Hukumar Kula da Hanyoyin Ruwa na Cikin Gida a Najeriya (NIWA) ta dora laifin rashin fara aikin Tashar Jirgi ta Baro a kan rashin kyan hanya.
Shugaban NIWA George Moghalu ya ce hukumarsa na aikin da masu ruwa da tsaki domin ganin hukumomin da ke da alhakin sun gyara hanyar zuwa tashar ta Baro.
Moghalu ya bayyana muhimmancin tashar ga harkar sufurin ruwa na cikin gija wanda shi ne kashin bayan samar da kaya ga Tashar Jiragen Ruwa a Kan Tudu da ke Kaduna da takwarorinta da Gwamnatin Tarayya ke shirin budewa.
A zantawarsa da wakilin Aminiya a kan tashar jirgin da aka gina a kan Naira biliyan 5.8 Moghalu ya ce NIWA na duba yiwuwar tuntubar Gwamnatin Jihar Neja ta hada kai da Gwamnatin Tarayya su gyara titunan.
Masu ruwa da tsaki sun sha kokawa game da yadda tashar jirgin ruwan ba ta aiki, shekara guda bayan Shugaba Muhammadu Buhari ya kaddamar da ita a jihar Neja.
Ko a baya-bayan nan Etsu Nupe Alhaji Yahaya Abubakar da Gwamnatin Jihar Neja sun bukaci Gwamnatin da ta hanzarta aikin babban titin Agaie zuwa Katcha zuwa Baro har ya karasa zuwa tashar jirgin ruwan.
Basaraken da kuma Gwamna Abubakar Sani Bello sun bayyana tashar ta Baro a matsayin jigo wurin habaka tattalin arziki a yankin Arewacin Najeriya da ma kasar baki daya.
Aminiya ta ruwaito cewar manyan tituna biyu da ke zuwa tashar da suka hada da Baro/Katcha/Agaie da kuma ta Baro/Muye ta Bulla ta Gegu a kan hanyar Abuja/Lokoja sun lalace sosai.
Daga ciki, Gwamanti Tarayya ta bayar da aikin gyaran hanyar Baro/Agaie mai nisan kilomita 55.