Gwamna Abba Kabir Yusuf, ya caccaki tsohon Sakataren Gwamnatin Jihar Kano, Abdullahi Baffa Bichi da cewa maƙaryaci ne da ba shi da “kunya”.
Gwamnan ya bayyana haka ne a yayin wani taro da ya yi tare da ilahirin kansiloli 484 da ke fadin jihar a ranar Lahadi da maraice.
- Kotu za ta rataye matashi kan kisan karuwa
- Lakurawa: Yadda mafarauta 13 suka gamu da ajalinsu a Sakkwato
Abba Kabir Yusuf ya ce gwamnatinsa ba wajen zaman ɓarayi ba ce sabo da jajircewa wajen yaƙi da cin hanci da rashawa.
Da ya ke jawabi a wajen taron da kansilolin, Gwamna Yusuf ya ce gwamnatinsa ba za ta lamunci satar kudin al’umma ba.
A cewarsa, yana jagorantar gwamnati mai tsafta da kaffa-kaffa wajen sace kudin al’umma, inda ya jaddada cewa “ɓarawo ba ya zama a gwamnatin mu,”
Ya ce wannan kokarin yaki da din hanci ne ya sanya gwamnatin ke samun makudan kuɗaɗen da ta ke ta bijiro da ayyuka domin jin dadin al’ummar Kano.
Abba ya mayar da martani kan zarge-zargen da Baffa Bichi ya yi cewa gwamnatin Jihar ta Kano tana tafka laifuka na cin hanci da rashawa fiye da gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje, ta musanta dukkan zarge-zarge waɗanda ta bayyana a matsayin “abin dariya”.
“Zarge-zarge ƙarya ce tsagwaronta kuma abin dariya, Baffa Bichi babban maƴaryaci ne, kuma dukkan abin da ya faɗa ƙarya ce ziryan,” in ji Gwamnan.
“Musamman, Gwamna ya yi watsi da zargin cewa Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, shugaban Tsarin Kwankwasiyya, yana karɓar naira biliyan biyu duk wata daga gwamnatin Jihar Kano.
Gwamna Abba Yusuf ya bayyana wannan zargi a matsayin “ƙololuwar ci-da-zuci na siyasa da rashin gaskiya.”
Gwamnan ya ce Baffa Bichi ya kwashe fiye da shekara ɗaya a cikin gwamnatinsa amma bai yi waɗannan zarge-zarge ba sai bayan an sallame shi daga aiki bisa rashin iya aiwatar da ayyukansa, yana mai cewa da a ce da gaske yake da sai ya yi zarge-zargen a lokacin da yake cikin gwamnati.
Ya ce zai ci gaba da gudanar da mulki cikin adalci, yana mai yin kira ga al’ummar Jihar Kano ta yi watsi da irin waɗannan zarge-zarge na ‘yan siyasar da ska rasa tasiri.