyar.
Jaridar wasanni ta Marca da ke Spain ta ce Real ta sake baje wadannan camfe-camfen a wasan karshe da ta kara da Liverpool a birnin Paris.
Ga camfe-camfen da kungiyar ta yi amanna da su kafin buga wasannin karshe:
Boye muhimman shagulgula
Ka’idar farko ita ce babu magana a kan shagulgulan da za a yi. Kungiyar ta shirya duk irin shagulgulan da zai yi idan ta yi nasarar lashe kofin, amma ana matukar boyewa da sirrinta shagulgulan da za a yi.
Camfin ganawa da ’yan jarida
Karim Benzema shi ne dan wasan da Real Madrid ta zaba ya wakilci kungiyar a ganawa da manema labarai kafin fara wasan da Real ta yi rashin nasara da ci 1-0 a hannun PSG ranar 14 ga Fabrairu.
Lura da Madrid ta yi rashin nasara a wasan, hakan ya sa an hana shi ganawa da manema labarai kafin buga wasan karshe, inda Marcelo da Thibaut Courtois suka wakilci kungiyar a hira da manema labarai.
Jirgin muhimman mutane
A koyaushe, Real Madrid takan dauki shatar jirgin da zai yi jigilar dangi da dillalai da tsofaffin ’yan wasanta da muhimman mambobinta da ’yan jarida da sauran mashahuran mutane.
’Yan jarida irin su Jorge Bustos da Manuel Jabois ana yi musu kallon wadanda a kullum ba a barin su a tafiye-tafiyen wasannin, yayin da shi ma Richard Gere ya kasance a wasan karshe a shekarar 2016 a Milan.
Nacho Pena: Mai sanar da sa’ar Real Madrid
Dan jaridar gidan talabijin na DirecTV ya fara bayyana a wasannin Real tun wasan karshe da ta buga a Lisbon a 2014, kuma tun lokacin yake aikin karfafa gwiwar magoya bayan kungiyar kuma yake sanar da jerin ’yan wasan da za su taka mata leda kafin fara wasan da sanar da kwallayen da aka zura.
Kyalle A kowane wasan UCL, Real Madrid kan fitar da wani kyalle wanda aka rubuta ‘Hasta el final, vamos Real’, da ke nufin ‘Har zuwa karshen, mu je zuwa Real’.
Kroos: Wanda yake karshen sauka daga bas
A dukkan wasannin da Real take karawa musamman masu muhimmanci, kungiyar ba ta garaje da dabbaka wannan camfin ko al’ada.
Mutumin da yake karshen fita daga bas shi ne Toni Kroos. Haka batun yake a kowane lokaci.
Jirgin daukar ’yan wasa
Real Madrid ta tsara jirgin da zai dauki ’yan wasanta a wasannin karshe da aka yi a Lisbon a 2014 da Milan a 2016 da Cardiff a 2017 zai zama jirgi guda ne.
Al’adar hakan ta faro ne tun tafiyar kungiyar zuwa Lisbon, bayan da Real ta yi nasarar lallasa Bayern Munich da ci 4-0 a filin wasa na Allianz Arena a wasan kusa-da-karshe.
Sai dai ta karya wannan al’ada a tafiyarta zuwa Kiev sakamakon nisan zango da kuma sauya jirgi.
Daukar hoto da babban zakara
Za a iya cewa wannan ne kawai al’adar da kungiyar ba ta bi shi ba, saboda a yanzu Cristiano Ronaldo ya yi adabo da ita.
Dan kasar Portugal din da Marcelo da Casemiro sun kasance suna daukar hoto tare a hanyarsu ta zuwa duk birnin da zai dauki bakuncin wasan karshe na Zakarun Turai.
Sai dai rubuta tarihin nasarar cin Kofin Zakarun Turai (UCL) karo na 14 da Real Madrid ta yi ba zai kammala ba,ba tare da ambatar gudunmawar da dan wasan gaban kungiyar, Karim Benzema ya yi ba, wanda ya ci kwallaye 15 jimilla a gasar–10 daga ciki ya zura su ne a zagayen kifa-daya-kwale.
Sannan an zabi Benzema a matsayin dan wasan gasar bana ta Zakarun Turai da ya fi bajinta.