✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda na tuka keke daga Kaduna zuwa Legas don Buhari – Kabiru Ja’afaru

Aminiya ta samu tattaunawa da Malam Kabiru Ja’afaru wanda ya tuka kekensa tun daga Kaduna zuwa Legas don ya jinjina wa Yarabawa kan goyon bayan…

Aminiya ta samu tattaunawa da Malam Kabiru Ja’afaru wanda ya tuka kekensa tun daga Kaduna zuwa Legas don ya jinjina wa Yarabawa kan goyon bayan da suka bai wa zababben shugaban kasa Janar Muhammadu Buhari. Malam Ja’afaru ya bayyana kalubalen da ya fuskanta da kuma abubuwan da ya gani a kan hanya.

Aminiya: Za mu so ka gabatar da kanka da kuma dalilin da ya sa ka yi wannan tafiya?

Sunana Kabiru Jafaru. Na fito daga jihar Kaduna ne, a Hayin Rigasa, karkashin masarautar Alhaji Kabiru Gangarida. Na kai kimanin shekara 35. Ina da mata daya da ’ya’ya hudu. Ban yi karatun boko ba sai dai na Arabiyya. Na yi wannan tafiya ne don in jinjina wa Yarabawa bisa kokarin da suka yi, kuma na yi ne don in nuna wa duniya cewa akwai hadin kai a tsakanin mutanen Najeriya, babu bambanci tsakanin musulmi da kirista a Najeriya. Da yardar Allah muna kyautata zaton wannan gwamnati za ta yi adalci. Saboda idan ka duba za ka yadda aka yi zaben da ya gabata wanda duk duniya ta shaida an yi shi bisa gaskiya da adalci.
Aminiya: Me ya sa ka yanke shawarar ka yi tafiya a kan keke a maimakon ka yi da kafa kamar yadda wadansu suka rika yi?
Ai ni ma zan iya yin tafiyar a kafa, amma ni na yi niyya in yi tafiyar ne a kan keke kuma haka na ga ya fi dacewa. Kuma a lokacin da zan yi tafiyar na tanadi keke da tufafi biyu da kayan Fulani da rediyo da solusho da fanfon buga iska da adda da sanda da ruwan sha da ’yan kudin kashewa, amma kafin tafiyar ta yi nisa duk komai ya kare. Sai abin da bayin Allah suka rika ba ni.
Aminiya: Ya tafiyar ta kansace kuma wadanne kalubale ka gamu da su a kan hanya?
Na taso tun ranar 27 ga watan da ya gabata da asuba. Ina kammala sallar asuba na je na yi sallama da sarkinmu, ya ba ni takarda ya ce mini duk inda na je in nuna musu takardar da yardar Allah za a ba ni wurin kwana. Kuma haka aka yi, duk garin da na je da na nuna musu takardar sai ka ga an karbe ni hannu bibbiyu. Wani wurin kuma da sun ga tutar jam’iyyar APC sai ka ana ba ni goyon baya. Lokacin da zan taso akwai ’yan jarida duk sun yi ba ni gudunmawa. Na taso ke nan na fara tafiya sai na fara haduwa da kwazzabai da kuma manyan motoci suna wucewa ba tare da sun tausaya mini ba, wadansu sai su tura ni gefen hanya, sakamakon haka sai tayata ta sacce. Daga bisani sai na lura ashe tayar ba irin wanda ake buga masa iska ba ne, tayar tubeless ce. Ga shi ban iso Buruku ba, sai na ci gaba da tura keken, can ina tafiya sai na hadu da maharba sun fito daga daji sai na yi musu sallama na ce musu ga halin da nake ciki, nan take sai suka tsaya da kekunansu, suka yi mini faci suka ba ni ’yan ki-bawul na tif muka yi sallama na ci gaba da tafiya. Na kama tafiya na wuce garin Buruku kafin in kai wani gari ana ce masa Udawa, sai tayar ta sake saccewa. Haka na rika tura keken, sai da na kai ga inda wadansu sojoji suke, sai wani daga cikinsu ya tsayar da ni. To dama lokacin sallah ya yi kuma gashi na hango wani masallaci da wata yarinya tana sayar da abinci sai na karasa wurin, na ce ta zuba mini na naira talatin, ta zuba mini ina ci ke nan sai wannan sojan ya sake daka mini tsawa ya ce in zo wurinsa, ni kuma sai na debi ruwa na yi alwala na yi sallah, na zauna ina wuridi, sai wannan sojan da ya ga ban zo ba sai ya yi fushi ya taso ya zo yana yi mini tsawa, yana cewa me ya sa da ya kira ni ban zo ba? Ban san a nan wurin suke cakin na ababen hawa ba? Sai na ce yallabai abinci na ci kuma na yi sallah kuma ni matafiyi ne, sai kawai ya ce karya kake, kai dan boko haram ne. Sai kawai ya sa kafa ya ture kekena, sai ni kuma na fara istirja’i, Sai ya ce ina ruwansa da APC, ba lokacin zabe ya wuce ba, sai kawai ya fisge tutar APC da na sanya a gaban kekena, sai na ce bari in nuna maka daga inda na fito, ina fito da takardar da Sarki ya ba ni sai ya fisge ta har ya yaga wani bangare na takartdar, yana cewa ina ruwana da wannan takardar, sai ya rika cewa ni dan Boko Haram ne, ina zan je da kayan fulani da adda da sanda? Sai na ce zan je Legas ne, sai ya kwashe da mari har sau biyu. Da ya mare ni na ga cewa idan na yi wasa zai yi mini sharri, in bai harbe ni ba zai yi mini illa, sai na yi hikima na tattara kayana na daure, sai ya fara tambayar mutanen da ke wurin yana cewa kun san shi? Sai suke ce ba su san ni ba. Sai ya ce ‘oya tafi-tafi,’ sai na ce keken ya sace sai ya ce in dauki keken a kaina in tafi, sai na yi sauri na ci gaba da tura keken a haka. Har sai da na je cikin garin Udawa, ina zuwa sai na tambaye su ko suna da ofishin ’yan sanda sai suka ce sai dai in je wurin ’yan kato da gora, ina tunkararsu sai suka rika ihu suna murna suna cewa sai baba! sai wannan abin da sojan ya yi mini ya fita daga raina, don mutanen garin sun karrama ni da ruwa da abinci. Daga nan sai na ci gaba da tafiya a haka ina tura keken, idan na gaji na hau shi a haka, har na zo wani gari ana kiransa Kuriga-Mai- ’yan mata, a nan na fara kwana. Ai tun da na fara tafiya sai da na yi kwana bakwai ban yi barci ba. Idona sai zafi yake yi, ni dai burinna in wayi gari in gan ni a Legas. Kuma har ga Allah ban taba zuwa Legas ba, wannan shi ne zuwana na farko.
Aminiya: Ta yaya ka gane hanya?
Gaskiya ban tanadi wani abu da zai rika nuna mini hanya ba, sai dai akwai wani direba da ya san hanyar ana ce masa Abu Sha’aban, shi ya rika kirana yana tambayata inda nake, idan na gaya masa sai ya ce to ka bi wuri kaza ko ka bi dama ko hagu ko kuma gabas ko kudu ko arewa ko yamma. Wani lokaci ma sai ya ce mini ka yi a hankali a wurin da kake akwai rami ko kwazazzabo ko kwana ko hawa ko kuma gangara. Wani lokaci kuma sai ya ce mini idan ka je gari kaza sai ka yi tambaya. Shi tunda ya ji zan ji tafiyar sai ya kira ni ya ce shi gudunmawar da zai ba ni ita ce zai tamaka mini da kwatance har in kai Legas. Ta haka na zo Legas.
Aminiya: Taya da tuf guda nawa ne suka lalace maka?
Taya guda biyu ne suka lalace mini, shi kuma tuf guda bakwai. Sannan dalilin da ya sa na dauko adda da sanda, a matsayina na bafulatani dole in rike su. Saboda idan bafulatani ya rike su ji yake kamar yadda soja ne da yake rike bindiga, zai iya shiga ko’ina ba tare da wani tsaro ba. Su kuwa kayan fulani na sanyo su ne saboda su kara mini kwarjini da kyau. Na taso tun ranar 27 ga watan Afirilu, na iso Legas ranar Asabar 9 ga watan Mayu, kuma na sauka a gidan Alhaji Bashiru Tofa da ke unguwar Agege, wani Alhaji Kailani ne ya ba ni lambarsa da na zo Legas sai na kira shi ya yi mini kwatance.
Aminiya: Wadannen kalubale ka fuskanta da ka iso yankin Kudu?
Gaskiya al’adar Yarabawa ta burge ni sosai. Farko dai na sauka garin Ogomosho a gidan wani Hardon Fulani Alhaji Umaru. Na ga wadansu al’adu kamar sasanta rigimar aure duk a gidan sarakuna ake warware su. Sun zama tamkar Kotu. Daga nan sai garin Oyo. Na ga hanya daya ce, saboda yadda hanyar take da turi na zo Oyo daga garin Ogomosho. Duk cinyoyina sun goge sosai. Ruwan sama ya dake ni. Daga nan sai garin Alaka inda na kwana a wurin wadansu Hausawa da suka karbe ni suka yi mani kwatancen garin Ibadan inda na je gidan Alhaji Na Sasa. Daga nan sai garin Ogere inda na kwana, daga na sai garin Ibafo sai kuma Legas.
Aminiya: Shin mutane ba su ba ka sakonni ba ga Osinbanjo?
Gaskiya mutane da yawa sun ba ni sakonni zuwa gare shi. Wadansu sun ba ni wasiku a rubuce, wadansu kuwa sun ba ni sakon ne da baka cewa idan na samu ganin mataimakin shugaban kasa Osibanjo in shaida masa cewa suna cikin wahala. Akwai wadansu Fulani da suka rika gaya mini cewa a taimaka wa Fulani kuma gwamnati ta yi maganin rikicin da yake faruwa tsakanin makiyaya da manoma. Sakon da ya fi muhimmanci a wurina shi ne inda na tarar da wadansu yara a wani gari cikin talauci ga shi kayansu duk ya yayyage, sai wani tsoho ya kira ni ya ce in gaya wa Osinbanjo cewa su gyara makarantun boko kuma su tabbatar an sanya yara a makaranta. Wani abu da zan yi wa Allah godiya shi ne tsarin da Allah Ya yi mini daga barayi da ’yan fashi, sai dai wani tsoho da na gamu da shi bayan na wuce garin Kagara, sai ya tsayar da ni ya tambaye ni ina zan je, sai na ce masa Legas zan je kuma daga Kaduna nake, sai ya ce gaskiya kun dace da gwamna, da ma El-Rufa’i ne ya dace ya jagoranci jihar Kaduna saboda yana da ilimi kuma ya fito daga gidan ilimi, nan ya tsaya ya rika yi mini addu’a, da ya kammala sai muka yi sallama muka rabu.
Aminiya: Ba ka ganin mutane za su ga cewa ka yi wannan tafiya ne saboda ka samu abin duniya?
Ba haka ba ne. Na yi wannan tafiya ne saboda Allah. Idan ka je Kaduna ka bincika za ka ga ina da sana’ar yi. Ni ina sayar da takalma ne a Kaduna, idan ka je Sabon Tasha ka tambayi Kabiru Ja’afar mai sayar da takalma. Za a nuna maka shagona.
Aminiya: Idan ka gamu da mataimakin shugaban kasa Osibanjo da Tunubu me za ka ga kaya musu?
Gaskiya zan ji dadi. Akwai sakonnin da aka ba ni a kan hanya. Zan mika musu in ce musu ya kamata a duba koken jama’a kuma su yi kokari su ga an yi maganin matsalolin da suke damun mutane.
Aminiya: Idan za ka koma gida a kan kekan za ka sake komawa ko kuwa?
Yanzu dai burina na farko shi ne in ga na zo Legas lafiya kuma Allah Ya biya mini, burina na biyu in ga na sadu da Osinbajo da Tunubu da sauran shugabannin jam’iyyar APC kuma in ga na isar da sakonnin da jama’a suka ba ni, sannan daga bisani sai in zauna in yi nazari kuma idan zan koma me ya kamata in yi? Ko in koma a mota ko kuma a kan keke.