Tsohon Gwamnan Jihar Imo, Ikedi Ohakim, ya bayyana yadda shi da ’ya’yansa suka tsallake rijiya da baya a harin da aka kashe ’yan sandan da ke tsaron lafiyarsa.
Aminiya ta ruwaito yadda mahara suka kai wa ayarin motocin Ohakhim farmaki a ranar Litinin, suka kashe ’yan sanda da ke tsaron lafiyarsa a Karamar Hukumar Ehime Mbano da ke Jihar Imo.
- Kotu ta ba da belin matashin da ya sace kayan N4m
- ’Yan Najeriya sun koka da karancin sababbin takardun kudi a bankuna
A tattaunawarsa da kafar TheNiche mai yada labarai ta Intanet, tsohon gwamnan ya ce, “Muna tafiya tsakanin Isiala Mbano zuwa wadannan mutanen suka tare mu.
“Sun kawo mana farmaki ta baya suka dinga harbi babu kakkautawa, na dauka na mutu ina tare sa ’ya’yana — mace da namiji.
“Abin da ya ceci ni shi ne wannan motar sulken; Ina raye a yau ne saboda Ubangiji ya nufa da kuma taimakon motar sulke.
“Sai dai abun takaici shi ne sun kashe mana yara hudu ciki har direbana; Gaskiya ne mun rasa mutum hudu kuma abun ya dame ni. Wane laifi suka yi musu?”
Ohakim, ya ce bayan direbansa ya tsere daga wajen, maharan “Sun bi bayanmu suna harbin tayar motarmu. Ubangiji Ya taimake mu tayar motar tana iya tafiya ko babu iska.
“Tayar ta dauke mu tsawon minti 20 kafin mu iso gida kafin ta sace gaba daya.
“Direban yana da kwarewa sosai, ya dinga musu yawo da hankali har muka bace musu a daidai Mahadar Umuahia, daga nan ya bi wata hanya su kuma suka kasa gane inda muka yi.
“Bayan mun dawo ne gidan gwamnati suka aike da karin jami’an tsaron da suka kawo gawarwarkin yaran nawa da suka kashe.
“Wannan ya fi karfin a ce ’yan awaren IPOB ne gaskiya. Wadannan kwararru ne, sun samu horo sosai. Sun zo a cikin mota kirar BMW. Sun zo da nufin kashe ni ne.”