✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Yadda muka tsallake rijiya da baya a harin Jos

Yadda aka yi ta yi wa matafiyan kisan gilla bayan an ritsa motocinsu

Wani daga cikin matafiyan da aka tare aka kashe wasunsu a Harin Jos, Jihar Filato, a karshen mako, ya bayyana yadda maharan suka yi wa abokan tafiyarsu kisan gilla bayan sun ritsa motocinsu.

Mutumin ya shaida wa shirin Najeriya A Yau wanda Aminiya take gabatarwa ta intanet cewa da shi aka kwashe gawarwakin wasu daga cikin mutanen da aka kashe a motocin nasu zuwa asibiti.

– Abin da Ya Biyo Bayan Kisan Wasu Matafiya A Jos
– NSCIA da MURIC sun yi Allah-wadai da kisan mutum 25 a Filato

Ya ce, “Kafin mu baro asibitin dai an samu gawar mutum 26,” shi da wasu mutum 28 kuma sun tsallake rijiya da baya a harin na Jos, wasunsu  kuma da rauni.

“Ni da wadansu mun samu rauni da wadansu da yawa kuma da Allah Ya kiyaye ba a taba su ba; Don da aka kawo mu yanzu mun kai 29.”

Fulanin da aka yi wa kisan gillan a harin da aka kai musu  a kan hanyar Jos zuwa Zariya, suna hanyarsu ta dawowa ne daga Bauchi, bayan sun kai wa Sheikh Dahiru Usman Bauchi ziyara domin murnar shiga Sabuwar Shekarar Musulunci ta 1443 bayan Hijira.

A zantawarsa da shirin na Aminiya, kan harin na Jos, Shugaban kungiyar Fulani ta Gan-Allah Fulbe ta Kasa (GAFDAN), Suleiman Yakubu, ya ce matafiyan sun fito ne daga sassa daban-daban na Kudancin Najeriya da ma kasar Ghana domin ziyartar shehin malamin.

– Yadda aka kai Harin Jos

Shugaban Fulanin ya ce wani yaronsa da ke cikin matafiyan ya kira shi bayan harin ya shaida masa cewa, “Sun karkashe mu, ni kaina sun ji min rauni, amma na tsallake rijiya da baya.

“Na ce ku nawa, ya ce wallahi muna tafe mu da yawa, ga shi an karkashe mu, ga gawarwaki, ga kuma wasu an ji musu rauni.

“Mun shigo Jos, motocinmu na biye da juna —bas-bas, muna gangarowa cikin Jos din kawai sai muka ji suna cewa wadancan motocin Fulani ne, motocin Fulani ne.

“Kawai sai muka ga sun tarbe mu sun sa mu faka, [kawai muka ga] daga mai ice sai mai adda, sai mai bindiga.

“Shi ne na kira Ciyaman dina [na Filato] da Sakatare da Shugaban Matasa, Abdulkarim, na ce a je, maza a kai musu gudunmawa.

“Da yardar Allah jami’an tsaro sun yi ca da wuri, ’yan sanda da sojoji, an dauko su an kawo su asibitin na Filato.”

– Yawan mamata ya karu

Suleiman Yakubu ya ce bayan Harin Jos din da farko, “An samu gawar mutum 24, aka yi jana’izarsu, amma yanzun nan da muke magana da kai sun bugo min an samu [karin] gawa shida, wasu a bisa duwatsu, wasu a kwarkwada; Yanzu suna shirin su je tare da jami’an tsaro a dauko gawarwakin.

“An lissafa wadanda ba a gani ba, kuma su ne wadannan mutum shida ga su kuma an gan su.”

Ya ce sauran kuma, “Daga wadanda ke asibiti da wadanda suka ji raunin da bai taka kara ya karya ba, sai wadanda suka gudu.”

Sai dai ya ce zuwa lokacin da wakilinmu ya tuntube shi, ba a kai ga ba shi alkaluman wadanda aka ji wa rauni ba a harin na ranar Asabar.

Sai dai wata sanarwa da Gwamnatin Jihar Filato ta fitar kan harin ta ce mutum 23 ne suka ji rauni, wasu 26 suka tsira babu ko kwarzane.

– A gaggauta daukar mataki

Bafulatanin da ya tsallake rijiya da baya a ya yi kira da gwamnati ta gaggauta gano wadanda suka kai Harin Jos din, ta kuma hukunta su.

Shugaban Fulanin ya roki Gwamnatin Tararayya da ta Jihar Filato da su gaggauta daukar mataki domin “hana fitina, wadda wuta ce, in ta tashi kafin a kashe ta sai ido ya yi ja.”

Ya ce suna fatan gwamnati za ta dauki matakin da ya dace, “Idan muka ga ta dauki matakin da ya dace, ka gani to sai a iye wa jama’a, domin Fulanin nan akwai wadanda suka fito daga Ghana, duk shekara sai sun zo.

“Ka ga idan an kashe maka dan uwa, ka ga ba a dauki wani mataki ba, ba abin da aka yi, to ai irin wannan ke sa a dauki mataki da hannu, mu kuma ba ma son daukar mataki a hannunmu domin mu Fulani ne masu bin doka da oda.”

– Dokar hana fita a Jos

Tuni dai Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya yi alkawarin tabbatar da ganin an gano tare da hukunta maharan.

Rahotanni sun nuna hare-haren daukar fansa sun biyo bayan Harin Jos din, wanda ya sa a nata bangaren, Gwamantin Jihar Filato ta sanya dokar hana fita ta sa’a 24 a garin Jos.

A ranar Asabar mun kawo rahoton yadda wasu ’yan daba suka tare motocin matafiyan suka rika kashewa a yankin Gada-Biyu.

Wani dan garin Jos da muka zanta da shi bayan sanya dokar ya shaida mana cewa an fara tashin hankali a garin, kafin gwamnatin Jihar ta sanya dokar hana fita ta sa’a 24.

“Hargitsi ya fara tashi a wasu bangarori na wasu unugwanni da har ya kai ga asarar wasu daga cikin al’umma.

“Mun fito za mu fita harkokinmu sai ga shi an sa dokar hana fita; To dama akwai wuraren da aka sa dokar daga shida zuwa shida, amma sai ga shi yanzu an mayar awa 24.”