’Yan ta’addan Boko Haram da suka kai hari kan rundunar soji ta 27 da ke Buni Yadi a jihar Yobe, sun kashe akalla sojoji hudu tare da lalata kayan aiki da dama na soji.
An kai harin ne kafin wayewar garin Asabar, jim kaɗan bayan da Ƙungiyar Gwamnonin Arewa maso Gabas ta gana a Damaturu domin tattauna hanyoyin haɗin gwiwa wajen yaki da ta’addanci.
Wani jami’in tsaro ya bayyana cewa maharan sun kai mummunan hari suna harbul kan mai da harbe-harbe.
Hedikwatar sojojin Najeriya ta tabbatar da harin inda ta bayyana cewa sojoji na fafatawa da ISWAP a Buni Gari.
Sai dai har yanzu ba a bayyana cikakkun bayanai kan asarar rayuka ba.
Mazauna garin Buni Yadi, mahaifar Gwamna Mai Mala Buni, sun tsere zuwa wurare masu aminci, kuma sojoji sun rufe babbar hanyar da ta hada Yobe da kudancin Borno.
Wannan harin ya biyo bayan wani irin harin da aka kai makonni biyu da suka gabata a yankin Chalie na Buni Yadi inda aka ce an kashe sojoji uku.
Hare-haren ’yan ta’adda sun karu a yankunan Borno, inda suke kai hari kan kauyuka da sansanonin soji.
Gwamnan Jihar Borno Babagana Zulum da sauran shugabanni sun yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta ɗauki mataki, suna masu nuni da cewa wasu ƙananan hukumomi na karkashin ikon Boko Haram tare da nuna damuwa game da shigowar ’yan ta’adda daga kasashe makwabta.
Sun yi kira da a kai farmaki a yankin tafkin Chadi da dajin Sambisa.