Kafin yanzu mutanen Kano ba su dauki noma kabewa wani abin ku-zo-ku gani ba, sai da lamarin ya sauya da bukatar kabewar cikin lokacin kankani ta sa wasunsu arzikin dare daya.
An dade noman kabewa bai yi farin jini da kawo wa masu yin sa kudin shiga ba, kansancewar a yanzu ana shuka kabewar a matsayin raba-danni a gonaki da ya samar wa da manoma abin kashewa a lokacin da ake fama da matsin tattalin arziki a kasar nan.
Alhaji Garba Adamu wani manomi ne da ke zaune a Karamar Hukumar Takai, a hirarsa da wakilinmu ya bayyana cewa, a da bai dauki noman kabewa wani noma na kirki ba, sai lokacin da ya ankara da yadda yanzu mutane ke neman kabewar ruwa a jallo don amfaninsu na yau da kullum.
Manomin ya ce, ya soma ne da ware wani dan wuri a gonarsa, inda yake shuka kabewar domin gwaji da kuma amfanin kashin kansa, amma daga baya ya canza shawarar mayar da hankali wajen nomanta ka’in da na’in.
“Nakan shuka kabewar ne domin amfanin kaina a inda na ke shukata ta a tsakanin masara, amma sai na fahimci cewa zan iya samun kudi mai yawa daga gare ta in na mayar da hankali.
“La’akari da yawon nemanta da ake yi. Hakan ta sa na ware wani wuri a gonata domin gwaji.
“Gaskiya amfanin da na samu ya ba ni mamaki da hakan ta sa na ware wani wuri na musamman don shuka kabewa ita kadai.
“Za ka yi mamaki idan na fada maka cewa a yanzu kudin da ke samu ya fi na masarar da nake nomawa tsowon lokaci,” in ji shi.
Wani manomin mai suna Musa Zangina kamanta noman kabewa ya yi da lu’ulu’u ko zinaren karkashin kasa da sai mai rabo ne kaɗai ke samun sa, kasancewar babbar matsalar nomanta shi ne wurin ajiya.
“Yanzu manoman kabewa su ne attajiran da harkar take kai musu. Sai dai ba girin-girin ba, ta yi mai.
“Domin babbar matsalar kabewa shi ne ajiya da kuma kwarewa wajen kula da ita kafin a ci kasuwarta,” in ji Zangina.
A yayin zantawa da wakilinmu, Alhaji Auwalu Aliyu wani dillali a kasuwar kayan gwari ta ‘Yankaba a cikin garin Kano ya ce, lokaci guda kabewa ta zama abin nema ruwa a jallo, a inda masu sayen ta ke zuwa daga ciki da kuma wajen Kano har ma da wasu makwabtan kasashe.
Wanda hakan ba zai rasa nasaba da fa’idar da aka gano take da shi a matsayin abinci da kuma magani ba.
“An gano sirrin amfani da Kabewa ne daga masu maganin gargajiya wanda hakan ta sa mutane suka raja’a wajen neman Kabewar.
“Kasancewar suna amfani da kwallon da kuma bawon wajen maganin Olsa kuma mutane sun ce yana yi.
“Haka kuma yawan magana kan fa’idojinta a matsayinta na abinci ya sa mutane neman ta domin amfani da ita kamar yadda ake yi a shekarun baya,” in ji shi.
Dillalin ya kuma ce, a lokacin tsaka da neman kabewar sukan yi lodin akalla manyan motoci biyar a kasuwr don kai kabewar ciki da wajen jihar da kuma wasu kasashe makwabta, musamma Jamhuriyar Nijar da Kamaru da sauransu.
An kuma gano wasu jihohi na Arewa kamar Katsina da Kaduna da Zamfara da Sakkwato da kuma karin wasu manyan garuwan Kano da cewa duk su ma yanzu suna noman kabewar kuma suna kawo wa kasuwar ta ‘Yankaba domin sayarwa.
A yanzu farashin kabewar ya hau a kasuwar da kuma sauran wurare, domin ba za ka samu ‘yar karamar kabewa kasa da Naira 2,000 ba.
Yayin da farashin babba kan kai tsakanin Naira 3,500 zuwa Naira 5,000 a kan kowacce daya.
Yanzu a kasuwar ‘Yan Kaba a kullum a cike take da masu sayen kabewar ko domin amfanin yau da kullum na kashin kansu ko kuma don jarraba maganin da aka ce tana yi na wasu cutuka.