✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda mutumin da ya kashe mata 42 ya shiga hannu

Ya amsa cewa ya kashe matarsa da wasu 41, ya yi gunduwa-gunduwa da gawarwakin a cikin shekaru biyu

’Yan sanda sun kama wani mutum da ake zargi da kisan gilla da wasu mata 9 da aka tsinto gawarwakinsu a wani dutse da ake amfani da shi wajen zubar da shara a kasar Kenya.

Rundunar ’yan sandan kasar ta ce mutumin mai suna Jomaisi Khalisia, dan shekaru 33, ya amsa laifin kashe mata 42 tun shekarar 2022, ciki har da matarsa.

Masu bincike sun bayyana cewa matan da wanda ake zargin ya kashe ’yan shekaru tsakanin 18 zuwa 30 ne, kuma an kashe su ne a da salo iri guda.

An kama wanda ake zargin ne a wata mashaya da sanyin safiyar Litinin a lokacin da yake kallon wasan karshe na gasar Euro.

Al’ummar kasar Kenya sun fara ce-ce-ku-ce ne tun bayan da aka tsinci gawarwakin farko a ranar Juma’a a katafaren dutsen Mukuru da ke Nairobi ,babban birnin kasar.

Wanda ake zargin “[Ya] ya amsa cewa ya yaudari, ya kashe tare da jefar da gawarwakin mata 42 a jujin.

Mohamed Amin, shugaban hukumar binciken manyan laifuka (DCI) ya ce “An kashe matan ne a tsakanin shekarar 2022 zuwa ranar Alhamis.”

Ya ce bayan an kama wanda ake zargin, ya jagoranci ’yan sanda zuwa gidansa da ke kusa da wurin da lamarin ya faru.

Tun a ranar Juma’ar da ta gabata ne ’yan sanda suka killace wurin da aka samu gawarwakin matan a matakai daban-daban na rubewa.

’Yan sandan sun ce suna ci gaba da yi wa wanda ake zargin tambayoyi domin gano musabbabin kisan kuma za a gurfanar da shi a gaban kotu ranar Talata.

Tun da farko dai hukumar ’yan sandan Kenya ta ce tana bincike kan ko akwai hannun ’yan sanda a cikin kisan gillar kasancewar wurin da aka jefar da gawarwakin na kusa da ofishin ’yan sanda ne.