Musulmi a Najeriya da Kasar Saudiyya da wasu kasashe sun tashi da Azumin watan Ramadan a ranar Talata bayan ganin jinjirin watan a ranar Litinin.
Bayan hukumomi sun sanar da ganin watan na Ramadan, Musulumi a kasashe irinsu Saudiyya, Najeriya, Sudan, Masar, Syria, Qatar, Indonesia, Malaysia, Kuwaita, Jordan, Lebanon da Falasdinu da sauransu sun wayi garin Talata da azumi a bakinsu.
- Yarinyar da aka yanke wa al’aura ta warke
- An sauya tsarin Sallar Tarawih da Tahajjud a Masallacin Harami —Sudais
- Kar a manta da talakawa a lokacin Azumi — Buhari
Tun a ranar Litinin da aka ga watan, aka fara gabatar da Sallar Taraweeh bayan Sallar Isha’i a Masallatan Harami da ke Saudiyya da sauran wurare, kamar yadda aka saba a duk watan Ramadan.
Musulmi a fadin duniya ke ta bayyana farin cikinsu da yi wa juna fatar samun dacewa da alheran da ke cikin watan mai alfarma.
Tuni sabbin dokokin da kasar Saudiyya ta sanya a masallatan da sauransu na watan azumin suka fara aiki.
Dokokin sun hada da takaita shiga Masallacin Harami ga masu rajista kaadi, rufe wasu bangarori na Masallacin, da kuma hana bude baki a cikin taro da kuma takaita yin dawafi da masu Umrah kadai.
Sauran su ne hana masu Umrah taba dakin Ka’abah, rage yawan raka’o’in Sallar Taraweeh, bayar da tazara tsakanin masu ibada, da kuma hana su shan ruwan Zamzam yadda aka saba a baya.
An fara azumi a Najeriya
Da yake sanar da ganin watan da kuma daukar azumi a Najeriya, Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Muhammad Sa’ad Abubakar III, ya ce, “Bayan tantancewa da kuma tabbatar da ganin watan daga kwamitocin ganin wata na jihohi da na Kasa kamar yadda aka saba, ina sanar da cewa an ga watan Ramadan, wanda ya kawo karshen watan Sha’aban 1442 Hijiriyya.
“Haka kuma, bisa koyarwar Musulunci, ana umartar al’ummar Musulmi da su tashi da azumi ranar Talata.”
Sarkin Musulmi ya kuma yi kirga ga “’yan Najeriya da su ci gaba da zama lafiya da junansu ba tare da la’akari da bambancin addini ko kabila ba.”
Kasashen da ba su dauki azumi ba
Sai dai kuma duk da haka wasu kasashen duniya da ba a samu rahoton ganin wata ba sun sanar da cewa za su daukin azumin ne daga ranar Laraba, bayan cika watan Sha’aban kwana 30.
Kasashen da za su fara azumin a ranar Laraba sun hada da Indiya, Sri Lanka, Australiya da kuma Brunei.