Ga alama dai tasirin wakar da shararren mawakin siyasar nan Haruna Aliyu Ningi ya yi wa tsohon Gwamnan Jihar Kano Dokta Rabi’u Musa Kwankwaso da Gwamna mai ci Dokta Abdullahi Umar Ganduje, mai taken ‘Ga Kwankwaso ga Ganduje su za mu bi ba Burtu ba,’ ya kau, sakamakon dambarwar siyasa da ta kunno kai a tsakanin ’yan siyasar biyu.
Tun a ’yan watannin baya ne masu bibiyar harkokin siyasa a Jihar Kano suka yi hasashen rigimar siyasa a tsakanin Gwamna Ganduje da tsohon Gwamna Kwankwaso, duk da cewa wadanda ake yi dominsu suna ta musanta gabar siyasar a tsakaninsu, ta hanyoyi da dama, ciki har da kafofin watsa labarai.
Duk da wannan namijin kokari da ’yan siyasar biyu ke yi na musanta gabar siyasar a tsakaninsu, sai ga shi a ranar Litinin 7 ga watan Maris da muke ciki, abin boye ya fito fili a lokacin da tsohon Gwamnan ya kai wa mai ci ziyara a garinsu na Ganduje don yi masa ta’aziyyar rasuwar mahaifiyarsa.
Kimanin makonni uku ke nan da kai wannan ziyarar, amma har zuwa yau rikicin siyasar da ziyarar ta haifar bai kau ba a jihar ta Kano.
A takaice dai wannan ziyarar ta dora dan-bar gabar siyasa a tsakanin Ganduje da Kwankwaso.
A yayin ziyarar ta’aziyyar, Sanata Kwankwaso ya jagoranci dimbin magoya bayansa ne wadanda suka tarbe shi tun daga Filin Jirgin Sama na Malam Aminu Kano zuwa garin Ganduje domin ta’aziyyar.
Sai dai kuma a al’ada irin ta ’yan siyasa, a cikin tawagar ta Kwankwaso har da ’yan bangar siyasa, wadanda suka yi masa rakiya da kade-kade da bushe-bushe irin na siyasa. Haka kuma an tabbatar da cewa wadannan ’yan bangar siyasa suna dauke da miyagun makamai da suka hada da takubba da barandamai da adduna da sanduna da sauran makamai na gargajiya da aka san ’yan bangar siyasa na amfani da su a lokacin kamfen din siyasa.
Haka kuma an tabbatar da cewa magoya bayan Kwankwaso sun furta kalamai na batanci ga wadansu daga cikin kwamishinonin Gwamna Ganduje a lokacin ziyarar.
Wata majiyar Aminiya ta tabbatar da cewa, wadansu daga cikin ’yan bangar siyasar sun yi ikirarin cin mutuncin Babban Sakataren Gwamna Ganduje na Musamman Alhaji Bala Usman, idan da sun same shi a wurin zaman makokin.
Binciken Aminiya ya gano cewa, Gwamna Ganduje da Mataimakinsa da sauran manyan mutanen da ke wurin a lokacin da Kwankwaso ya kai ziyarar ba su ji dadin abin ya faru ba, ganin cewa zaman makokin ba gangamin siyasa ba ne.
Aminiya ta gano cewa, tun ma kafin ya isa garin na Ganduje, magoya bayan na Kwankwaso sai da suka haifar da wata ’yar kwarya-kwaryar barna a filin jirgin sama na Malam Aminu Kano yayin da jami’an tsaro suka hana su shiga filin saukar jirgin domin tarbo jagoran nasu.
Wata majiya ta shaida wa wakilinmu cewa, a maimakon magoya bayann Kwakwaso su bi doka kamar yadda aka bukace su, sai kawai suka tasallaka ta katangar filin saukar jirgin, wanda kuma a dalilin haka suka karairaya shingen karfe da ke saman katangar.
Daga ranar da aka kai wannan ziyara har zuwa yau dai batutuwan siyasa ne kawai ke kunno kai a Jihar Kano kamar tsinkewar carbi. Da farko dai Shugaban Jam’iyyar APC mai mulkin jihar, Alhaji Haruna Umar Doguwa ne ya fara kushe abin da tsohon Gwamnan ya yi a yayin ziyarar. Doguwa ya shaida wa manema labarai cewa, uwar jam’iyya da kuma Kwamitin Dattawa na Jam’iyyar ba su da hannu a waccan ziyara ta Kwankwaso, hasali ma ba a sanar da su ba, don haka ba da hannunsu aka yi duk abin da aka yi ba yayin ziyarar.
Haka kuma ya bayyana cewa, Jam’iyyar APC za ta kai kukanta ga uwar jam’iyya ta kasa domin ladabtar da tsohon Gwamnan kan abin takaicin da ya yi, wanda shi Doguwa ya ce ya saba wa addini da al’adar jama’ar Kano, don haka jam’iyyar ba za ta bar al’amarin ya wuce haka ba, ba tare da an hukunta wanda ya jagoranci yin sa ba.
Ya kara da cewa, APC a Kano ba ta da wani shugaban da ya wuce Ganduje, kuma ita jam’iyya shi ta sani a matsayin jagoranta ba wani ba.
Sai dai kwana daya da yin wannan jawabi ga manema labarai, Shugaban Jam’iyyar ya sake kiran wani taron manema labaran inda ya janye wadancan kalamai nasa, yana mai cewa ya gane kuskurensa na yin su. “Ina so in shaida wa duniya cewa na janye wadancan kalamai da na yi a kan ziyarar ta’aziyya da tsohon Gwamnan Kano Rabi’u Musa Kwnakwaso ya kai wa Gwamna mai ci a yanzu dangane da rasuwar nahaifiyarsa a garin Ganduje. Na farko dai ba ni na rubuta wancan daftarin da na karanta ba a lokacin taron manema labaran, haka kuma na karanta shi ne ta hanyar tursasawa da wadansu jami’an gwamnati suka yi min, don haka ina shaida wa al’umma cewa na nesanta kaina ga wancan jawabi,” inji Doguwa.
’Yan awanni kadan bayan kammala jawabin nasa, sai Kwamitin Zartarwar Jam’iyyar APC ya kira wani taron manema labarai inda ya nanata matsayinsa ga jawabin farko da shugaban jam’iyyar ya yi, wato na daukar matakin ladabtarwa ga Sanata Kwankwaso.
Kwamitin ya kuma nuna takaici ga matakin da shugaban jam’iyyar ya dauka na janye kalamansa na farko a kan tsohon Gwamna Kwankwaso. Shi ma kwamitin ya yi barazanar daukar matakin ladabtarwa ga shugaban na APC.
Shi ma da yake mayar da martani ga kalaman shugaban jam’iyyar ta APC kan ziyarar ta Kwankwaso, Dokta Yunusa Adamu dangwani, wanda kuma na hannun damar tsohon Gwamna Kwankwaso ne, ya yi tsokaci a kan dalilin da ya sa Kwankwaso ba ya yawan ziyartar Kano bayan saukarsa daga gadon mulki a shekarar da ta gabata. Ya ce a kokarinsa na kauce wa husumar siyasa ya sa Kwankwaso ya bayyana niyyarsa ta ziyartar Kano domin ta’aziyya a kurarren lokaci, amma sai ga shi duk da haka an samu dimbin jama’a da suka fito domin tarbarsa.
Ya ce, “Sai ga shi abin takaici wannan kyakkyawar niyya ta Kwankwaso ta ta’aziyya an juya ta koma abin kyama. Kuma wannan ya faru ne ’yan awanni da rasuwar Mataimakin Shugaban Jam’iyya na Jiha, Alhaji Ali danmaraya, amma sai ga shi gwamnati ta maida hankali ga taron ‘yan jarida a yunkurinta na raba jam’iyyarmu ta APC a Jihar Kano.”
Ya kara cewa, “Don haka ina kira ga gwamnatin Jihar Kano ta guji tsunduma Mai girma Shugaban kasa Muhammadu Buhari cikin wannan badakalar siyasa domin ta kare rauninta. A maimako haka, ya dace gwamnati ta fuskacin kalubalen da ke gabanta na ciyar da Jihar Kano gaba.”
Ana cikin wannan hali ne kuma kwatsan sai kungiyar Shugabannin kananan Hukumomi ta kasa (ALGON) ta Jihar Kano ta bayyana goyon bayanta ga Gwamna Ganduje dangane da wannan dambarwar siyasa da ta kunno kai a Jihar.
A wata sanarwa da Shugaban kungiyar na Jihar Kano Alhaji Ibrahim Ahmad karaye ya rattaba wa hannu, kungiyar ta nesanta kanta ga wancan abin takaici da tsohon Gwamnan ya aikata.“Muna bayyana bakin cikinmu ga abin da Sanata Kwankwaso ya yi a garin Ganduje inda ya mayar da ta’azziya kamfe na siyasa. Abin da Sanatan ya yi cin mutunci ne ga marigayyar, haka kuma tozartarwa ce ga addini da al’adar Bahaushe.”
kungiyar ta ce a shirye take ta dakushe duk wani yunkuri da wani mutum ko shi wane ne zai yi domin ya kawo baraka a cikin jam’iyyar ta APC a Kano.
A wani bangaren kuma, ’yan Majalisar Dokokin Jihar 34 ne suka yi wa Gwamna Ganduje mubayi’a a gidan gwamnati a ranar Talata 15 ga watan Maris domin nuna goyon bayansu ga Gwamnan. Da yake yi wa Gwamna Ganduje bayani a Gidan Gwamnati, Shugaban Majalisar Alhaji Kabiru Alhassan Rurum, ya ce ko kadan ‘yan majalisar ba su ji dadin abin da ya faru ba a yayin ziyarar ta Sanata Kwankwaso kuma sun nesanta kansu ga lamarin.
Rurum ya shawarci Ganduje ya gode wa Allah, ya tuna cewa ya keto hadurran siyasa a baya, amma da yake ya dogara ga Allah sai da ya ga bayan duk wadancan cikice-rikicen siyasa, har ga shi ma ya zama Gwamna.
Shugaban Majalisar ya kara da cewa, sakamakon dambarwar siyasar da ke faruwa, akwai bukatar Gwamnan ya nuna misali game da matsayin sanya jar hula da magoya bayan Jam’iyyar ta APC suke yi a Jihar Kano.
Da yake mayar da martani, Gwamna Ganduje ya shaida wa Shugaban Majalisar cewa hakika ya yi gwagwarmayar siyasa a baya kafin ya kai matsayin da yake kai a yanzu, kuma ko kadan ba ya da ra’ayin cin mutucin wani mahaluki da sunan siyasa, ko kuma domin kawai ya cimma burinsa na siyasa. Don haka ya yi kira ga ’yan majalisar su mai da hankali ga ayyukan ci gaban Jihar Kano kuma su yi hakuri da duk wata dambarwar siyasa da ka iya tasowa nan gaba a jihar.
Wata majiya mai tushe a cikin Majalisar Jihar Kano ta shaida wa Aminiya cewa, a cikin ’yan Majalisar Jihar 40 da ke wakiltar kananan hukumomi 44, mutum 10 ne kawai ke tare da Kwankwaso, yayin da 34 suke tare da Gwanduje.
A halin yanzu dai ga alama an ja daga tsakanin tsohon Gwamna da mai ci a yanzu, domin ko a ranar Litinin 14 da ta gabata sai da Gwamna Ganduje ya yi wasu kalamai na jurwaye mai kamar wanka ga Sanata Kwankwaso a lokacin da ya kai ziyarar gani-da-ido ga aikin hanyar Dakata zuwa Bela.
Ganduje ya ce, “Ba ma yawo da wuka, ba ma yawo da barandami, ba ma yawo da takwabi ko gariyo. Muna yawo ne da aiki kawai. A ziyarar da suka kawo a kwanakin baya sun ce sun yi aiki. Eh, mun yarda sun yi aiki a wasu wurare, amma kuma sun yi aika-aika a wasu wuraren. Kuma nan gaba kadan za mu bayyana wa duniya inda suka yi aika-aika.”
Ya kara da cewa, “Babu ruwanmu da wanda ba ya son Shugaban kasa Buhari. Duk wanda ya kara fadar munanan kalamai ga Buhari idan ya kara zuwa Kano to ku mutanen Kano ku nuna masa halayyarku ta Kanawa. Jihar Kano ta Buhari ce kuma Buhari na Kanawa ne, don haka ba wani dan siyasa da zai ja da Buhari sannan ya sake a Kano. Duk wanda ya soki Buhari to ya nemi wani gari ya fake amma ba Kano ba.”
Wadannan kalamai na Gwamna Ganduje manuniya ce ta cewa hakika dangantaka ta yi tsami tsakaninsa da tsohon Gwamnan kuma Sanata mai wakiltar Kano ta Tsakiya Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso.
Baya ga sanarwar da Dokta Yunusa Adamu dangwani ya bayar ga manema labarai, babu wani na kusa da Sanata Kwankwaso da ya sake furta wani kalami game da rigimar da ta kunno kai tsakanin Kwankwaso da Ganduje.
Wata majiya ta shaida wa Aminiya cewa, a halin da ake ciki a Kano yanzu sanya jar hula zabi ne, ba dole ba ne ga mabiya Jam’iyyar APC.
A baya dai Ganduje ya yi wa Kwankwaso Mataimakin Gwamna har sau biyu, kafin shi ma ya zama Gwamna. Ya yi masa Mataimaki daga 1999 zuwa 2003, haka kuma ya yi masa a karo na biyu daga 2011 zuwa 2015.
Don haka wannan takaddamar siyasa da ta kunno kai a tsakanin Ganduje da Kwankwaso lokaci ne kadai zai tabbatar da wane ne zai ci nasararta.
Yadda mutuwa ta tona tsakanin Ganduje da Kwankwaso
Ga alama dai tasirin wakar da shararren mawakin siyasar nan Haruna Aliyu Ningi ya yi wa tsohon Gwamnan Jihar Kano Dokta Rabi’u Musa Kwankwaso da…
