Najeriya ta ci bashibn Naira tiriliyan 225.93 a cikin shekrara 20 da suka gabata, wanda ya kusa ninka Naira tiriliyan 114.46 ta kasar ta samu na kudaden shiga a tsawon lokacin.
Alkaluman da Babban Bankin Najeriya (CBN) ya fitar sun nuna Gwamnatin Tarayya da jihohi 36 da kananan hukumomi 774 ne suka ciyo basukan daga shekarar 2001 zuwa 2022.
- ’Yan bindiga sun kashe, sun sace ’yan yawon Sallah a Katsina
- DAGA LARABA: Yadda Matsalar Tsaro Da Rashin Tsari Suka Ruguza Ilimi a Zamfara
Masana sun bayyana yawan basukan a mastayin babban abin damuwa, ganin da yadda tattalin arzikin Najeriya ya fi dogaro a kan danyen mai.
Yadda aka tara bashin N225trn a shekara 20
Kididdigar yawan basukan Naira 225.9 a tsawon shekara 20 da CBN ta fitar a watan Mayu ya nuna an ciyo bashin Naira tiriliyan 142.413 a cikin gida, sai kuma Naira tiriliyan N83.529 daga kasashen waje.
Bashi mafi yawa da aka ciyo a cikin gida shi ne na Naira tiriliyan 92.95 da Gwamnatin Tarayya ta karba ta hanyar raba takardun lamuni tun daga shekarar 2003.
Mai bi masa shi ne Naira tiriliyan 38.458 na takardun ‘Treasury Bills’.
Gwamnatin ta kuma tara karbi bashin Naira tiriliyan 6.526trn ta hanyar takardun lamunin ‘treasury bonds’; sai kuma Naira tiriliyan 2.86l ta takardun ‘promissory notes’.
A shekarar 2014 kuma, sakamakon faduwar farashin danyen mai gami da biyan tallafin man da kuma yawan basuka da ake bin Najeriya, Gwamnatin Tarayya ta shiga neman rance a cikin gida.
A sakamakon haka ta bullo da takardun rancen Sukuk da ‘Green Bond’ da kuma ‘Saving Bond’.
Aminiya ta gano Gwamnatin Tarayya ta samu rancen Naira tiriliyan 1.475 daga tsarin Sukuk da ta bullo da shi a 2017.
Ta kuma samu rancen Naira biliyan 98.45 daga Green Bond sai Saving Bond da ya sama mata Naira biliyan 59.34 tun daga 2017 da gwamnatin ta fara bayar da takardun lamunin biyu.
Yadda gwamnatoci suka raba N114trn da suka samu
Kididdihar alkaluman kudaden shiga na Naira Turkiya 114 da gwamnatocin suka samu a sheka 20 — daga 2001 zuwa 2021 — da CBN din ta fitar a watan Mayu ya nuna Gwamnatin Tarayya ta samu Naira tiriliyan N50.020, jihohi tiriliyan N31.147, kananan hukumomi kuma tiriliyan N23.625.
Naira tiriliyan 9.670 kuma an ba wa jihohi masu arzikin man fetur a matsayin kashi 13 cikin 100 da doka ta ware musu don kyautata rayuwar mazauna da gyara yankunan da ayyukan hakar mai ya gurbata wa muhalli.
Jihohi masu arzikin man su ne Delta da Akwa Ibom da Bayelsa da Ribas da Edo da Ondo, da Imo da Legas da kuma Abiya — ko da yake Akwa Ibom da Ribas da Bayelsa da Delta ke samar da kashi 95 cikin 100 na man da Najeriya ke da shi.
Kudaden shiga mafi tsoka da Gwamnatin Tarayya ta samu su ne Naira tiriliyan 8.515 a 2013, zamanin tsohon Shugaban Kasa Goodluck Jonathan, lokacin farashin gangar danyen mai Dala 98.
Na biyu shi ne Naira tiriliyan takwas da aka tara a 2018 zamanin Shugaba Buhari, lokacin farashin gangar danyen mai Dala 71.34.
Amma abin da kasar ke tarawa na kudaden shiga a shekara ba ya haura Naira tiriliyan biyan, in banda a karshen shekarar 2021 da aka samu Naira tiriliyan N7.751.