Ƙungiyar mayaƙan ISWAP sun mamaye garin Buni Gari a daren Juma’a da ƙarfe 12:00 na dare, mahaifar Gwamna Buni da ke ƙaramar hukumar Gujba a Jihar Yobe inda suka kai wani harin ba zata a garin da kuma barikin soja ta 27 da ke garin.
Wata majiya mai tushe daga garin ta tabbatar da cewa, lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 12:00 na daren Juma’a, inda maharan suka ƙona wani ɓangare na hedkwatar rundunar ta 27 da ke Buni Gari a Jihar ta Yobe.
Wannan gari na Buni Gari wadda bai wuce kilomita bakwai ba daga Buni Yadi hedkwatar ƙaramar hukumar ta Gujba wanda ke ɗauke da makarantar sojoji ta musamman kusan yanki ne da maharan ƙungiyoyin ‘yan Boko Haram da ISWAP suka fi kai kawo lokaci zuwa lokaci sakamakon kusancin da wani babban dajin da ya haɗa da dajin Sambisa.
Wasu mazauna yankin sun shaida wa Aminiya cewa, lokacin da waɗannan ’yan ta’addan suka iso garin sun yi ta harba makamansu ta kowace kusurwa lura da cewar garin na gaɓar dazuzzukan da ke kewaye da shi kafin daga bisani su shiga wani ɓangare na barikin sojan inda suka ƙona wasu gine-gine na mazauna yankin.
Aminiya ta tattaro rahoton cewa, a halin yanzu jami’an soji da ke ƙarƙashin rundunar Operation Haɗin Kai sun yi artabu da waɗannan ’yan ta’adda da ake kyautata zaton ’yan ISWAP ne.
Wata majiya mai tushe daga rundunar sojin Najeriya ta tabbatar da faruwar lamarin ta hanyar wani takaitaccen bayani da ta fitar a sahfinta na sada zumunta na X ( Twitter) a ranar Asabar.
Sai dai majiyar leƙen asiri na cewar, ’yan ta’addan sun kai hari a garin, inda suka riƙa harbe-harbe, amma cikin gaggawa sojojin tare da haɗin gwiwar mafarauta da ‘yan banga suka shiga tsakani inda suka shawo kan lamarin tare da fatattakar waɗannan ‘yan ta’addan.
Har ya zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, babu wani ƙarin bayani dangane da harin da kuma ko an yi asarar rayuka a hukumance.