Fassarar Salihu Makera
Godiya ga Allah da taslimi ga Annabi (SAW).
Bayan haka, lallai mafi hadarin cutar da take barazana ga al’umma, kuma take rusa karfinta, kuma take yi mata kaca-kaca, ita ce munafunci. Munafunci na haifar da tufka da warwara ga halin mutum, sai mutum ya rika bayyana sabanin abin da ke boye a zuciyarsa, ya rika fadin abin da ba zai aikata ba, ya yi alkawari ya saba, kuma ya yi yaudara, sannan yayin husuma ya yi fajirci.
Mafi munin illarsa kuma wanda ya fi watsuwa a yau, shi ne idan munafunci ya zamo siyasa abin bi, ko hanyar da kowa ke sha’awar hawa kanta, musamman a tsakanin shugabannin siyasa a kasashen Musulmi. Halin da muke ciki a yau yana fassara hakan daki-daki, kuma abin bakin ciki wadansu suna alfahari da hakan, suna ganin hakan wata burgewa ce.
Saboda hadarin haka Allah Ya fallasa halayen irin wadannan mutane a surori da dama, domin Ya tsarkake al’umma daga sharrin wannan muguwar dabi’a. Kuma Annabi (SAW) mai girma wanda ba ya fadin magana ta son zuciya ya fayyace siffofin wadannan mutane cikin fadinsa: “Alamun munafuki uku ne: Idan ya yi magana ya yi karya, idan ya yi alkawari ya saba, idan aka ba shi amana ya yi ha’inci, koda ya yi Azumi ya yi Sallah, kuma ya zaci shi Musulmi ne.” A wata ruwayar ya ce, “Idan ya yi rantsuwa ya yi yaudara, idan ya yi husuma ya yi fajirci.” Kuma ya ce, “Halaye hudu duk wanda ya tara su, ya zama cikakken munafuki. Wanda kuma yake da daya daga cikinsu, yana da wani yanki na munafunci har sai ya yi watsi da shi: Wato idan ya yi magana ya yi karya, idan ya yi rantsuwa ya yi yaudara, idan ya yi alkawari ya saba, idan kuma ya yi husuma ya yi fajirci.”
Hakika akwai bukatar mu kange mutanenmu daga ma’abuta wadannan halaye, domin kada su kasance bala’i ga daidaikun mutane da daukacin al’umma kamar yadda gara take cin itace, ko yadda sari ke lalata katako idan aka gafala daga gare su, tilas ne mu kasance a fadake kuma a hankalce game da su.
Mu tsaya mu dubi manyan alamomin wadannan mutane makiya gaskiya da suke kare karya. Hakika Manzon Allah (SAW) ya bayyana cewa siffarsu ta farko ita ce: “Idan zai yi magana ya yi karya.” Ibn Taimiyya (Rahimahullahu) ya ce: “Idan aka ambaci munafunci a cikin Alkur’ani, sai a ambace shi tare da karya, kuma idan aka ambaci karya, sai a ambace ta tare da munafunci. Allah Madaukaki Ya ce: “Suna yaudarar Allah da wadanda suka yi imani, alhali ba su yaudarar kowa face kawunansu, amma ba su sani ba. A cikin zukatansu akwai cuta, sai Allah Ya kara musu wata cutar, kuma suna da azaba mai radadi saboda abin da suka kasance suna karyatawa.” (K:2: 8-9). A cikin Suratu Tauba Allah Ya ce: “Kuma Allah Ya shaida su (munafukai) wallahi makaryata ne.” A nan Allah Ya ambaci karya. Kuma idan Allah Ya ambaci munafunci sai Ya ambaci karancin zikiri, (ambato ko tuna Allah). Allah Madaukaki Ya ce: “Kuma (su munafukai) ba sa ambato (ko tuna) Allah face kadan.” A wata ayar cikin Suratul Munafikun Allah Madaukaki Ya ce: “Ya ku wadanda suka yi imani! Kada dukiyarku da ’ya’yanku su kange ku daga ambaton Allah…” Allah Ya kore munafunci daga muminai, saboda zikiri da tuna Allah da suke yi, kuma Ya siffanta munafukai da karancin zikiri ko tuna Allah.
Masu karya la’anannu ne, don haka mutane su guji wannan dabi’a abar zargi. Lallai ginshikin munafunci kuma babban rukuninsa da kusoshin da suke rike da shi da turakun da suke tokare shi da da’irorin da suka kewaye shi ita ce karya. Munafukai ba za su yi munafunci ba face sai sun yi karya a cikin zukatansu. Munafunci kan fara ne da wani digo a cikin zuciya, ya rika girma har sai ya zama babbar shimfida kuma ganuwa mai hana imani wurin zama, Allah Ya tsare mu. Wannan ne ya sa ake cewa, “Wanda ya ginu a kan karya sai abincinsa ya yi zaki.” Ma’ana duk wanda rayuwarsa ta saba da karya zai yi wuya ya daina, maimakon haka zai ci gaba da karyar tsawon rayuwarsa. Wani mawaki ya ce: “Mutum ba ya yin karya face wulakantacce ko mai mugun aiki ko mai karancin ladabi.”
Yaudara da ha’inci:Saboda fadinsa (SAW): “Idan ya yi alkawari ya yi yaudara.” Duk wanda ya yi alkawari ga wani mutum ko mutane ko kungiya, sannan ya yi ha’inci ko yaudara, to wannan alama ce kuma rukuni ne daga cikin rukunan munafunci. Allah Madaukaki Ya ce: “Suna yaudarar Allah da wadanda suka yi imani, alhali ba su yaudarar kowa face kawunansu, amma ba su sani ba.” (K:2:8).
Fajirci yayin husuma: Saboda fadinsa (SAW) a cikin Sahihaini, “Idan ya yi husuma ya yi fajirci.” Wani malami ya ce: “Wanda ya yi husuma da Musulmi, sannan ya yi fajirci a husumarsa, hakika Allah Ya shaida cewa abin da ke cikin zuciyarsa shi fajiri ne munafuki.” “Daga cikin mutane akwai wanda maganarsa take burge ka a rayuwar duniya, alhali Allah Ya shaida abin da ke cikin zuciyarsa shi mai tsananin husuma ne.” Kuma (SAW) ya ce: “Mafi muni mazaje a wurin Allah shi ne mai tsananin yawan husuma.”
Za ka ga fajiri yana cin zarafin mutane ta hanyar husuma, ba ya jin kunyar amfani da miyagun kalamai da kausasa magana don ya musguna wa wanda ya saba masa.
Bai damuwa ya jawo rashin lafiya ko wahala ko cuta ko rauni ko ma ya kashe mutum, kansa kawai ya sani, wannan yana daya daga cikin siffofin munafukai. Daga cikin siffofinsu har wa yau akwai wulakantawa da yada barna. Allah Madaukaki Ya ce: “Lallai idan munafukai da wadanda suke da cuta a zukatansu da masu rarraba kan mutane a cikin Madina ba su hanu ba, za Mu shushuta ka a kansu, kuma ba za su makwabce ka ba a cikinta face kadan.”
Munafukai suna sabbaba rarrabuwar kan mutane da yada karairayi a tsakanin mutane domin firgitar da su ta yadda za su haifar da gaba da kiyayya a tsakanin mutane. “Suna nemanku da fitina, kuma a cikinku akwai ’yan leken asirinsu, kuma Allah Masani ne ga azzalumai.”
Sai kuma watsa fasadi a cikin kasa da sunan gyara. “Kuma idan aka ce musu; “Kada ku yi barna a cikin kasa,” sai su ce, iyaka mu masu gyara ne. A’a (karya suke yi) su masu fasadi ne, amma ba su sani ba.” Munafuki yakan rika yada fitina kamar wutar daji yana kona gidaje, yana bata zamantakewar jama’a, yana daidaita al’umma. Idan aka ce masa, kana bata al’amura tare da rarraba kan jama’a. Sai ya ce: “Wallahi ba na nufin komai face gyara,” alhali ya san barna da fasadi yake nufi. Mafi yawan masu bata tsakanin iyali da al’umma da kabilu da zamantakewar jama’a su ne wadannan munafukai. Allah Ya ce: “Daga cikin mutane akwai wanda maganarsa take burge ka a rayuwar duniya, amma Allah Yana shaida a kan abin da yake cikin zuciyarsa shi mai tsananin husuma ne. Idan ya juya a cikin kasa sai ya rika fasadi a cikinta yana hallaka abinci da zuriya, kuma Allah ba Ya son fasadi.”
Tsoron aukowar tsawa: “Suna zaton kowace tsawa a kansu take.” A kullum suna cikin tsoro da firgici, suna kuma cikin kai-kawo a rayuwarsu.
Umarni da abin ki da hana aikin alheri: Kamar yadda Allah Madaukaki Ya ce: “Munaukai maza da munaukai mata, sashinsu majibintan sashi ne; suna umarni da abin ki, suna hana aikin alheri, kuma suna damke hannunwansu (rowa). Sun mance da Allah, sai Ya mance da su, lallai munafukai su ne fasikai.” A kullum suna wargaza al’umma da kawo tashin hankali da rudar da mutane da jirkita addini da hallaka mutane da kwace musu dukiya ko hakkokinsu, kuma suna umarni da ababen kyama, suna toshe hanyoyin isa ga abubuwa masu kyau.
Sukan bayyana alfasha da kwadayi da wauta a zantukansu, ga girman kai da jiji da kai da iya zakin baki. Allah Madaukaki Ya ce: “Idan suka yi magana sai ka saurara wa maganarsu.” Saboda iya zakin baki da sarrafa harrufa da karkata murya da fasaha a yayin maganar da dagewa kan zance da wasa da lafuzza. Tirmizi ya ruwaito Hadisi da ke cewa: “Rashin magana da kunya wasu yankuna ne daga yankunan imani, amma yawan magana da rashin kunya wasu yankuna ne daga cikin munafunci.”
Daga cikin alamun munafukai akwai rashin karbar hukuncin Allah tare da riya cewa sun yi imani. Ciruwa zuwa ga hukuncin Allah yana tabbatar da tsarki da tsabtar zuciya da mika wuya ga hukuncin Allah da ciruwa daga karkata da sha’awace-sha’awacen zuciya. Wannan kuwa bai samuwa a cikin zuciyar da munafunci ya yi mata hijabi. Saboda haka ne munafukai suka rasa wannan mika wuya ga Allah cikin hukuncinSa, kuma ba su neman yin hukunci da dokokin Allah, sun fi fifita ra’ayi a kan shari’a. Sai su rika bayyana girman Littafin Allah a baki, amma idan hukuncin Allah ya zo sabanin abin da suke so, sai su juya masa baya, su dage wajen yakar wanda ya bayyana musu wajibcin bin hukuncin Allah kan al’amarin. Allah Ya yi gaskiya cikin fadinSa: “Suna cewa: “Mun yi imani da Allah da Manzon (Allah), kuma mun yi da’a.” Sannan wani yanki su juya baya daga cikinsu, a bayan fadin haka. Wadannan ba masu imani ba ne. Idan aka kira su zuwa ga Allah da ManzonSa domin Ya yi hukunci a tsakaninsu, sai wani yanki daga cikinsu su kangare.”
Saboda bacin zukatansu, ba su iya ba hukuncin Allah matsayin da ya dace, idan aka ga yau sun yi haka, to saboda wata maslaha ce da za su samu, ko ganima da za su kwasa. “Idan gaskiya ta kasance a gefensu, sai su zo masa suna masu kankan da kai. Shin a cikin zukatansu akwai cuta ce, ko kuwa sun yi shakka ce, ko suna tsoron Allah Ya saukar da bala’i a kansu ne, ko ManzonSa ya fallasa su? Ba haka ba ne, wadancan mutane su ne azzalumai.” Sabanin masu imani da aka siffanta su da imani da samun rabo. “Abin sani kawai maganar muminai idan aka kira su zuwa ga Allah da ManzonSa domin Ya yi hukunci a tsakaninsu, sai su ce: “Mun ji, kuma mun bi.” Wadancan su ne masu babban rabo. Wanda ya yi da’a ga Allah da ManzonSa, kuma ya ji tsoron Allah, kuma ya yi maSa takawa, wadancan su ne masu rabauta.”
Daga cikin alamunsu akwai cewa, ta cikin maganganunsu ana iya gane adawa ga ma’abuta gaskiya da salihan bayi. Sakamakon yadda zukatansu ke cike da kiyayya ga muminai da nuna musu adawa. Duk da abin da suke boyewa a zukatansu kinsu da sonsu, harsunansu sukan furta wani abu daga abin da suke boyewa. “Hakika kiyayya ta bayyana daga bakunansu, alhali abin da suke boyewa a zukatansu ne mafi girma. Muna bayyana muku ayoyin ne in kun kasance kuna hankalta.”