✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

NAJERIYA A YAU: Mokwa: Tsakanin Taraddadin Rashin Matsuguni Da Jimamin Rashin ’Yan-Uwa

Wasu mutanen da dama dai sun yi batan dabo a wannan ibitila’i, wanda ya yi sanadiyyar rayukan mutanen da adadinsu ya haura 150.

More Podcasts

Shin wanne ya fi zafi – takaicin rasa matsuguni ko alhinin rashin sanin halin da ɗan uwa na jini yake ciki?

Wannan ne halin da wasu al’ummomi a Ƙaramar Hukumar Mokwa ta Jihar Neja suke ciki, bayan da suka tsinci kansu tsamo-tsamo a tsakiyar wata mummunar ambaliyar ruwa.

Wasu mutanen da dama dai sun yi batan dabo a wannan ibitila’i, wanda ya yi sanadiyyar rayukan mutanen da adadinsu ya haura 150.

Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne a kan yadda wadannan dubban mutane suka kai labari da halin da suke ciki.

Domin sauke shirin, latsa nan