Tsohon Gwamnan Neja, Muazu Aliyu, ya ce shi ya fara watsa tsohon shugaban Boko Haram, Shekau na ainihi da takwaransa Abu Qaqa da jama’arsu daga jihar a lokacin da yake gwamna.
Mu’azu ya ce da bai tashe su ba, karshenta da yanzu sun mayar da Jihar Neja hedikwatar Boko Haram.
Ya shaida wa babban taron Kungiyar Kwararrun Masu Hulda da Jama’a ta Najeriya (NIPR) na 2023 cewa a lokacin da ya zama gwamnan Neja a 2007, jihar na fama da matsalar tsaro kuma Shekau na ainihi da Abu Qaqa suna zaune yankin Mokwa na jihar.
Ya ce, “Akwai wasu mutum tara da suka zama barazanar tsaro a Karamar Hukumar Mokwa waɗanda kuma zuwa 2007 yawansu ya ninninku zuwa mutum 7,000.
- Gwamnan Kano ya kama hadiminsa yana karkatar da abincin tallafi
- Muguwar kaddara ta sa na shiga Kannywood —Hafsat
“Sun mayar da kansu tamkar wata ƙasa, inda suke yin fashi tare da yin garkuwa da mutane musamman mata a yankin.
“Da muka gudanar da ƙidaya sai muka gano cewa kashi 60 cikin 100 na mutanen ba ’yan Najeriya ba ne. A lokacin Shekau na ainihi da kuma Abu Qaqa su ne shugabanninsu.
“A lokaci mun da samu goyon bayan tsohon shugaban kasa marigayi Umaru Musa Yar’adua muka watsa su bayan mun biya su diyya muka kwashe ’yan Najeriyan cikinsu a motoci zuwa jihohinsu, ’yan kasashe waje kuma muka kai su iyakokin shuga kasashensu.
“Wannan mataki shi ne ya taimaka, amma watakila da Jihar Neja ce za ta wayi gari a matsayin tushen Boko Haram,” in ji tsohon gwamnan.
Ya ci gaba da cewa “mun samu labarin suna yawa ziyartar Gasar Neja, kuma na san Gwamnatin Tarayya a shirye take ta taimaka wa duk gwamnan jihar, idan dai ya yi masa bangaren.”
Mu’azu Babangida Aliyu ya ce babbar hanyar magance matsalar tsaro ita ce yin kyakkyawan shiri da kuma nagartaccen kasafin kudi.
Ya bayyana cewa ta hanyar isasshen kasafin kudi bangaren ilmi da tattalin arziki za su inganta ta yadda matsalar kananan yara miliyan 20 marasa zuwa makaranta da kuma tsananin talauci su zama tarihi a Najeriya.
Da yake nasa jawabin, Ministan Yada Labarai, Mohammed Idris Malagi ya ce kasafin kudin 2024 na Naira tiriliyan 27.5 da Shugaba Tinubu Ahmed Tinubu ya yi zai kawo kyakkyawan sauyi a rayuwar ’yan Najeriya idan majalisa ta amince da shi.
A cewarsa, tun da shuagabn kasar ya hau mulki yake ta bullo da tsare-tsare masu ma’ana da za su ba da damar samub bunƙasar rayuwar ’yan Najeriya ta bangarori daban-daban.