Wata ’yar Isra’ila mai shekaru 85 da Hamas suka sako ta bayan sun yi garkuwa da ita, ta yaba da irin kulawar da mayakan kungiyar ke ba wa mutanen da ke hannunsu.
Yocheved Lifshitz ta ce duk da cewa a lokacin da aka sace su mayakan sun dake ta, amma daga baya sun ba su kulawa sosai a tsawon lokacin da suke hannunsu.
- Falasdinawan da Isra’ila ta kashe a Zirin Gaza sun haura 5,000
- Ɗalibin jami’a ya ‘kashe’ Ɗan sakandare a Bauchi
Yocheved Lifshitz wadda mazauniyar yankin Yahudawa na Nir Oz kibbutz da ke makwabtaka da Gaza inda Hamas ta kai hari ranar 7 ga wata, ta ce har yanzu mijinta na hannun kungiyar da ta yi garkuwa da mutum kimanin 200.
Da aka tambaye ta dalilinta na mika wa daya daga cikin mayakan Hamas hannu suka yi musaba a lokacin da kungiyar ta sako ta, sai ta ce, “Sun nuna mana tausasawa, sun kyautata mana, kuma sun ba mu duk abin da muke bukata.
“Suna da fara’a da kuma taka-tsantsan,” kuma bisa dukkan alamu sun yi cikkaken tsari mai kyau kafin su yi garkuwa da mu.
Dattijuwar ta ce, “sun shirya wa harin tun da dadewa, saboda duk wani abu da namiji ko mace za ta bukata sai da suka tanade shi, hatta da sabulun wanke kai sun tanada.
“Abincin da suke ci, shi suke ba mu — har da kayan lambu da cukwi da sauransu,” in ji Lifshitz.
Hamas ta sako Lifshitz ne tare da wata ’yar shekara 79 mai suna Nurit Cooper, kwana uku bayan kungiyar ta sako wata ba’amurkiya tare da ’yarta.